Abin da jam'iyyun hamayya ke cewa game da 'yansandan jihohi

'Yansanda

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Batun dokar kafa 'yansandan jihohi a Najeriya na ci gaba da shan suka daga wadanda ke ganin rashin dacewar kafa su.

Wani rukuni da ya a 'yan kwanakin ya yi kukan kura game da lamarin, shi ne jam'iyyun adawar kasar.

Yayin da jam'iyyar hamayya ta ADC ta bayyana shakkunta game da irin hanzarin da ake yi wajen ganin kudirin kafa 'yansandan na jihohi da ke gaban majalisar dokokin Najeriyar ya zama doka, ita kuwa jam'iyyar PRP gani take kamata ya yi a dage wannan batu, har sai bayan zaben shekata ra 2027, idan dai ba da wata mugunyar manufa ake son kafa 'yansandan na jihohi ba.

Wannan batu dai na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin masana harkar tsaro, da daidaikun jama'a da kungiyoyin farar hula, har ma da jam'iyyun siyasa.

Inda galibi suke ta bayyana fargaba ko dari-dari ko ma zargin akwai lauje cikin nadi, game da wannan batu, musamman ma dai ganin yadda ake ta azamar ganin kudirin da ke gaban majalisar dokokin kasar ya zama doka.

Jam'iyyar adawa ta ADC na ganin kafa 'yan sandan jihohi tamfar wata luka-luka ce, wai shukar dafaffen wake domin kuwa babu wani sauyi da hakan zai wanzar.

Faisal Kabir, daya ne daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar ta ADC, ya shaida wa BBC cewa, suna ganin wannan batun na samar da'yansandan jihohi babu abin da zai haifarwa da Najeriya sai matsaloli.

Ya ce," Mun gani a baya a wasu jihohi da aka dauki irin wadannan 'yansandan idan zabe y azo babu abin da suke sai musgunawa 'yan adawa, don haka mu abin da muke so gwamnati ta dakatar da wannan mataki ta je ta yi abin da zai samar da cikakken tsaro da taimakon 'yan Najeriya."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Kuma ya kamata gwamnati ta kara taimakwa jami'an tsaron da ake dasu yanzu wajen kara basu horo da kyautata jin dadi da walwalarsu da kuma samar musu kayan aikin da ya dace." In ji shi.

Ita ma jam'iyyar hamayya ta PRP inda ta tofa nata albarkacin bakinta kan wannan batun inda shugaban jam'iyyar na kasa, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya shaida wa BBC cewa bakin jam'iyyar ya karkata, bayan nazari mai zurfi kan lamarin.

Ya ce," Mu muna ganin yanzu ba lokaci ne na samar da 'yansandan jihohi ba, kada ma a soma, gara a bari ayi a zabe, idan na yi na yi zabe idan 'yan Najeriya sun gamsu da shugaba Tinubu ya dawo kan mulki to idan ya dawo bayan zaben 2027 sai ya samar da 'yansandan na jihohi."

"Mu fargabarmu ita ce muna gani kamar za a samar da 'yansandan jihohi ne ba don kara samar da tsaro ba, kawai za ayi ne don a karfafawa mai karfi wato gwamnatin yanzu na Tinubu." In ji shi.

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya dai ta sha mayar da martani kan zarge-zarge da fargaba da kuma sukar da ake ta yi kan batun na kafa 'yansandan jihohi, inda ta ce abu ne da take ganin ya dace, domin kuwa za a yi wa dokar kafa 'yan sandan na jihohi wasu dangarfai wadanda za su kare hakkin bil'Adama, da gudanar ayyukansu bisa doka da oda, kuma ba tare da wuce gona da iri ba.