Mene ne takamaiman abin da Amurka ke buƙata daga Iran?

Asalin hoton, Reuters
Amurka na son Iran ta fito fili ta sanar cewa za ta buɗe Mashigar Hormuz kuma mashigar za ta ci gaba da kasancewa a buɗe, sannan kuma ta ɗauki alƙawarin daina kai hari kan jiragen dakon man fetur.
Wasu kafafen yaɗa labarai na Amurka, sun ambato wata majiya daga jami'an Amurka na cewa, a asirce, Iran ta amince cewa ta yi kuskure da ta kai hari kan jiragen ruwa da ke bi ta mashigar.
Sai dai wasu na cewa Iran ta alaƙanta harin da wata ƙungiya ƴan tawaye waɗanda ba ta da iko a kansu.
Trump ya ce ɓangarorin biyu sun amince su ci gaba da tattaunawa, duk da cewa Amurkar ta ce yaƙin da ake fafatawa a wannan mako a Mashigar Hormuz na faruwa ne sanadiyyar karya sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta.
'Dole Iran ta amsa laifinta ko ta ɗanɗana kuɗarta'
A watan Yuni ne Amurka da Iran suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta. A ƙarƙashin yarjejeniyar, Iran ta amince za ta tabbatar cewa jiragen ƴan kasuwa na safara cikin aminci ta Mashigar Hormuz.
Wasu manyan jami'an gwamnatin Amurka sun shaida wa tashar talabijin ta CBS news, abokiyar hulɗar BBC a Amurka, cewa Iran ta ce ''wata gurɓatattar ƙungiya" na son ta yi zagon ƙasa ga yarjejeniyar ta hanyar kai hari kan jiragen ruwan dakon mai.
"Jami'an Iran din sun dawo wurin tattaunawa inda suka ce, 'Mun yi kuskure. Mu ci gaba da tattaunawa," kamar yadda wani jami'i ya shaida wa gidan talabijin na CBS.
A wani taron manema labarai a ranar Juma'a, jami'an Amurka sun ce sun aika wa Iran da saƙo ta hannun masu shiga tsakani a yankin, inda suke son Iran ta fitar da sanarwa kan cewa Mashigar Hormuz a buɗe take kuma za ta ci gaba da kasancewa a buɗe, kuma ta bayyana cewa ta daina kai wa jiragen ruwan da ke ratsawa ta mashigar hari.
End of Unaweza kusoma
Kafafen yaɗa labarai da dama sun ruwaito wannan mataki.
"Wajibi ne Iran ta bayar da sanarwa, ko kuma ta fuskanci tsattsauran mataki," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Wani rahoton kafara yaɗa labarai ta CBS ya ce, fadar shugaban Amurka ta White House na kuma buƙatar Iran ta sanar cewa ta aikata laifi bayan da ta kai wa jiragen ruwa na ƴan kasuwa hari.

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mataimakin shugaban Amurka JD Vance da Sakataren harkokin waje na Amurka Marco Rubio da kuma wasu manyan jami'an gwamnati da ke lura da tattaunawa da ƙasashen Gabas ta Tsakiya, wato Steve Witkoff da surukin shugaba Trump, Jared Kushner ne za su jagoranci tattaunawar da za a yi a ƙasar Oman.
A ɓangare ɗaya kuma wata tawaga daga Qatar ta isa Iran a ranar Juma'a domin tattaunawa kan yadda za yayyafa wa wutar rikicin ruwa, da kuma lalubo tsarin da zai bai wa jiragen ruwa damar sufuri ta Mashigar Hormuz cikin aminci.
"Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta buƙaci mu ci gaba da tattaunawa," kamar yadda Trump ya bayyana a wani bayani da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Juma'a.
"Mun amince da buƙatarsu, amma Amurka ta bayyana musu ƙarara cewa yarjejeniyar tsagaita wutar da aka ƙulla ta wargaje," in ji shi.
Yaƙin da ya sake ɓarkewa a makon da ya gabata shi ne fito na fiton soji mafi ƙazancewa tsakanin Amurka da Iran tun bayan sanya hannu kan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ƙasashen biyu a watan Yuni.
Jiragen ruwa uku da ke kan hanyarsu zuwa ƙasar Oman ta wata hanyar ruwa da Amurka ta shata ne suka fuskanci hari.
Iran ta dage kan cewa hanya ɗaya tilo da za a iya bi cikin aminci ita ce wadda ta shata da ta bi ta yankin ruwan teku da take iko da shi.
Mene ne matsayin Mashigar Hormuz a yarjejeniyar?
An ɗan samu ci gaba a tattaunawar da aka yi lokacin da Amurka da Iran suka sanya hannu kan wata yarjejeniya mai ƙunshe da sharuɗɗa 14 a watan da ya gabata, wadda ake samar da ita domin tsagaita wuta da kuma kawo ƙarshen yaƙin.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, an tsara cewa Iran da Oman za su tattauna da sauran ƙasashen yankin Gulf domin tantance maomar Mashigar Hormuz da kuma tsara yadda za a riƙa sufurin jiragen ruwa ta cikinta.
A tsawon yaƙin Iran ce ta ke ta ƙoƙarin tabbatar da ikonta kan Mashigar.
Saboda haka ne ma Iran ɗin ta ce za ta kafa wata hukuma wadda za ta riƙa kula da zirga-zirga ta mashigar, hukumar ce za ta riƙa bai wa jiragen ruwan da za su ratsa izini.
Kamfanin dillancin labarai na Fars da ke Iran ya ruwaito cewa a ƙarƙashin sabuwar yarjejeniyar da Amurka, Iran da Oman ne za su riƙa kula da mashigar.
Matakin zai hada da karɓar haraji daga jiragen ruwan da suke ratsawa ta mashigar, wadda ke da matuƙar muhimmanci.











