Yadda ƴan mata biyu tagwaye suka rasu a cikin sa'a 48 a Yobe

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Wannan labari ya ɗauki hankalin jama'a ba kawai saboda rasuwar ƴan'uwan tagwaye cikin kwanaki biyu ba, har ma saboda kusancin da ke tsakaninsu da kuma matsayin iyayensu a fannin kiwon lafiya a Najeriya.

Dr. Hadiyah Usman da Dr. Aidah Usman, masu shekaru 28, duk suna fama da cutar sikila tun suna yara.

Baya ga baƙin cikin rasa 'ya'ya mata biyu cikin kwanaki biyu, labarin rasuwar tagwayen ya kuma haska irin tasirin da cutar sikila ke ci gaba da yi a Najeriya, ɗaya daga cikin ƙasashen da ke da yawan masu fama da cutar a duniya.

A shafukan sada zumunta, mutane da dama musamman matasa sun bayyana alhini da kaɗuwa ga iyalan tagwayen, musamman ganin cewa sun rasu cikin sa'o'i 48 kacal tsakani kuma dukkansu matasa likitoci.

Yadda tagwayen suka rasu

A cewar majiyoyin iyali, Hadiyah ta kamu da matsananciyar rashin lafiya sakamakon rincaɓewar cutar sikila, inda aka kwantar da ita a Federal Medical Centre da ke Nguru a jihar Yobe kafin daga bisani ta rasu a ranar Juma'a.

A daidai wannan lokaci kuma, ƴar uwar tagwaitakarta Aidah tana karɓar magani a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri saboda irin wannan matsala ta lafiya.

Bayan an sallami Aidah daga asibiti sakamakon samun sauƙi, ta koma Nguru domin ta yi jimamin rasuwar 'yar uwarta. Sai dai kuma ƙaddara ta riga fata, ita ma ta rasu a ranar Lahadi, sa'o'i 48 kacal bayan rasuwar Hadiyah.

Tagwayen dai ƴaƴa ne ga Farfesa Hadiza Abdullahi Usman, Daraktar Kula da Asibitin na FMC Nguru, da Farfesa Usman Abdullahi, babban likita mai ba da shawara kuma malami.

Rasuwarsu ta haifar da jimami mai zurfi a tsakanin iyalansu, abokan aiki da kuma ma'aikatan lafiya.

Bayanai daga iyaye da iyalin mamatan ya nuna cewa ba sabon abu ba ne ga tagwayen su kamu da rashin lafiya a lokaci guda, ko da suna zaune a wurare daban-daban.

Sun ce suna da kusanci na musamman, suna karatu tare, suna cin abinci tare, kuma suna yawan kasancewa tare tun suna ƙanana.

Mece ce cutar Sikila?

Cutar sikila ko amosanin jini na ɗaya daga cikin cututtukan da za a iya cewa na neman zama ruwan dare, saboda yadda ake yawan samun yin aure tsakanin masu rukunin jini AS da AS ko SS da AS.

Larurar amosanin jini, wato sickle cell anaemia larura ce da ke raunata mai fama da ita har ma da iyalan mai fama da ita, da al'umma baki daya.

An ware ranar 19 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin ranar yaƙi da cutar amosanin jini wato sikila a duniya. Rana ce da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware domin faɗakar da al'umma kan wannan cutar a duniya.

Bincike ya nuna cewa duk shekara ana haihuwar jarirai 300,000 a duniya kuma rabi daga wannan yawan a Najeriya ake haihuwar su. Daga cikin 150,000 na Najeriya ɗin, 100,000 ne ke mutuwa duk shekara.

Alƙaluma sun nuna cewa mafi yawan masu cutar suna arewacin ƙasar ne. Masana kiwon lafiya sun yi amanna cewar rashin yin gwajin jini kafin aure yana taka rawa sosai wajen haifar yara masu ɗauke da cutar sikila a ƙasar.