Manchester United na harin Nico Paz, Besiktas na son Amad Diallo

Asalin hoton, Getty Images
Zuwan Mauricio Pochettino a matsayin mai horar da ƴan wasan Manchester United zai iya taimaka wa Old trafford ɗauko Nico Paz, duk da dai Real Madrid na son biyan euro miliyan 80 (fam miliyan 67.6) don ganin sun sake ɗauko dan wasan daga Como a 2027.(Sun)
Besiktas na son ɗauko dan wasan Manchester United Amad Diallo kan fam miliyan 37.5 a watan Janairu. (NTV Spor - in Turkish)
Liverpool da Manchester United na zawarcin ɗan wasan Barcelona Alejandro Balde, sai dai Barcelonan na ba ta son siyar da ɗan wasan. (Teamtalk)
Ɗan wasan Benfica Vangelis Pavlidis na cikin jerin ƴan wasan da Pochettino ke son kawowa Manchester United, sai dai ɗan wasan na son komawa Tottenham da Barcelona. (Caught Offside)
Ba lallai ɗan wasan Juventus Weston McKennie, ya koma buga gasar firrimiya ba, duk da cewar an yi ta raɗe-raɗin cewar ƴan wasan zai Amurka za su iya biyo tsohon kociyansu Pochettino zuwa Manchester United. (Sky Sports)
Arsenal na ci gaba da sa ido kan ɗan wasan RB Leipzig Antonio Nusa, da na Brentford Kevin Schade, yayin da suke duba irin matakan da za su ɗauka wajen ƙara inganta ƙungiyar. (Sky Sports)
Barcelona hta sake sabunta shrinta na ɗauko ɗn wasan Brighton & Hove Albion Luka Vuskovic. (Teamtalk)
Middlesbrough na da ƙarfin guiwar cewar ɗan wasan ingila na ajin shekaru 21Will Lankshear, zai 21, yi watsi da ƙungiyoyin da ke buga firmiya ya yi zamansa a ƙungiyar. (Sun)
Tsohon dan wasan Arsenal Rob Holding, da kwantaraginsa ta ƙare na jan hankulan Sheffield United, LAFC da Houston Dynamos. (Sky Sports)
Arsenal na sa ido kan Club Brugge winger Carlos Forbs, da aka yi masa kiyasin farashin fam miliyan 20. 22. (Fichajes - in Spanish)


























