Fasinja ya rasu a jirgin Kenya Airways jim kaɗan kafin ya sauka a Legas
Wani fasinja ya rasu a cikin jirgin Kenya Airways da ke tafiya daga Nairobi zuwa Legas, bayan ya daina motsi jim kaɗan kafin jirgin ya sauka a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed.
Kenya Airways ya ce lamarin ya faru ne jiya Talata da ƙarfe 9:20 na dare agogon Najeriya, kimanin mintuna 20 kafin jirgin ya sauka a Legas.
Rahotanni sun ce ma'aikatan jirgin sun kai wa fasinjan agajin gaggawa tare da bin ƙa'idojin da aka tanada domin irin wannan yanayi.
Jirgin ya sauka da ƙarfe 9:41 na dare, inda jami'an lafiya suka shiga jirgin. Bayan sun duba fasinjan, sun tabbatar da cewa ya rasu.
Kamfanin jirgin bai bayyana sunan fasinjan ko musabbabin mutuwarsa ba.
Kamfanin dai ya ce yana bayar da gudunmawa da yin aiki tare da iyalan mamacin, hukumomin Najeriya da kuma hukumomin kula da zirga-zirgar jiragen sama.