Cunha ya ceci Manchester United daga rashin nasara a Fulham, Fulham 1-1 Manchester United
Ƙwallon da Matheus Cunha ya ci Fulham ta taimaka wa Manchester United ta tashi kunnen doki 1-1 a gasar Premier League ranar Lahadi.
Fulham ta fara zura kwallo a raga bayan da Lisandro Martinez ya ci gida a karawar da aka yi a Craven Cottage - daga baya United ta farke ta hannun dan wasan tawagar Brazil.
Da wannan sakamakon kungiyar da Michael Carrick ke jan ragama ta kaucewa rashin nasara uku a jere, yanzu tana ta 12 a teburin Premier League da maki biyar daga karawa biyar.
Fulham kuwa tana matsayi na 19 da maki biyu kacal.