Como na harin Chalobah, Everton na dab da siyen Delap

Trevoh Chalobah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Trevoh Chalobah
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Como ta taya ɗan wasan Chelsea Trevoh Chalobah kan euro miliyan 27 (Fam miliyan 23). (Sky Sports - in Italian)

Everton na harin ɗan wasan Chelsea Liam Delap, yayin da suke ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan. (Football Insider)

Brighton ta taya ɗan wasan Atalanta Honest Ahonar kan euro miliyan 34 (fam miliyan 29) don cike gibin dan wasan Jamus Jan Paul van Heckes da zai koma Tottenham. (Ben Jacobs via Football Italia)

Real Madrid ta bi sahun Liverpool da Parsi St-Germain zawarcin ɗan wasan Ivory coast Yan Diomande daga RB Leipzig.(El Debate - in Spanish)

Yayin da ake hasashen komawar Mauricio Pochettino gasar Firimiya, Amurka ta yi masa tayin tsawaita kwantaraginsa a mastyin mai horar da ƴan wasanta na tsawon shekaru biyar. (Talksport)

Inter Milan na iya yin rashin nasara wajen ɗauko dan wasan IngilaCurtis Jones, yayin da Liverpool, kan fam miliyan 34 (euro miliyan 40), yayin da Inter din ta taya shi kanfam miliyan 21.5 (euro miliyan 25), sakamakon kwantaragin sa da zata ƙare a kaka mai zuwa. (Calciomercato - in Italian)

Atletico Madris na ƙoƙarin kwadai tawa dan wasan Arjantina Julian Alverez da ya ci gaba da zama a ƙungiyar, sai dai dan wasan ya dage kan cewar har yanzu ya na son komawa Barcelona don ci gaba da taka leda. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Tuntubar da Newcastle United ke yi kan ɗan wasan Borussia Dortmund Felix Nmecha, ta gano cewar farashin ɗan wasan Jamus ɗin ya zarta kuɗin da ta ke son siyen sa. (Chronicle)

Fatan Manchester United na ƙara ƙarfafa tsakiyar ƙungiyar, na fuskanatar koma baya sakamakon rauni da dan wasan Uruguay Manuel Ugarte ya samu, bayan da aka fitar da shi daga filin wasa, a kan gado ɗaukar marasa lafiya a yayin wasan da ƙasarsa da Sipaniya a gasa cin kofin duniya. (Mail)

Hull City ta nuna sha'awarta na ɗaukar dan wasan Belgium Thomas Meunier, yayin da zarar kwantarginsa ta ƙare a Lille. (Talksport)

Ɗan wasan Manchester United Marcus Rashford na son komawa Barcelona, bayan zamansa a mastyin ɗan wasan aro ya kamala, sai dai Barcelona na kan ra'ayinsu na jira har sai an buɗe kakar siyar da ƴan wasa sannan sai su kamala cinikin siyen ɗan wasan Ingilar. (Teamtalk)