Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwa 10 da ke kashe aure a arewacin Najeriya - Malamai
A shekarun baya idan aka ji aure ya mutu a unguwa ko a gari akan shiga zulumi ko tambayar dalili bisa makomar miji ko matar ko 'ya'ya saboda rabuwar iyayensu.
Sai dai yanzu zamani ya zo da sauyi ta yadda a wasu lokutan mutuwar aure bai zamo wani babban abin jimami ba, inda ake samun ma'aurata 'yan ƙasa da shekaru 30 aurensu yake mutuwa, a wani lokacin ma fiye da mutuwa daya, wani abu da masu lura da al'amuran yau da kullum ke ganin akwai firgici a cikinsa.
Wata ƙididdiga ta Hukumar Hizba ta jihar Kano ta nuna cewar aƙalla gwamman aure ne ke mutuwa a wata guda, a jihar da tafi kowacce yawan al'umma a arewacin Najeriya.
Malam Aminu Daurawa ya ce wannan ƙididdigar ta iya hukumar Hizba ce wadda kuma su aikinsu ya fi ƙarfi a gyaran aure da sulhu ga ma'aikata.
Ya ce ba su da ƙididdigar kotu da ta ɓangaren fada, "kuma mafi yawan auren da ke mutuwa yana mutuwa ne a kotu".
Wannan ne ya sa BBC ta tuntubi wasu malamai kuma masana zamantakewar rayuwa, wadanda suka haɗa da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Farfewa Mansur Isa Yelwa da kuma Dakta Abdallah Usman Gadon Ƙaya.
Malaman uku sun yi ittifaƙin cewa dalilai 10 na janyo mutuwar aure ƙarƙashin rabe-rabe huɗu da suka hada da ta ɓngare miji da na ɓangren mata da na iyaye da 'yan uwa da kuma na al'umma.
Rashin yarda da juna
Dr Abdallah Gadon Ƙaya ya ce da yawan ma'aurata a yau suna zaman aure ne ba tare da yarda da juna ba ɗari bisa ɗari.
"Aure abu ne da yarda da aminci suke taka rawa sosai a ciki, amma da zarar an raba su ko an gaza samunsu to aure zai fuskanci damuwa,".
Bibiyar juna ma'aurata suke yi a yau, "me yake ciki ko me take ciki" sai shaiɗan ya shiga ya riƙa angiza ma'auratan suna jin kamar suna cutar juna.
Babu wanda a al'ada ko addini aka ce sai ya bibiyi wayar dan uwansa in ji Sheik Abdallah, "amma a yau in wani tsakaninsu ya hana ɗayan lambar sirrinsa sai fitina ta faru".
A mafi yawan lokuta idan ka yi komai dan Allah sai Allah ya zama gatanka cikin lamuranka in ji Gadon Kaya.
Zalunci
Ma'aurata kan zalunci junansu a zamantakewar yanzu musamman idan suka gaza samun abin da suka yi tsammani daga juna, in ji Farfesa Mansur Yelwa.
Mu da muke sasancin aure a ko da yaushe muna ganin yadda maza ke zaluntar mata, babu abinci, babu kulawar da ta kamata.
"Wani ko karatun yaransa bai damu da shi ba, sai su kai shekarun tasawa amma babu ko ɗaya da ke makaranta, in ji Dr Abdallah Gadon ƙaya.
Ya ƙara da cewa su ma mata sukan zalunci maza su riƙa yi musu sata daga kuɗi zuwa kayan abinci. Wani lokacin maigidan ya kawo komai na gida amma sai a yi kwanaki ba a yi masa girki ba.
Yana daga cikin zaluncin da ma'aurata ke wa juna a yau, yadda suke cakuɗa "addini da son ransu don biyan buƙatarsu".
Farfesa Yelwa ya ce "a ƙasar Hausa girki al'ada ce mai daɗaɗɗen tarihi, wadda Larabawa ba su damu da ita ba, sai ka ji a yau ana rikici wai mace ba za ta riƙa yi wa mijinta girki ba, kuma da sunan koyarwar addini".
