Iran ta zargi Amurka da ƙeta yarjejeniya bayan hare-haren soji

Asalin hoton, Getty Images
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana hare-haren da Amurka ta kai a matsayin “karya yarjejeniya a fili,” tana mai cewa hakan ya ci karo da yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin ƙasashen biyu domin kawo karshen yaki.
A cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce harin da Amurka ta kai a gaɓar tekun Iran” ya saɓawa Mataki na 2, Sashe na 4 na Yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya, tare da ƙeta Sashe na 1 na Yarjejeniyar fahimtar juna kan kawo karshen yaki da aka sanyawa hannu a ranar 18 ga Yuni..
Haka kuma, Iran ta bayyana harin da Isra’ila ta kai a Lebanon a matsayin “keta yarjejeniya” tana mai ɗora alhakin sakamakon abubuwan da ke faruwa kan Amurka da sauran ɓangarorin da ta ce suna da hannu wajen goyon bayan matakan da Amurka ke ɗauka kan Iran.
A daren jiya, rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta sanar da cewa jiragen yaƙinta sun kai hari kan rumbunan makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa na Iran, da gabar teku.
Bayan waɗannan hare-hare, Rundunar IRGC ta Iran ta ce ta mayar da martani ta hanyar kai hari kan wuraren da sojojin Amurka ke jibge a yankin.











