Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me zai faru idan kuna shan paracetamol fiye da kima?
Ƙungiyar Likitocin Iyali ta ƙasar Wales (RCGP) ta ba da shawarar cewa mutane su riƙa karanta takardar bayanin magani da umarnin amfani da ke cikin ƙunshin kowanne magani kafin amfani da shi.
Haka kuma, ta ce yana da muhimmanci a tuntuɓi likita kafin shan kowane irin magani.
A cewar Hukumar Lafiyar Birtaniya (NHS), shan sinadarin paracetamol fiye da adadin da aka amince da shi na iya haifar da mummunar illa ga hanta da kuma ƙoda.
Daga cikin alamomin farko na gubar paracetamol akwai tashin zuciya, amai da kuma ciwon ciki.
Wannan lamari ya sake jaddada muhimmancin tabbatar da irin sinadaran da magunguna daban-daban suka ƙunsa, musamman idan mutum yana shan magunguna fiye da ɗaya a lokaci guda.
Me masana ke cewa game da Paracetamol ?
A cewar sabbin alƙaluman da Hukumar Kididdiga ta Birtaniya (ONS) ta fitar, mutuwar mutum 27 a ƙasar Wales a shekarar 2024 ta samo asali ne daga maganin paracetamol, inda aka bayyana maganin a matsayin musabbabin mutuwar a takardun shaidar mutuwa.
Shugaban ƙungiyar likitocin Wales, Dokta Will McIntosh, RCGP, kuma likitan kula da lafiya na farko, ya ce ba sabon abu ba ne matasa su sha paracetamol fiye da ƙa'ida ba tare da sun sani ba.
Sai dai ya ƙara da cewa shan magunguna biyu waɗanda dukkansu suke ɗauke da sinadarin paracetamol a lokaci guda na iya haifar da haɗari.
Dokta McIntosh ya bayyana cewa matsin lambar aiki da karatu na sa matasa musamman amfani da magungunan da ake saya ba tare da takardar likita ba.
"Musamman idan mutum na fama da cutar da ƙwayar cuta ta jawo, ko da kuwa ba mai tsanani ba ce, yana da muhimmanci ya samu isasshen hutu," in ji shi.
Ya kuma jaddada cewa a wasu lokuta mutane kan yi watsi da muhimmancin hutu saboda son samun sauƙi cikin gaggawa.
"Ga yawancin irin waɗannan cututtukan, jiki na buƙatar hutu da lokaci domin ya yaƙi kamuwa da cutar. Haka kuma ana iya amfani da magungunan da ake samu ba tare da takardar likita ba," in ji shi.
Ya bayyana cewa kantunan sayar da magunguna suna taka-tsantsan sosai wajen sayar da magunguna masu yawa, don haka galibi ana ƙayyade adadin paracetamol da mutum zai iya saya.
Ya kuma ce likitoci sun fi fahimtar haɗarin shan paracetamol fiye da ƙa'ida, musamman a tsakanin tsofaffi.
Ya ƙara da cewa haɗarin na iya zama mafi muni ga tsofaffin da ba su da isasshen nauyin jiki.
"A irin waɗannan lokuta, alamun cutar na iya zama masu tsanani sosai kuma haɗarin ya kan yi yawa," in ji shi.
"Saboda haka muna fatan yawan irin waɗannan lokuta zai kasance kaɗan ƙwarai," in ji shi.
A ƙarshe, ya shawarci mutane su karanta takardar bayanin magani da kuma umarnin amfani da shi a hankali kafin su fara amfani da duk wani magani.
Abin da za ku lura da shi idan za ku sha paracetamol
A cewar Hukumar Lafiyar Birtaniya (NHS), mafi girman adadin paracetamol da babban mutum zai iya sha cikin sa'o'i 24 shi ne ƙwayoyi takwas na 500mg.
Hukumar ta kuma gargaɗi cewa wasu magunguna masu suna na kasuwa na iya ƙunsar sinadarin paracetamol, don haka ya kamata a karanta takardar bayanin magani da umarnin amfani da shi a hankali kafin a sha.
Sannan ta ce bai kamata mutum ya ci gaba da shan paracetamol na fiye da kwana uku a jere ba tare da tuntuɓar likita ba.
Haka kuma, idan mutum yana shan paracetamol, bai kamata ya haɗa shi da wani magani da shi ma ya ƙunshi wannan sinadari ba.
Wannan ya haɗa da yawancin magungunan da ake amfani da su wajen maganin mura da kuma mura mai tsanani (flu).