Cin amana
Cin amanar juna da ɓoye muhimman batutuwa na karya ginshiƙin ginin aure, in ji Sheik Aminu Ibrahim Daurawa shugaban Hukumar Hizba ta jihar Kano a Najeriya.
Malamin ya ce a yau lamarin waya ya ƙara ta'azzara wannan lamari, mace ko namiji za su riƙa soyayya da wasu a waje tare da cewa suna da aure ba su rabu ba.
"A wasu lokuta matan aure kan zubar da cikin mazajensu ba tare da mazan sun sani ba. Wani lokacin namiji ya ƙara aure ba tare da sanin matarsa ta gida ba," to dun irin wadannan ake kallo a cin amanar da idan ɗaya ya ji ba zai hakura ba, a ƙarshe sai an kassara auren.
Na daga cikin cin amanar aure mu'amala da ƙawayen da ke kai mata wajen bokaye, ko kuma 'yan tsibbu domin biyan wata buƙatarsu, ko dai mallakar miji ko iyayensa ko kuma hana shi aure.
Ƙazanta
Sheik Abdallah Gadon Ƙaya ya ce mafi yawan matan auren da ake gani a gidan biki ko Tiktok tsaf-tsaf da yawa "ƙazamai ne, sai za su unguwa suke gyara".
Katarar da 'yan mace ba ta damu da askin gashin jikinta ba, ko kuma wanke ƙafarta ba. Wasu in ka shin-shina kansu za ka ji har wari yake yi saboda rashin gyara.
Amma a mafi yawan lokaci za ka yi wa wasu matan uzuri in ji Sheik Abdallah, dalili kuwa shi ne mazansu ke zalintarsu ba sa ba su kuɗin gyara jiki.
A ɓangaren maza kuwa kaza kazantarsu ta haɗa da ta rashin "wanke baki ko ɗan kamfai ba sa aski, sannan kuma da dama ba su damu da turare ba", in ji Malam.
Malamin ya ce ko saduwa ta fi dadi da gamsarwa cikin tsafta da kamshi da kyawun yanayi.
Bambancin shekaru
Bambancin shekaru wani abu ne da ke takararwar gani wajen rura rikicin rashin fahimta tsakanin ma'aurata.
Dattijo mai shekara 65 ya auri yarinya 'yar shekara 20 kuma yana so ta riƙa yi masa irin abin da matarsa mai shekara 50 take masa na nuna kulawa da kare haƙƙoƙi da iyakokin aure.
Shekaru kimanin 45 ne ɓanbanci tsakaninsu wanda za su iya sauya zamani.
"Duk yadda ka kai da iya soyayya banbancin shekaru ba za su bari ku fahimci juna ba. Ita kuma ƙarama ce lokacin da take buƙata daga namiji da wuya ta samu tun da shi ya manyata al'amuran gabansa yake yi, kamar yadda malam ya yi bayani.
"Mata suna son soyayya kuma da daidai su, da ta ga ta sauya sai ta fara zargin ba sonta yake ba, ko kuma ya aureta ya sauya".
Shi ma in ya gaza samun yadda yake tsammani daga wurin yarinyar da ya aura hakan kan zama wata fitina da ka iya kaiwa ga rabuwar aure in ji Malam.
Tsoma bakin iyaye da 'yan‘uwa
Iyaye da dama a zamanin nan kan nuna son kulawa da yaransu wadda a lokuta da dama kan wuce iyaka.
Cikin irin wannan kulawar sukan so su nuna iko da abubuwan da suke faruwa a gidajen 'ya'yansu.
Kamar mahaifiyar miji da mata 'ya'yansu ke ce kiransu a zamanance 'Hawan Jini ko Olsa' su na neman sanin duk wani abu da ɗansu ke ciki da iyalansa a gidansa.
"Idan mahaifiyar miji ko ƙannansa na kan abin da yake yi wa matarsa, amma duk abin da ya yi wa 'ya'yansa ba sa damuwa saboda 'ya'yansu ne, in ji Daurawa.
Ya ƙara da cewa hakan ya haifar da mummunar tsana tsakanin surukan, amma duk wacce ta riƙe mutuncinta ba a samun haka da ita.
A ɓangaren iyayen mata kuwa, mafi yawansu damuwarsu me 'yarsu za ta samu, saboda ka da a mutu a barta da yara.
