Ƙasurguman Kachalloli biyu da suka mutu a faɗan ƴanbindiga a Zamfara

Bindigogi
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Rahotanni daga Jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya na cewa wani mummunan faɗa da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin ƴanbinga ya yi sanadin kashe wasu daga cikin manyan jagororinsu.

Mannir Fura Girke ɗan jarida ne mai bincike kan ayyukkan ƴan fashin daji a arewacin Najeriya ya shaidawa BBC cewa faɗan ya samo asali ne sakamakon ɗaukar fansa.

''A kwanakin baya ne wasu ƴanbindiga ƙarƙashin jagorancin Kachalla Dogo Baldu suka kai hari dabar Kachalla Alhaji Mu'azu a dajin Dausayi da ke jihar Katsina, inda suka kashe shi tare da yaransa bakwai'', in ji Fura Girke.

Mai binciken kan ayyukan ƴanbindiga ya ce Kachalla Alhaji Mu'azu ɗaya ne daga cikin manyan yaran ƙasurgumin ɗan fashin dajin nan Ado Aleiro, wanda ya yi kaurin suna a ayyukan fashin daji.

''To bayan kwanaki da wannan kisa ne sai ɓangaren Ado Aleiro suka ƙudiri aniyar ɗaukar fansa kan Dogo Baldu da yaransa'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa wannan ne ya sa ɓangaren Ado Aleiro da yaran sa suka kai hari gidan Dogo baldu da ke ƙauyen Mai Galma a jihar Zamfara, suka kuma kashe shi tare da yaransa uku.

Wane ne Kachalla Dogo Baldu?

'
Bayanan hoto, '

Mannir sani fura Girke ya ce Dogo Baldu ƙasurgumin ɗanbindiga ne da ya yi ƙaurin suna a ayyukan fashin daji a yankin kewayen Gusau.

Ya ce Dogo Baldu ɗan'uwa ne ga wani ƙasurgumin ɗan fashin daji mai suna Kachalla Abdulkarim ne da shi ma aka kashe a kwanakin baya.

''Ya shahara wajen kai munanan hare-hare a wannan yanki tare da garkuwa da mutane'', in ji shi.

Masanin taron ya ce Kachalla Dogo Baldu ne da yaransa suka fi tare hanyar Gusau zuwa Funtua.

''Sannan su ke kai hare-hare zuwa yankin gabashin Gusau da har zuwa wani yanki na Danmusa a jihar Katsina'', in ji shi.

Wane ne Kachalla Alhaji Mu'azu?

Kachalla Alhaji Mu'azu kamar yadda Mannir Fura Girke ya bayyana ɗan'uwa ne da Ado Aleiro.

Ya kasance yana da daba a cikin Dajin Dausayi da ke yankin Danmusa a jihar Katsina mai maƙabtaka.

''Ya shahara wajen kai hare-hare a yankunan ƙananan hukumomin Bakori da Faskari da kuma Ƙanƙara, duka a jihar ta Katsina'', a cewar Mannir Girke.

Wane tasiri kashe su zai yi?

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mannir Sani Fura Girke ya ce kashe waɗannan kachalloli da yaransu zai yi gagarumin tasiri a yaƙi da yanbindiga da ake yi a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

''Wannan ba ƙaramar nasara ba ce saboda duk lokacin da aka kashe kachallah guda ɗaya, to ka kashe abubuwa na harkar ƴan fashin daji ne da yawa'' in ji shi.

Fura Gike ya kuma ce kisan Kachalla Baldu zai yi matu kar tasiri wajen rage ayyukan ƴanfashin daji musamman a yankunan da yake yawan kai wa hare-hare shi da yaransa.

''Duk wanda jami'an tsaro suke nema su kashe yau kuma sai ya zama su ne suke faɗa har da kashe juna, to kaga abu ya zo cikin sauƙi kenan''

''Shi kachallah shi ke mu'amala da infoma da masu kawo masa makamai da miyagun ƙwayoyi, don haka idan an kashe wannan zai kawo ƙarshen wannan daba''

Ya ce su dama yanbindiga ba su da wani tsari na shugabanci, duk wanda ya mallaki makamai to shi ma sai ya zama jagora, ya samu yara ya yi ta aiki.

''Babu wani da za ka ɗaga ka ce shi ne shugaban ƴanbindiga baki ɗaya, zaman ƴan marina ake yi, kowa da inda ya sanya gaba, kowa yana yin abin da zai iya ne domin ta shi ta fi she shi'' in ji shi.