Me ya sa tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu ke ziyartar malaman addini?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A yayin da ake tunkarar zaɓen 2027, tawagar yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da jerin ziyarce-ziyarcen neman goyon baya daga fitattun malaman addini a sassa daban-daban na Najeriya.

A baya-bayan nan tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu ƙarƙashin jagorancin babban daraktan kwamitin Sanata Abdul'aziz Yari ya ziyarci Sheikh Sani Yahya Jingir da Sheikh Bala Lau da Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi da kuma Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara.

Matakin na haifar da muhawara da tambayoyi kan dalilan waɗannan ganawa a daidai lokacin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi.

Masana harkokin siyasa na ganin cewa irin waɗannan ziyarce-ziyarcen na da muhimmanci wajen neman kusanci da al'ummomi, musamman ganin tasirin da malamai ke da shi wajen tsara ra'ayin mabiyansu kan manyan batutuwan ƙasa.

Sai dai wasu na kallon matakin a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin faɗaɗa tushen goyon bayan siyasa gabanin zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa, yayin da wasu ke cewa ganawar na da alaƙa da neman addu'a da shawarwari daga jagororin addini.

Me ya janyo ziyarar?

Farfesa Abubakar Kari, malami a Jami'ar Abuja kuma masani kan harkokin siyasa, ya ce ziyarce-ziyarcen na da alaƙa da ƙoƙarin neman goyon bayan malaman addini, kasancewar suna da dimbin mabiya da ke sauraron shawarwarinsu.

Ya ce shugabannin kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Tinubu sun fahimci irin martaba da girmamawar da al'ummar Arewacin Najeriya ke yi wa malaman addini, wanda ya sa suke neman kusantar su a wannan lokaci.

"Ko a shekarun baya, ra'ayoyi da huɗubobin malamai sun taka muhimmiyar rawa wajen tasiri kan yadda wasu mutane ke kallon harkokin zaɓe da siyasa," in ji shi.

Masanin siyasar ya ci gaba da cewa "Ina ganin wannan ne ya sa tawagar ta rungumi hanyar tuntubar malaman addini, domin ta haka za ta iya samun goyon bayansu tare da ƙarfafa dangantaka da mabiyansu."

Malamai za su iya tasiri wajen zaɓe?

Farfesa Kari ya ce komai na iya faruwa, musamman idan aka yi la'akari da cewa a hankali wasu daga cikin mabiya da masu ra'ayi ɗaya da manyan malaman addini na fara nesanta kansu daga jagororinsu.

Ya ce akwai masu sukar wasu malaman da zargin cewa sun tsunduma cikin harkokin siyasa, yayin da wasu ke ganin suna amfani da yawan mabiyansu ne wajen ƙarfafa tasirinsu da matsayinsu a cikin al'umma.

"Wasu malaman sun yi suna sosai har ana zarginsu a sarari da shiga siyasa. Haka kuma, a wasu lokutan ra'ayoyinsu kan harkokin siyasa suna saɓawa da na wasu daga cikin mabiyansu," in ji shi.

Sai dai duk da haka, Farfesa Karin ya ce matakin da 'yan siyasa ke ɗauka na neman kusantar malaman addini abu ne da za a iya fahimta.

"Saboda haka ba lallai ba ne ƙoƙarin 'yan siyasar ya ba da sakamakon da suke fata. Amma duk da haka yana da muhimmanci su yi hakan, domin idan suka samu goyon bayan malaman, akwai yiwuwar hakan ya taimaka musu wajen samun goyon bayan wasu daga cikin mabiyan malaman," in ji shi.

Hakan zai shafi yadda jama'a ke kallon malaman?

A baya, da dama daga cikin malaman addini kan yi ƙoƙarin nesanta kansu daga harkokin siyasa, lamarin da ya sa ake kallonsu a matsayin masu taka-tsantsan da ba sa goyon bayan wata jam'iyya ko ɗan takara kai tsaye.

Sai dai a yanzu, yayin da ake ganin wasu daga cikinsu na karɓar baƙuncin ƴan siyasa ko kuma bayyana ra'ayoyinsu kan harkokin zaɓe, wasu na tambayar ko hakan ba zai sauya yadda al'umma ke kallonsu ba.

Farfesa Abubakar Kari ya ce irin waɗannan ziyarce-ziyarcen na iya yin tasiri ga kima da martabar malaman a idon jama'a.

"Wasu daga cikin malaman sun shiga siyasa sosai har ana danganta su da wasu jam'iyyu ko ƴan takara. Haka kuma, ba sa jin tsoron bayyana matsayinsu a fili kan al'amuran siyasa," in ji shi.

Ya ƙara da cewa hakan ya haifar da sauyi a yadda wasu ke kallon malaman addinin.

"Wannan ya yi tasiri a kan martabar wasu daga cikinsu, domin a idon wasu mutane kimarsu ta ragu idan aka kwatanta da yadda ake kallonsu a baya," in ji malamin jami'ar.

Me ya kamata malaman su yi don kare kimarsu?

Farfesa Kari ya ce duk da cewa tsarin dimokraɗiyya ya bai wa kowa damar bayyana ra'ayinsa, akwai buƙatar malaman addini su yi taka-tsantsan wajen hulɗarsu da 'yan siyasa.

Ya ce neman goyon bayan malamai wani abu ne da ƴan siyasa ba za su daina yi ba, amma ya kamata malamai su guji nuna goyon baya kai tsaye ga wani ɗan takara ko jam'iyya.

"Ƴan siyasa ba za su daina zuwa wajen malamai domin neman goyon baya ba. Amma abin da ya kamata malamai su yi shi ne su guji fitowa fili suna nuna goyon baya ga wani ɗan takara," in ji shi.

Farfesa Karin ya ƙara da cewa ya dace malaman su ci gaba da taka rawar da al'umma ke kallonsu a matsayin iyaye da masu ba da shawara ga kowa ba tare da nuna wariya ba.

"Ya kamata su yi amfani da martaba da kimar da suke da ita a cikin al'umma wajen ciyar da muradu da buƙatun mabiyansu da kuma talakawan Najeriya gaba ɗaya, maimakon tsunduma cikin siyasar ɓangaranci," in ji shi.