"Wani lokacin uwar matar ce za ta tilastawa mijin sai ya bar 'yarta ta yi aiki, ko kuma ita za ta riƙa faɗa mata me za ta riƙa yi domin samun kuɗi a hannun mijinta," in ji Daurawa.
Malam Daurawa ya ƙara da cewa wata kuma kullum tana cikin tambayar 'yarta me take ciki a gidanta, me ta dafa, ko me suka yi da maigidanta?
Kishi da ya wuce ka’ida
Babu wanda zai ce maka kishi bai halasta ba, amma yadda wasu ke ɗaukar shi da za fi ne ke bayar da mamaki.
Maza da yawa suna nuna kishi irin wanda ko a addini babu shi, za su ce ba su yarda matansu su mallaki waya mai whatsApp ba, ko duk wani chat da ake yi.
"Maza da dama sun rabu da matansu saboda suna Facebook, ko WhatsApp, wanda matan da yawa da 'yan uwansu suke magana ba da kowa ba. Kuma mazan ko bincike ba su yi suke ɗaukar mataki daga baya su yi ta nadama," in ji Daurawa.
Su kuwa mata an sansu da kishi ba zai zama wani baƙon abu ba amma irin wanda ake samun rahotannin kashe maza ko watsa musu ruwan zafi ko cire musu mazakuta shi ne wanda ya yi muni in ji Shehin Malamin, kuma ko shari'a ba ta yarda da irin wannan ba.
Kwatanta abokin zama da wasu
Kowa da irin arzikin da Allah ya hore masa da kuma irin matakan da suke kai, kuma ya kamata duk wani ɗan Adam ya amince da banbance-banbance da Allah ya tsara tsakaninsu.
Kalmomi irinsu "Dubi mijin wance" ko kuma "Dubi matar wane" sukan karya zukatan abokan zama daga maza har mata.
"Ba gazawa ba ce idan mutum ya gaza a wani ɓangare na rayuwa, idan aka bi a hankali sai a ga a wani ɓangaren kuma ya kai matuƙa, in ji Malam Daurawa.
Malam ya ce idan ba ki da gashin wance bai kamata ki ce za ki yi kitson wance ba, haka zalika shi ma namijin.
Hakan kuma yana kaiwa ga ingiza abokin zama ya shiga wata hanya mara kyau, ko kuma ya fusata ya haƙura da abokin zamansa.
Rashin girmama juna
Wasu ma'auratan rikici kan dabaibaye zamantakewarsu ta yadda kullum suna cikin faɗa da ɓacin juna.
A kowacce irin zamantakewa ana samun rikici a cikinta, kuma ana warware shi cikin girmamawa da mutuntawa.
Bahaushe kan ce ko tsakanin harshe da haƙori akan samun saɓani, amma ana shiryawa.
"Idan ma'aurata suka yi faɗa yanzu cin mutuncin juna suke yi, su zagi juna koma iyayensu a wani lokacin," in ji MMalam Daurawa.
Wannan na cikin matsalolin da suke sa a yi sakin aure cikin rashin daraja da rashin girmama juna.
Kullum malam ya ce suna sasanta aure amma na rashin ganin mutuncin juna yana da wuyar sha'ani.
Shaye-shaye da mugayen abokai
Matsalar shaye-shaye ta tashi daga kan tituna zuwa cikin gidaje, iyaye da mataye da mazajen aure na yawan kokawa kan yadda shaye-shaye ya zama ruwan dare tsakanin mutane.
Aure da yawa ya mutu saboda matsalar shaye-shaye da musamman ta ratsa gidajen matan aure.
Malam Daurawa ya ce, sun sha ganin yadda abokai ko ƙawaye ke tasiri wajen koyawa magidanta shaye-shaye.
"Wani lokacin ma'auratan ne ɗaya yake koyawa ɗaya sai ya zama su duka suna yi, zaman lafiya shi ne a nesanta su da juna, saboda matuƙar suna tare matsalar ba za ta kau ba".
Malamin yace wannan matsala tana cikin waɗanda suke samun kokensu a kai a kai kuma ta ma riga ta zama ruwan dare.