Ana samun rabuwar kai, bayan da Ronaldo ya bar tawagar Portugal, Cristiano Ronaldo
Yayin da Lionel Messi ke shirin yin ban-kwana a matakin gwarzo bayan nasarar da ya samu a rayuwarsa da ya buga wa Argentina tamaula, shi kuwa Cristiano Ronaldo na cikin fushi, wanda ya bar fili zuwa dakin canja kayan yan wasa a fusace a karawa da Portugal ta yi a Norway.
Bayan gasar Kofin Duniya, Messi mai shekara 39 ya yanke shawarar yin ritaya daga buga wa Argentina wasanni, yayin da Ronaldo mai shekara 41 ya zaɓi ci gaba da taka leda a Portugal.
Tuni aka tsayar da ranar Talata a wasan ban kwana da Messi a wasan sada zumunta da Benin, inda aka gayyaci yan wasan da suka lashe kofin duniya a 2022 tare da Messi, domin su taya shi murnar yin ban kwana da tawagar.
Shi kuwa Ronaldo, wanda ya zauna benchi ya fusata bayan da aka sa shi ya motsa jiki, daga baya ba a saka shi ba a wasan Norway, sannan ya samu tabbacin cewar ba za a saka shi a karawa da Denmark ba a Nations League, ya tattara kayansa ya bar sansanin Portugal.
Ɗan wasan da ke taka leda a Al-Nassr ta Saudiyya ya ci wa Portugal ƙwallo 146 da buga mata wasa 234 — shi ne kan gaba a wannan kwazon a tawagar.
Bayan wannan babban rikici da sabon kocin Portugal, Jorge Jesus - yanzu ya ce za a yi wa Ronaldo maraba idan yana son komawa, yayin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin Ronaldo da wakilansa da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Portugal domin nemo mafita.
Ko da yake Ronaldo ba zai iya ci gaba da buga ƙwallo har abada ba, amma dai ya kamata a yi masa biki na kasaita a duk lokacin da ya yanke shawarar yin ritaya.
Magoya bayansa na ci gaba da nuna goyon baya ga tsohon dan wasan Manchester United da Real Madrid da Juventus, inda kafafen sada zumunta suka cika da saƙonnin da ke goyon bayan Ronaldo tare da sukar Jesus.
A gefe guda kuma, wasu magoya baya da kuma wasu daga kafafen yaɗa labarai a Portugal sun soki abin da suke gani a matsayin halin son kai.
Kafin wasan Portugal na gaba da Denmark a watan Nuwamba, ana sa ran Ronaldo zai yanke shawara ko zai koma buga wa Portugal wasannin ko kuma ya ui ritaya kai tsaye.