Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Messi ya yi bankwana da Argentina cikin hawaye
Lionel Messi ya ce yana ''godiya da alfahari'' ya kammala buga wa tawagar Argentina wasanni, wanda ya zura kwallo a fafatawar da suka doke Benin 3-0 a daren Talata a Buenos Aires.
Dan wasan mai shekara 39, ya yi wasan karshe sanye da rigar Argentina a karawar sada zumunta da Benin da cin kwallo ta uku a bugun fenariti, sannan shi ne ya bayar da sauran biyun da suka yi nasara.
A cikin watan Agusta, Messi ya sanar da cewar ya yi ritaya daga buga wa Argentina, bayan gasar cin kofin duniya, wanda ya yi sama da shekara 20 yana wakiltarta.
Kuma karon farko da ya yi wa Argentina wasa tun bayan mutuwar babansa, Jorge mai shekara 68, bayan da ya sha fama da doguwar jinya.
Bayan tashi daga karawar Messi ya yi wa magoya baya jawabi na kusan minti 10, yayin da wasu daga cikin abokan wasansa - ciki har da Enzo Fernandez na Manchester City - suka fashe da kuka.
"Akwai abubuwa da dama da nake ji a zuciyata a yanzu," in ji shi. "Tabbas na manta da wasu abubuwa da dama da nake son faɗa muku, saboda wannan lokaci ne mai matuƙar mahimmaci a gare ni. Mutum na farko da ya zo min a rai shi ne mahaifina.
"Zan bar tawagar Argentina ina ta godiya da alfahari kuma ina cikin natsuwa. Na gode da kowa"
Messi ya buga cikakken mintuna 90 a bikin yi masa ban kwana a gaban magoya baya 85,000 da suka cika filin wasa na Monumental, inda aka shirye-shirye na musamman da ya haɗa da haska fitilar nan ta laser da kade-kade da wasu abubuwan da aka gabatar don tunawa da gwazon dan wasan tawagar Argentina.
Lokacin da Messi ya sanar da yin ritaya a watan Agusta, ya ce shawarar da ya yanke ta ''zama abin bakin ciki a gareshi", amma ya yi imanin cewa ''lokaci ya yi."
Wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or takwas ya ce ya fara rubutan saƙon da ya sanar da yin ritaya ne a ranar 21 ga watan Yuli, kwana biyu bayan Argentina ta sha kashi a hannun Spain a wasan ƙarshe a gasar cin kofin duniya ta wannan bazara.
Messi ya fara buga wa Argentina wasa ne a shekarar 2005, ya fara da canjin dan wasa a minti na 63 a karawar sada zumunta da Hungary, wanda Argentina ta ci 2-1.
Sai dai kasa da minti daya da shigarsa filin aka ba shi jan kati kai tsaye bayan da ya yi wa mai tsaron bayan Hungary, Vilmos Vanczak gula a fuska.
Duk da wannan fara wa da cin karo da cikas, Messi ya ci gaba da buga wa Argentina wasanni, harma ya zama shi ne kan gaba a yawan taka mata leda da kuma ci mata kwallaye da lashe Copa America biyu da kofin duniya a Qatar a 2022.
Messi shi ne na biyu a yawan cin kwallaye a gasar cin kofin duniya mai 21 a raga, yayin da Kylian Mbappe ke gabansa mai 22 a raga.
Haka kuma shi ne na biyu a duniya a yawan ci wa kasa kwallaye a tarihi mai 126, bayan Cristiano Rolando wanda ya ci wa Portugal 146.
"Ba ni da wani abin yi face yin alfahari da rigar Argentina, " Messi ya ci gaba da cewa.
"Tsawon shekara 20, har ma a lokacin da muke fuskantar kalubale, ban daina sa kwazo ba, ina bayar da dukkan gudummuwar da zan iya yi, kuma koda yaushe ina son kasancewa cikin tawagar.
''Raina zai matukar bace ganin ba zan ci gaba da buga wa tawagar wasanni ba, domin da zan iya zan so na kasance a cikinta har karshen rayuwata.
"A wannan lokacin ina ta yin magana fiye da yadda na taɓa yi, saboda kawai ba na son wannan lokacin ya ƙare.
