Abubuwan da suka kamata ku sani kan fara kamfe na gwamnoni a Najeriya

..

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Larabar 9 ga Satumba 2026, ne Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta amince a fara yakin neman zaɓe a hukumance ga 'yan takarar gwamnoni da na majalisun jihohi gabanin zaɓukan 2027. Wannan na zuwa ne bisa jadawalin zaɓe da hukumar ta fitar.

Zaɓukan gwamnoni za su gudana ne a jihohi 28, yayin da jihohi takwas ba sa cikin wannan zagaye saboda suna da tsarin zaɓe na daban.

NEC ta ce kamfen ya fara ne kwanaki 150 kafin ranar zaɓe sannan dole ne ya ƙare awanni 24 kafin ranar zaɓe. INEC ta ƙara da gargaɗin cewa duk wanda ya karya dokokin kamfen na iya fuskantar hukuncin da doka ta tanada.

Abin da hakan ke nufi

Tun daga ranar Laraba, jam'iyyu da 'yan takara za su iya:

  • Gudanar da gangamin yakin neman zaɓe.
  • Tallata manufofinsu a kafafen yaɗa labarai.
  • Shirya tarukan ganawa da masu zaɓe.
  • Gudanar da wayar da kan jama'a da tattara goyon baya a matakin mazaɓu da ƙananan hukumomi.

Abubuwa 6 da INEC ta haramta game da yaƙin neman zaɓe

Yayin da aka ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen gwamnoni da ƴan majalisar jihohi a hukumance a Najeriya, ƙofar ta buɗe ga jam'iyyu da ƴantakara domin yaɗa manufofinsu. To sai dai kuma ta ware wasu hanyoyi shida da ta haramta wa ƴan takarar yin kamfe.

  • Amfani da harshe mai kaushi
  • Kamfe a Wuraren ibada
  • Amfani da ƴanbori
  • Amfani da ƙarfi
  • Yi wa mutane barazana
  • Saka lokaci ɗaya don zuwa wuri ɗaya

Nawa ne kuɗin da ɗantakar gwamna zai iya kashewa?

Bisa tanadin sabuwar dokar zaɓe ta 2026, sashe na 92 ya ƙara adadin kuɗin kamfe da ƴan takara za su iya kashewa, inda aka bayyana cewa an yi hakan ne saboda hauhawar farashin kaya da tsadar gudanar da kamfe idan aka kwatanta da shekarun baya.

Dokar ta tanadi cewa ɗan takarar gwamna bai kamata ya kashe fiye da naira biliyan uku ba a dukkannin harkokin kamfe dinsa baki ɗaya. Dokar ta kuma tanadi naira miliyan 100 ga ɗantakarar majalisar jiha.

Sai dai dokar ba ta ce dole ne ɗan takara ya kashe wannan adadi ba idan ba shi da su, illa dai ta sanya iyakar da ba zai wuce ba.

Dokar ta ce da zarar an kammala zaɓe ƴan takara za su bayar da bayanin ƙididdigar abin da suka kashe.

Dokar ta amince ɗan takara ya karɓi gudummawar kuɗi daga magoya bayansa, mambobin jam'iyyarsa da kuma wasu ƙungiyoyi ko mutane da suka yanke shawarar tallafa masa bisa ƙa'ida.

Sashe na 89 sakin layi na ɗaya ya tanadi cewa duk wanda ya saɓa wa waɗannan ƙa'idoji da sani ko da gangan, kotu na iya hukunta shi da biyan tara da ta kai kashi ɗaya cikin ɗari na kuɗin da ya kashe.

Yaushe ne za a yi zaɓen?

Zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi a Najeriya zai gudana ne a ranar 6 ga Fabrairu 2027, kamar yadda jadawalin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ya nuna:

  • Fara kamfen: 9 ga Satumba 2026
  • Ƙarshen kamfen: 5 ga Fabrairu 2027 (awanni 24 kafin zaɓe)
  • Ranar zaɓe: 6 ga Fabrairu 2027

Jihohin da za a yi zaɓen gwamna a 2027

Jihohin da za a yi zaɓen gwamna tare da babban zaɓen 2027 su ne jihohi 28 da ba sa cikin tsarin zaɓe na daban.

  • Abia
  • Adamawa
  • Akwa Ibom
  • Bauchi
  • Benue
  • Borno
  • Cross River
  • Delta
  • Ebonyi
  • Enugu
  • Gombe
  • Jigawa
  • Kaduna
  • Kano
  • Katsina
  • Kebbi
  • Kwara
  • Lagos
  • Nasarawa
  • Niger
  • Ogun
  • Oyo
  • Plateau
  • Rivers
  • Sokoto
  • Taraba
  • Yobe
  • Zamfara

Jihohin da ba za a yi zaɓen gwamna ba

Jihohin da ba za a yi zaɓen gwamna a 2027 ba saboda suna da tsarin zaɓe na daban su ne:

  • Anambra
  • Bayelsa
  • Edo
  • Ekiti
  • Imo
  • Kogi
  • Ondo
  • Osun

Wannan yana nufin cewa zaɓen gwamnoni a waɗannan jihohi takwas ba zai gudana tare da babban zaɓen 2027 ba, domin wa'adin gwamnoninsu ya bambanta da na sauran jihohin ƙasar.