Dokoki huɗu masu ruɗani da majalisar Najeriya ta 10 ta amince da su

Asalin hoton, Tajudeen Abbas/X
A ranar Laraba ne majalisar Dattawan Najeriya ta amince da dokar kafa ƴansandan jihohi a faɗin ƙasar.
Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio, ne ya sanar da hakan bayan samun goyon bayan mafi rinjayen sanatoci a zaman majalisar na ranar Laraba.
Wannan na zuwa ne bayan shafe shekaru ana tafka muhawara kan matakan da ake son ɗauka domin magance matsalolin rashin tsaro a ƙasar.
Daya daga cikin muhimman tanade-tanaden ƙudirin shi ne bai wa gwamnonin jihohi ikon naɗa kwamishinonin ƴansanda na jihohinsu, amma sai bayan majalisun dokokin jihohin sun tantance kuma sun amince da su.
Tuni dai dama majalisar wakilan ƙasar ta amince da dokar kafa ƴansandan jihohin, a wani mataki na yaƙi da matsalar tsaro da ƙasar ke fama da ita.
Ƴanƙasar da dama dai na nuna fargaba game da amincewa da ƙudirin, suna masu zargin cewa gwamnonin jihohi za su riƙa amfani da ƴansandan ta hanyar da ba ta dace ba.
Sai dai ba wannan ne karon farko da wannan majalisar ta 10 ke amincewa da dokoki, duk kuwa da nuna adawa da dokokin da ƴanƙasar ke yi.
A wannan muƙala mun duba wasu dokoki huɗu da majalisar ta amince da su, duk kuwa da adawa da ƴanƙasar suka nuna.
Dokar haraji

Asalin hoton, Fadar shugaban kasa
A shekarar 2024 zuwa 2025 babu wani abu da ya fi ɗaukar hankalin ƴan Najeriya ta fuskar siyasa fiye da batun sabuwar dokar haraji da gwamnatin shugaba Tinubu ta ɓullo da ita.
Dokar ta shafe watanni masu yawa ana ce-ce-ku-ce a kanta, wani batu da ya raba kan ƴan jam'iyyar APC, ciki har da gwamnonin jihohi da ƴanmajalisa.
A lokacin wasu gwamnoni da ƴanmajalisa, musamman na arewacin ƙasar sun yi zargin cewa sabuwar dokar za ta cutar da yankin arewacin ƙasar.
Sai dai daga baya kwamitin haraji na ƙasar, ƙarƙashin jagorancin ministan kuɗin ƙasar na yanzu, ya yi wasu gyare-gyare da ya ce an cire wuraren da ake ganin za su haifar da matsalar.
Inda kuma ƴanmajalisar suka amince da ita duk kuwa da cewa wasu ƴan ƙasar ba su gamsu da dokar ba.
Sabuwar dokar, wadda ta fara aiki a shekarar da muke ciki ta 2026, har yanzu wasu ƴanƙasar na ci gaba da sukarta, saboda a cewarsu dokar ba ta fayyace irin abubuwan da ta ƙunsa ba.
Dokar taken ƙasa

Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ranar 29 ga watan Mayun 2024 ne shugaba Tinubu ya sanya hannu kan dokar da ta dawo da amfani da tsohon taken ƙasar mai suna "Nigeria: We Hail Thee".
Sauya taken ya zo wa ƴan ƙasar da dama da mamaki, kasancewar wasu ma ba su san an kai ƙudirin gaban majalisar ba.
Matakin ya sa an daina amfani da taken ƙasar na 'Arise, O Compatriots', wanda aka shafe fiye da shekara 45 ana amfani da shi a ƙasar.
Yayin bikin cikarsa shekara ɗaya a kan mulki da murnar cika shekara 25 da komawa mulkin dimokuraɗiyya, shugaban ya taya ƴan ƙasar murna kuma ya nemi 'yan majalisa "su ci gaba da aiki tare don gina ƙasar da na gaba za su yi alfahari da ita".
Ƴan ƙasar da dama sun nuna damuwa da adawa da sauya taken ƙasar, kasancewar yadda abin da ya zo musu da mamaki.
Har yanzu ƴan ƙasar da dama ba su iya sabon taken ƙasar ba, duk kuwa da amfani da shi a hukumance na fiye da shekara biyu.
Dokar zaɓe

Asalin hoton, INEC
Wata doka da majalisar Najeriya ta 10 ta amince da ita, ta kuma janyo muhawara tsakanin ƴanƙasar ita ce dokar zaɓen ƙasar ta 2026.
Tun a shekarar 2025 ake sa ran majalisar ta yi gyara a dokokin zaɓen ƙasar, amma kuma ta jinkirta hakan sai a farkon shekarar 2026.
Wasu abubuwa da suka ɗauki hankalin ƴanƙasar game da sabuwar dokar shi ne batun aika sakamakon zaɓe ta na'ura da kuma batun ɗora sakamakon zaɓen kai tsaye zuwa shafin intanet na INEC.
Batun ya haifar da zanga-zanga da suka daga masu rajin kare dimokraɗiyya da kuma ƴan hamayya waɗanda suka zargi jam'iyyar mai mulki da amincewa da yunƙurin shirya wa maguɗin zaɓe.
Sai dai Shugaba Tinubu ya kare matakin da cewa babu batun siyasa a sabbin gyare-gyaren da aka yi wa dokar zaɓen ƙasar.
A lokacin sanya hannu kan dokar, Tinubu ya ce "babu batun siyasa a cikin wannan gyare-gyare. Abu ne na tsari'', in ji shi.
''Ƙoƙari ne na cike giɓi da ƙarfafa tsari da kuma samar da tsaftatacciyar hanya ga masu tsarawa da kuma masu yin zaɓuka," in ji shi.
Dokar ƴansandan jihohi
Duk da cewa majalisar dattawan ƙasar ba ta amince da dokar ba zuwa yanzu, amma tuni majalisar wakilan ƙasar ta amince da ita, kuma bisa ga dukkan alamu majalisar dattawan za ta amince da dokar.
Sai dai masana harkokin tsaro na al'amuran yau da kullum na ci gaba da nuna fargaba game da dokar.
Suna masu zargin gwamnoni da amfani da ƴansandan jihohin ta hanyoyin da ba su dace ba, musamman domin muzguna wa ƴan hamayya.
Sai dai a nata ɓangare, gwamanti ta dage cewa matakin zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta a halin yanzu.











