Sojojin Najeriya sun yi ƙarin haske kan bidiyon ganawarsu da ƴanbindiga a daji

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Rundunar sojin Najeriya ta yi karin haske kan wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ya nuna ganawa tsakanin sojoji da wasu da ake zargin ƴan bindiga ne a wani daji.
Tun bayan ɓullar bidiyon ne dai ake ta tafka muhawara a kansa musamman a shafukan sada zumunta.
Inda wasu ke ganin abin da sojojin suka yi bai dace ba, yayin da wasu kuma ke cewa hakan wata dabara ce ta yaƙi.
Lamarin da ya sa sojojin suka yi ƙarin haske domin warware shakkun da mutane ke ciki.
Me bidiyon ya ƙunsa?
A cikin bdiyon mai tsawon mintuna da aka ɗauka cikin daji, an fara shi tun daga kan hanyar tafiya inda aka yi yi ganawar a tsakiyar daji.
Bayan an isa inda aka yi ganawar, an ga jami'an tsaro na sojoji da DSS, riƙe da makamansu, yayin da ake gefe guda kuma aka nuna ƴanbindigarsu ma riƙe da makamai.
An ga ɓangarorin biyu na gaisawa bayan da suka haɗu a cikin dajin, sannan aka ji suna maganganu game da makaman da ke hannayen ɓangarorin biyu.
An ji wata murya a cikin bidiyon na cewa ''mu zauna lafiya mana, wallahi shi ne ya fi komai ɗan'uwa''.
Haka kuma an ga wani mutum sanye da kayan sarautar gargajiya da ake kyautata zaton cewa basarake ne.
An ji jawabai tsakanin duka ɓangarorin yayin ganawar, inda a ciki aka jiyo muryar ɗaya daga cikin mutanen na cewa ''ku jarraba shi ku gani, daga lokacin da ku ka gwada shi za su fahimci cewa akwai sojoji masu alƙawari''.
Yadda bidiyon ya janyo ce-ce-ku-ce
Tun bayan ɓullar bidiyon ake ta aza ayar tambayar abin da ya kai jami'an tsaron cikin daji, ko kuma me suka tattaunawa da ƴanbindigar.
Inda wasu ke zargin sojojin da sanin inda ƴanbindigar suke amma suka kasa kawar da su.
Masu amfani da shafukan sada zumunta sun yin muhawara masu cin karo da juna game da bidiyon.
Inda wasu ke zargin sojojin da yin alaƙa da ƴanbindigar da suka addabi al'umomin ƙasar.
Me ya kai sojojin ganawa da ƴanbindigar?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Cikin wata sanarwa da rundunar OPERATION SAVANNAH SHIELD (JTF OPSS) ta fitar ta ce jami'an nata sun je dajin ne a wani yunƙuri na sulhu tsakanin ƴanbindigar da jami'an tsaro a jihar Kwara.
Sanarwar, wadda muƙaddashin mataimakin darakta yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal, Ibrahim Shittu ya sanya wa hannu ta ce ganawar sojojin da ƴanbindigar wani yunƙuri na kawo zaman lafiya a yankin.
''Hedikwatar JTF OPSS na son fayyace cewa abin da aka gani a bidiyon wani tsararren matakin tsaro ne da ya shafi sojoji da wasu ƴan bindiga da suka nuna aniyarsu ta miƙa makamansu tare da taimakawa wajen sakin mutanen da suka yi garkuwa da su'', a cewar sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa a yayin ganawar, sojojin sun samu nasarar karɓar bindigogi kirar AK-47 guda 12, sannan kuma ƴanbindigar suka saki wasu mutum 10 da suka yi garkuwa da su.
''Wannan ci gaba wata muhimmiyar nasara ce ta dabarun tsaro da ke haɗa amfani da ƙarfin soji da kuma hanyoyin sasanci, da nufin magance matsalolin tsaro tare da jawo masu ɗauke da makamai su miƙa wuya ba tare da faɗa ba'', in ji sanarwar.
Ba dai wannan ke karon farko da ake ganin jami'an tsaro na gaisawa da ƴanbidiga ba.
Ko a watannin baya ma an ga wani bidiyo da aka ɗauka a jihar Katsina da ya nuna wasu jami'an ƴansanda na ɗaga wa wasu gungun mutane ɗauke da muggan makama a kan babura, waɗanda suka yi jerin gwano suka biyo hanyar da ƴansandan suka kafa shingen binciken ababen hawa.
A cikin bidiyon an ga yadda ƴansandan da ke shingen na ɗaga wa mutanen hannu, lamarin da shi ma a alokacin ya haifar da ce-ce-ku-ce, kafin daga bisa rundunar ƴansanda ta ce mutanen ƴan sa kai ne ba ƴan bindiga ba.
Matsalar ƴanbindiga na ɗaya daga cikin matsalolin tsaron da Najeriya ke fuskanta.
Ƴanbindiga kan kai hare-hare kan garuruwa da ƙauyuka ko tare manyan hanyoyin ƙasar tare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.
Matsalar wadda a baya ta fi ƙamari a yankin arewa maso yammacin Najeriya, yanzu ta fara naso zuwa jihohin arewa da tsakiya, musamman jihar Kwara, Kogi kuma Neja.
Wani abu da masana harkokin tsaro ke alakanta da yalwar dazukan da suka tsara yankin arewa maso yamma zuwa arewa ta tsakiyar, har ma suka zarce zuwa ƙasashen Benin da Nijar.



