"Amma ina ganin lokaci ya yi da zan yi ritaya. Gasar cin kofin duniya ta ƙarshe mun yi kokari sosai bayan duk abin da muka fuskanta. Mun isa wasan ƙarshe da da fatan lashe kofin, amma mun iya kokarinmu har zuwa ƙarshe, kamar yadda muka saba.
Messi zai ci gaba da taka leda a matakin kuniya tare da Inter Miami mai buga Major League Soccer ta Amurka, inda yake da kwantiragi da zai ci gaba har zuwa ƙarshen kakar 2028.
A daren da aka gudanar da bukukuwa ban kwana da tsohon dan wasan Barcelona da Paris St-Germain tun daga farko har ƙarshe a babban birnin Argentina, ana yawan ganin Messi yana nuna alamun yadda wannan lokaci yake taba masa zuciya.
An ɗauki hotonsa yana share hawaye yayin da yake cikin motar da ke ɗauke da takwarorinsa zuwa filin wasa, sannan kuma ya sake nuna alamun damuwa a fuskarsa, yayin da ake rera taken ƙasar Argentina cikin armashi.
Kafin a fara wasan, an yi gagarumin wasan wuta, kuma yayin da 'yan wasan suka fito filin, an shimfiɗa wata babbar riga ta Argentina mai ɗauke da shahararren lamba ''10'' ta Messi da kuma kalmar ''gracias'', wato "na gode".
Bayan mintuna 10 da fara wasan, aka dakatar da karawar domin sake yin wasan wuta, yayin da magoya baya suka sake tashi tsaye suna yi wa Messi jinjina, sannan dukkan 'yan wasan Benin suka yi musabaha da shi.
Bayan shagalin ya lafa, Messi ya kasance a tsakiyar kusan duk wani hari da Argentina ta kai, kamar yadda ya saba yi. An tare kwallo biyu da ya yi a bugun tazara da kasa amfani da manyan damarmakin da ya samu.
Sai dai shi ne ya bara da dukkan kwallo biyun da aka ci, sannan ya zura ta uku a raga a bugun fenariti, kuma daga karshe ya buga kwallo ta bugi turke.
"Duniya na gode maka da duk abin da ka yi wa ƙwallon ƙafa."
'Duniya na gode maka da duk abin da ka yi wa ƙwallon ƙafa'
"Wannan mafarki ne da ya zama gaskiya. Ban taɓa tunanin zan zama kocin ɗan wasan da ya fi kowa fice a tarihi ba," in ji kocin Argentina, Lionel Scaloni, bayan kammala wasan.
"Muna matuƙar godiya gare shi har abada saboda ya ba mu damar kasancewa tare da shi.
"Hawaye na zuwa ne saboda abubuwa da dama da suke rayawa a cikin raina. Ba za mu ƙara ganinsa ba yana buga wa Argentina tamaula, kuma hakan zai kasance abin baƙin ciki. Ya bar mana gibi mai matuƙar girma.
Ɗan wasan Brazil, kuma tsohon abokin wasansa a Barcelona da Paris St-Germain, Neymar, ya rubuta a shafinsa na X cewa:
"Ba Argentina kaɗai ke gode maka ba, duniya ma tana gode maka saboda duk abin da ka yi wa ƙwallon ƙafa.
"Na gode da yadda ka sa na ƙara son ƙwallon ƙafa. Abin alfahari ne a gare ni na taɓa buga wasa da kai, sannan ya fi haka girma kasancewa tare da kai wajen rubuta tarihi."
Rodrigo De Paul, babban abokin Messi kuma abokin wasansa a matakin ƙasa da kuma ƙungiya, ya ce:
"Ya taimaka min wajen bunkasa wasanni na, har ma a matsayina na mutum.
"Na zama mutum mafi nagarta, ɗan Adam mafi nagarta, ɗan wasa mafi nagarta, uba mafi nagarta kuma aboki mafi nagarta.
Tsohon abokin wasansa a Argentina, Ángel Di María, ya ce:
"Ganin sa cikin farin ciki da kuma wannan nutsuwar da ke tattare da sanin cewa ya bayar da duk abin da yake, shi ne abin da ke sa mu duka farin ciki.
"Ina gode masa har tsawon rayuwata."