Me ya sa ba a shimfiɗa tutar Saudiyya da Iraki a ƙasa ba a Gasar Kofin duniya?

Asalin hoton, Getty Images
Tutar Saudiyya da ta Iraki ba a shimfiɗa su a ƙasa a lokacin da ake take ƙasa da ƙasa kafin fara wasa a gasar Kofin Duniya, saboda suna ɗauke da rubuce‑rubucen addini.
Ana nuna manyan tutocin kowace ƙasa a filin wasa kafin kowanne wasa.
Mafi yawansu ana shimfiɗa su a ƙasa, yayin da tawagogi ke shiga filin wasa, sannan kuma a naɗe su a ɗauka a fitar daga fili daga nan a take leda.
Sai dai an sami wasu banbance‑banbance.
Wasu tutoci ana ɗaga su sama ba tare da sun taɓa ƙasa ba, kuma wannan ya shafi lokutan wasan da ya haɗa ko dai da Saudiyya ko kuma Iraki.
Ana bai wa tutocin kulawa da tsaurara matakai, kuma dalilin saboda rubutun addini da ke kan tutocinsu
Tutar Saudiyya na ɗauke da Kalmar Shahada – ("Babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Muhammadu manzonSa ne") – wanda aka rubuta a sama da inda takobi yake.
Tutar Iraki kuwa tana ɗauke da Takbiri, kalmar Larabci "Allahu Akbar", ma'ana "Allah ne Mafi Girma", wata kalma da Musulmi ke amfani da ita a cikin addu'o'insu na yau da kullum, a lokutan farin ciki, da kuma a kiran salla.
Rubutun da aka yi a tutar Iraki guntu ne, idan aka kwatanta da na tutar Saudiyya, amma ƙa'idar iri ɗaya ce – rubutaccen saƙon addini mai tsarki da aka saka na din-dindin a kan tutar ƙasashen.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Saboda duka tutocin suna ɗauke da kalmomin da ake amfani da su a cikin addu'a da ibadar Musulunci, ba a son ka ɗauka tamkar ƙyallen da aka saba amfani da shi a koda yaushe – kamar shimfiɗa su a ƙasa da zama a kansu da amfani da su a matsayin tawul, ko tattara su wuri guda cikin rashin tsabta – ana ɗauka a matsayin rashin girmamawa a al'adar Musulunci.
Wannan ba daidai yake da nuna adawa da tutar ƙasar ta hanyar ƙonawa ko taka ta a matsayin cin mutunci na ƙasa ba – abin da ake nufi a nan shi ne kare tsarkin kalmomin da ke kan tutar.
Barin rubutun addini ya taɓa ƙasa ko cikin ƙazanta, ana kallonsa a matsayin cin zarafin addini, ba ƙasar kawai ba.
Ga Saudiyya, wannan ya wuce haka. Ba a lamuntar tutar Saudiyya ta taɓa ƙasa ko ruwa ba, kuma ba a saukar da ita rabin sanda, domin yin hakan ana ganin kamar rage darajar Shahada ce kanta.
Ga magoya baya, ƴan wasa da kuma masu watsa shirye‑shirye kan kasashen biyu, an tunatar da su cewa waɗannan tutoci suna da ma'ana biyu – ta ƙasa da ta addini – kuma ana mu'amala da su a bisa haka.











