Jihohin Najeriya da jam'iyyun hamayya ke da ƙarfi gabanin zaɓen 2027

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 7

Yayin da shirye-shiryen siyasa ke ci gaba da ɗaukar zafi gabanin zaɓen 2027, jam'iyyun hamayya na ƙara mayar da hankali kan jihohin da suke da ƙarfi domin riƙe kambinsu, da kuma ƙoƙarin ƙwace wasu jihohin daga APC saboda tasirin magoya baya.

Duk da cewa APC ce ke mulki a matakin tarayya, akwai wasu jihohi da jam'iyyun hamayya irin su ADC da NDC da PDP da APM suka kafa tubali mai ƙarfi, lamarin da ya sa jihohin suka zama muhimman wuraren fafatawar siyasa.

A zaɓen 2023, wasu daga cikin waɗannan jihohi sun nuna yadda jam'iyyun hamayya za su iya kalubalantar APC, inda suka samu nasarori a zaɓen gwamnoni da ƴan majalisu da ma na shugaban ƙasa.

Masana siyasa na ganin cewa yadda waɗannan jihohi za su kasance a shekarun da ke tafe zai iya taka muhimmiyar rawa wajen tantance alƙiblar zaɓen 2027, musamman idan har jam'iyyun hamayya suka ci gaba da haɗa kai da kuma riƙe sansanoninsu.

To amma waɗanne ne jihohin da jam'iyyun hamayya suka fi ƙarfi a Najeriya, kuma mene ne ya sa suke ci gaba da zama ƙalubale ga jam'iyyar APC da ke kan mulki?

Kano - NDC

Jihar Kano da ke arewa maso yammcin Najeriya ta kasance kan gaba cikin jerin jihohin da jam'iyyar hamayya ta NDC ke da ƙarfi a cikinta.

A jihar Kano NDC, na ƙarƙashin ikon jagoran kwankwasiyya, Dr Rabiu Musa Kwankwanso, wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan siyasar Najeriya.

Kwankwaso na da matuƙar tasiri a siyasar Kano, inda a baya ya sha tsayar da ƴantakarar, yayin da yake jam'iyyar hamayya kuma ya samu nasara mai yawa.

Ko a 2023 jam'iyyar ta NNPP mai hamayya a lokacin ta kayar da APC mai mulki, inda ta ƙwace kujerar gwamnan jihar, tare da samun sanatoci biyu cikin uku na jihar, baya ga ƴan majalisar tarayya masu yawa.

Haka ma a zaɓen 2019 duk da cewa bai samu nasarar ƙwace kujerar gwamna ba, amma ya samu ƴanmajalisar dokoki da na tarayya masu yawa.

Yanzu haka NDC ta tsayar da Comrd. Aminu Abdussalam, wanda ya kasance tsohon mataimakin gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, domin fafatawa da gwamna, wanda ya nzu ɗan APC ne.

Adamawa - NDC/ADC

Jihar Adamawa na ɗaya daga cikin jihohin da ake kallon za su taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya a 2027, musamman saboda kasancewarta mahaifa ce ga Atiku Abubakar, wanda ya daɗe yana da tasiri a siyasar jihar da ma yankin Arewa maso Gabas.

Kasancewar Atiku na cikin ADC, kuma shi ke yi mata takarar shugaban ƙasa a 2027, masu sa ido kan al'amuran siyasa na ganin jam'iyyar ADC za ta samu gagarumin tagomashi a Adamawa, domin Atiku na da ɗimbin magoya baya da suka kasance tare da shi tsawon shekaru a jihar.

A gefe guda kuma, Sanata Aishatu Dahiru Ahmed, wadda aka fi sani da Binani, ɗaya daga cikin fitattun ƴan siyasar jihar na takarar gwamna a NDC.

Binani ta nuna ƙarfinta a zaɓen gwamnan Adamawa na 2023, inda ta zo ta biyu bayan fafatawa mai zafi da ta ja hankalin jama'a a faɗin ƙasar.

Wannan ne ya sa Adamawa ta kasance ɗaya daga cikin jihohin da za a sa ido sosai a kansu, kasancewar tana da manyan ƴan siyasa masu tasiri daga ɓangarorin siyasa mabambanta.

Bayelsa - NDC

Jihar Bayelsa na daga cikin wuraren da jam'iyyun hamayyar NDC za ta iya yin tasiri a zaɓen 2027, musamman saboda tasirin da shugabannin siyasa daga jihar ke da shi a yankin Neja Delta.

Tsawon shekaru, Bayelsa ta kasance ɗaya daga cikin jihohin da siyasar cikin gida da ta ƙasa ke da alaƙa ta kut-da-kut.

Ɗaya daga cikin abubuwan da ke ƙara wa NDC ƙarfi a jihar shi ne kasancewar shugaban jam'iyyar na ƙasa ɗan asalin Bayelsa ne.

Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa wannan na iya taimaka wa jam'iyyar wajen jan hankalin magoya baya da kuma faɗaɗa tasirinta a cikin jihar.

Kebbi - ADC

Jihar Kebbi na daga cikin jihohin da ake ganin jam'iyyar ADC za ta iya taka muhimmiyar rawa a cikinsu a zaɓen 2027, musamman bayan sauye-sauyen da ake gani a siyasar jihar.

Duk da kasancewar APC na da tasiri a jihar, wasu masu nazarin siyasa na ganin cewa hamayya na ƙoƙarin gina ƙarfi a Kebbi.

