Abubuwa 7 da aka haramta wa ƴansanda game da siyasa

    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da zaɓen Najeriya na 2027 ke ƙaratowa, gwamnatin tarayyar ƙasar ta ja kunnen ƴansanda da kada su zama ƴan koren ƴan siyasa, kuma dole ne su kasance masu adalci da zama tsaka-tsaki ga kowa.

Kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya bayyana, shugaban ƙasar Bola Tinubu ya buƙaci rundunar 'yan sandan Najeriya su yi aiki bisa bin doka da oda.

A ƙasashe da dama, zarge-zargen amfani da jami'an tsaro wajen murɗe akalar siyasa ko fifita wasu ƴan takara kan wasu na daga cikin abubuwan da ke janyo ce-ce-ku-ce a lokacin zaɓe.

Masana na cewa ko da ba a ba da umarni kai tsaye ba, wasu halaye da matakan da jami'ai ke ɗauka kan iya haifar da zargin nuna son kai da ɓangaranci.

Mun tattauna da masana kan wasu hanyoyin da jami'an ƴan sanda za su iya shiga siyasa ko a zarge su da nuna ɓangaranci a lokacin siyasa.

Wane hurumi ƴansanda ke da shi a siyasa?

A tsarin dimokuraɗiyya, rundunar ƴan sandan Najeriya hukuma ce da aka kafa domin tabbatar da tsaro, doka da oda, ba tare da nuna biyayya ga wata jam'iyya ko ɗan siyasa ba.

Duk da cewa shugaban ƙasa shi ne babban jagoran ɓangaren zartarwa, aikin 'yan sanda ya kamata ya kasance karkashin dokoki da ƙa'idojin aikinsu, ba umarnin siyasa ba.

Lauya kuma masani harkokin shari'a, Barista Aminu Abdulrasheed, ya ce a bisa doka bai kamata rundunar ƴan sanda ta karɓi umarni daga wani ɗan siyasa wajen gudanar da ayyukanta ba. A cewarsa, rundunar na da tsarin shugabanci da jerin umarni nata, wanda jami'ai ke bi daga manyansu har zuwa ƙasa.

"Babban aikin ƴan sanda shi ne tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi, hana aikata laifuffuka, binciken masu laifi da kuma tabbatar da zaman lafiya a cikin al'umma," in ji shi.

Wannan ya haɗa da lokutan zaɓe, inda ake sa ran su samar da yanayin da 'yan ƙasa za su iya gudanar da harkokinsu na siyasa cikin lumana ba tare da tsoro ko fargaba ba.

Sashe na 214 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ne ya kafa rundunar ƴan sandan Najeriya, tare da ba ta ikon gudanar da ayyukan tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar.

Ta ya za a gane ƴansanda na nuna wariya?

Ɗaya daga cikin manyan alamomin da kan sa a yi zargin cewa jami'an tsaro suna nuna ɓangaranci shi ne idan aka ga ana mu'amala da jam'iyyun siyasa ko ƴan takara ta hanyoyi mabambanta ba tare da wani dalili na doka ba.

Barista Abdulrasheed, ya ce idan wata jam'iyyar siyasa ta shirya gudanar da taro ko gangamin yaƙin neman zaɓe, sai jami'an tsaro su hana ta yin hakan alhali suna barin wata jam'iyya ta gudanar da makamancin wannan taro ba tare da tangarda ba, hakan kan haifar da zargin cewa an ɗauki ɓangare.

"Ana kallon hakan a matsayin nuna son kai ko ɗaukar ɓangaren wata jam'iyya," in ji shi.

Masanin ya kuma bayyana cewa dokoki da ƙa'idojin aikin rundunar 'yan sanda ba su ba jami'ai damar shiga harkokin siyasa ko tallata wani ɗan takara ko jam'iyya ba.

A cewarsa, da zarar jami'in tsaro ya fito yana goyon bayan wani ɗan takara ko yana amfani da matsayinsa wajen amfanar wata jam'iyya, hakan na iya kawo cikas ga amincewar jama'a da sahihancin tsarin zaɓe.

Wata alamar nuna ɓangaranci kuma ita ce idan jami'an tsaro sun fi mayar da hankali wajen takura wa wani ɓangare na siyasa fiye da wani.

Masana na cewa hakan kan haɗa da hana tarurruka ko gangami, kama magoya baya ko kuma sanya tsauraran matakan tsaro a kan wasu ƴan siyasa ba tare da yin irin haka ga sauran masu mulki ba.

Sai dai Barista Abdulrasheed ya bayyana cewa akwai yanayin da doka ta amince 'yan siyasa su nemi kariyar jami'an tsaro.

"Idan akwai yiwuwar barazanar tsaro ga rayuwa ko dukiyoyi, aikin 'yan sanda ne kare lafiyar kowa ba tare da la'akari da jam'iyya ko ra'ayin siyasa ba," in ji Baristan.

Masanin ya jaddada cewa a lokacin zaɓe, gwargwadon yadda jami'an tsaro ke nuna adalci ga dukkan ɓangarori, hakan na ƙara wa jama'a kwarin gwiwa cewa tsarin zaɓen na gudana cikin gaskiya.

Amma idan aka fara ganin wasu matakai da ke nuna bambanci, to hakan kan jefa rundunar cikin zargin zama kayan aikin siyasa maimakon cibiyar tsaro da aka kafa domin yi wa 'yan ƙasa hidima.

Waɗanne ayyuka ne aka haramta wa ƴansanda a lokacin siyasa?

Baya ga ayyukan tsaro da doka ta ɗora musu, akwai wasu abubuwa da bai kamata jami'an ƴan sanda su aikata ba saboda suna iya jefa su cikin zargin nuna ɓangaranci ko shiga siyasa.

Barista Aminu Abdulrasheed ya ce babban abin da doka da ƙa'idojin aikin 'yan sanda suka hana shi ne nuna son kai ga wata jam'iyya ko ɗan takara. A cewarsa, aikin jami'in ɗan sanda shi ne kare kowa daidai, ba tallata ra'ayin siyasa ko taimakawa wani ɓangare ya samu rinjaye ba.

Daga cikin ayyukan da aka haramta musu akwai:

  • Tallata ko nuna goyon baya ga wata jam'iyya ko ɗan takara yayin da suke bakin aiki.
  • Yin amfani da iko ko makamai wajen tsoratar da masu zaɓe ko magoya bayan wata jam'iyya.
  • Hana wata jam'iyya gudanar da halalattun tarurruka ko gangami alhali ana barin wata jam'iyya ta yi irin wannan taron.
  • Kamawa, tsarewa ko binciken ƴan siyasa bisa dalilan siyasa maimakon amfani da hujjojin karya doka.
  • Ba da kariya ta musamman ga wata jam'iyya fiye da sauran jam'iyyu ba tare da dalilin tsaro ba.
  • Tsoma baki a yadda ake kaɗa ƙuri'a, ƙirga ƙuri'u ko bayyana sakamakon zaɓe, domin waɗannan ayyuka na hukumar zaɓe ne.
  • Karɓar umarni daga ƴan siyasa da ke sa su kauce wa ƙa'idojin aikinsu ko tanadin doka.

Masana na cewa, a lokacin siyasa ana sa ran ƴan sanda su kasance masu zama tsaka-tsaki, da nuna adalci da ƙwarewa, su kare haƙƙin dukkan jam'iyyu da masu zaɓe, tare da ɗaukar mataki iri ɗaya kan duk wanda ya karya doka ba tare da la'akari da matsayinsa na siyasa ba.