Ɗaya daga cikin fitattun jiga-jigan da ake dangantawa da wannan yunƙuri shi ne tsohon Ministan Shari'a kuma Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami, wanda ke yi wa ADC takarar gwamna a jihar.

Malami na daga cikin sanannun ƴan siyasar Kebbi kuma yana da tasiri a fannoni daban-daban na siyasar jihar sakamakon doguwar hulɗarsa da al'ummar yankin.

Wasu masana siyasa na kallon Kebbi a matsayin ɗaya daga cikin jihohin da za a sanya ido sosai a kansu a zaɓen 2027.

Sokoto - ADC

Baya ga jihar Kebbi, Sokoto mai maƙwabtaka na daga cikin jihohin da ake ganin tasirin ADC.

Tsohon gwamnan jihar, Sanata Aminu Waziri Tambuwal - wanda ke da tasirin magoya baya - shi ke jagorantar jam'iyyar a jihar.

Tambuwal ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ƴan siyasar Arewa da suka gina ƙaƙƙarfan sansanin magoya baya tsawon shekaru.

Tasirinsa a Sokoto ya bayyana a zaɓuɓɓukan da suka gabata, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara alkiblar siyasar jihar da kuma haɗa kan magoya bayansa.

Masana na ganin cewa irin wannan tasiri na iya taimaka wa ADC wajen kafa ƙwaƙƙwarar hamayya a jihar.

Kaduna - ADC

Jam'iyyar ADC na da matuƙar tasiri a jihar Kaduna, musamman bayan sauyin sheƙar wasu manyan ƴan siyasa zuwa jam'iyyar.

Jihar na da muhimmanci a siyasar Arewa saboda yawan masu zaɓe da kuma tasirin da take da shi a matakin ƙasa.

Ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan da ke ƙara wa ADC ƙarfi a Kaduna shi ne tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmad El-Rufai, wanda ke da ɗimbin magoya baya da kuma tasiri a siyasance.

Masana siyasa na ganin cewa shigarsa cikin ADC na iya taimaka wa jam'iyyar wajen faɗaɗa tasirinta a yankin Arewa maso Yammacin ƙasar.

Bayan El-Rufai, Ashiru Kudan, wanda a yanzu ke yi wa jam'iyyar takarar gwamnan, shi ma na da ɗimbin magoya baya.

Gombe - PDP

Jihar Gombe na daga cikin jihohin da PDP ke da ƙarfi da kuma kyakkyawan fata a zaɓen 2027.

Duk da sauye-sauyen da ake samu a siyasar Najeriya, jam'iyyar na ci gaba da neman riƙe abin da take ganin sansaninta ne na siyasa a jihar.

Shigar Farfesa Ali Isa Pantami, cikin jam'iyyar ya taimaka wajen farfaɗo da ruhinta a jihar Gombe.

Pantami na da farin jini a tsakanin wasu al'ummomi a jihar, musamman saboda sanin da aka yi masa a fagen ilimi da harkokin fasaha.

Masana siyasa na ganin cewa shahararsa da ɗimbin magoya bayansa na iya taimaka wa PDP wajen ƙarfafa matsayinta a jihar.

Kwara - PDP

Baya da Gombe, wata jihar da har yanzu PDP ke da tasiri ita ce jihar Kwara da ke yankin arewa ta tsakiyar Najeriya.

Tasirin tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, da ɗan takarar sanatan Kwara ta Tsakiya na jam'iyyar, Saliu Mustapha, wanda ke samun goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike.

Bauchi - APM

A jihar Bauchi jam'iyyar APM ce ake ganin za ta yi tasiri a siyasar jihar, duk da cewa akwai jam'iyyun NDC da PRP, waɗanda su ma ke a tasiri.

A wannan shekarar ne dai gwamnan jihar Bala Mohammed ya fice daga jam'iyyar PDP tare da komawa APM, inda ya tsaya takarar Sanata, wani abu da ya ƙara wa jam'iyyar ƙarfi a jihar.

Masana siyasa na ganin cewa wannan sauyi na iya ƙara wa APM karɓuwa a Bauchi, musamman idan har jam'iyyar ta samu nasarar jawo wasu manyan ƴan siyasa da masu ruwa da tsaki zuwa cikinta kafin zaɓen 2027.

Oyo - APM

Baya ga Bauchi, ana ganin jihar Oyo a matsayin jihar da APM za ta yi gagarumar tasiri a zaɓen 2027.

Kamar dai Bauchi, shi ma gwamnan jihar Seyi Makinde bayan ficewarsa daga PDP, jam'iyyar APM ɗin ya koma, sannan ya tsaya mata takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Makinde na da ɗimbin magoya baya da kuma tsarin siyasar Oyo tsawon shekarun mulkinsa, kuma hakan na iya taimaka wa jam'iyyar wajen ƙarfafa tasirinta a tsakanin masu zaɓe.

Tasirin gwamnan jihar da kuma ƙudurinsa na neman shugabancin ƙasa na iya sanya jihar ta kasance muhimmin sansanin jam'iyyar a yankin Kudu maso Yamma.

Osun - Accord

Sai kuma jihar Osun, inda jam'iyyar Accord ke da tasiri bayan da gwamnan jihar, Ademola Adeleke ya sauya sheka zuwa cikinta bayan ya bar PDP a farkon shekarar nan.

Bayan komawarsa Accord, Gwamna Adeleke ya kuma sake lashe zaɓen gwamna a ƙarƙashin tutar jam'iyyar, wani abu da ke nuna ƙarfin tasirin jam'iyyar a jihar.