'Muna ta roƙon gwamnati ta ceto yaranmu amma shiru' - Iyayen ɗaliban Borno

Asalin hoton, Ifeanyi Immanuel Bakwenye / AFP via Getty Images
Iyayen ɗaliban da aka sace daga garin Mussa da ke jihar Borno a ranar 15 ga watan Mayu sun buƙaci hukumomin Najeriya su ƙara ƙaimi wajen ganin an ceto ƴaƴansu.
Sun yi wannan kira ne bayan sakin ɗalibai da malaman makarantar da aka sace a jihar Oyo kwana guda bayan da aka yi garkuwa da ɗaliban na Borno.
Ɗaya daga cikin iyayen, Bukar Buba, ya shaida wa BBC cewa suna cikin "baƙin ciki da takaici", ganin cewa har yanzu ƴaƴansu ke hannun masu garkuwa da mutane duk da cewa an saki waɗanda aka sace a Oyo.
Ya ce iyayen ba su ji daɗin yadda har yanzu ƴaƴansu na ci gaba da zama a hannun ƴan bindiga ba, inda ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta ɗaukar matakan da za su kai ga kuɓutar da su.
"Muna cikin baƙin ciki tun bayan da aka sace mana yaranmu. Ba mu ma san halin da suke ciki a cikin daji ba, musamman a wannan lokacin na damina. Mun sha kuka tare da roƙon gwamnati ta taimaka ta ceto yaranmu, amma har yanzu ba mu ji wani labarin sakin su ba," in ji Buba.

Asalin hoton, NIGERIAN ARMY/X
A ranar 10 ga Yulin 2026, gwamnati ta sanar da ceto ɗalibai da malaman makarantar da aka yi garkuwa da su a jihar Oyo, kwanaki 56 bayan sace su daga makarantarsu da ke ƙaramar hukumar Orire a yankin Ogbomoso.
Shugaba Bola Tinubu ya ce an ceto ɗaliban da malamansu ba tare da an rasa rai ko raunata kowa ba. Ya kuma tabbatar da kama mutane takwas da ake zargin ƴan ƙungiyar Ansaru ne, tare da kashe wasu da ake zargin suna da hannu a harin.
Shugaban ya danganta nasarar ceto waɗanda aka sace da ƙoƙarin jami'an tsaro, inda ya yaba musu kan yadda suka gudanar da aikin.
Yadda aka sace ɗaliban Borno
A ranar 15 ga watan Mayu ne, wasu mahara ɗauke da makamai suka yi garkuwa da fiye da ɗalibai 50 daga makarantu uku da ke garin Mussa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
An kai harin ne a makarantun Government Day Secondary School, da Mussa Central Primary School, da kuma State Universal Basic Education Board (SUBEB) Secondary School.
Daga cikin yaran da aka sace akwai da dama wadanda ba su wuce shekaru biyu zuwa biyar ba.
Shaidu sun ce maharan sun yi amfani da yaran a matsayin garkuwa yayin da su ke tserewa a kan babura, lamarin da ya hana jami'an tsaro buɗe musu wuta.
Har zuwa yanzu, babu wata ƙungiya da ta fito ta ɗauki alhakin kai harin.
'Abin da ya sa har yanzu ba'a ceto ɗaliban Borno ba'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bukar Buba, wanda aka sace masa ƴarsa mai shekara shida, ya shaida wa BBC cewa kimanin makonni biyu da suka gabata, kwamishinan ilimin jihar Borno ya gana da iyayen yaran, inda ya buƙa ce su da su ƙara haƙuri.
Ya ce, kwamishinan ya sanar da su cewa gwamnati na ƙoƙarin tattaunawa da masu garkuwa da yaran domin a san yadda za a kuɓutar da su.
"Kwamishinan ilimi ya gana da wasu daga cikin iyayen, ya kuma gaya mana cewa gwamnati na shirin fara tattaunawa da masu garkuwa da yaran," in ji Buba.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta haramta biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane. Wata doka da aka kafa a shekarar 2022 ta ayyana biyan kuɗin fansa a matsayin laifi, kuma gwamnati ta sha musanta rahotannin da ke cewa tana biyan kuɗi domin a saki waɗanda aka sace.
A watan Nuwamban 2025, bayan da ƴan ta'adda suka yi garkuwa da fiye da ɗalibai da ma'aikata 200 daga wata makarantar kwana ta Katolika da ke Papiri a jihar Neja, an yi ta yaɗa rahotannin cewa gwamnati ta biya "kuɗin fansa" mai yawa ga Boko Haram domin a sake su.
Sai dai Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya musanta wannan zargi, inda ya ce ƙarya ce tsagwaronta, kuma hakan zubar da mutunci da ƙwarewar jami'an tsaron Najeriya ne.
Muna iya bakin ƙoƙarinmu - Ƴansanda
Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta ce jami'an tsaro na ci gaba da haɗa kai da sauran jami'ai domin ganin an ceto ɗaliban da aka sace.
Mai magana da yawun rundunar, Nahum Daso, ya tabbatar wa BBC cewa har yanzu yaran na hannun masu garkuwa da su, kuma suna ci gaba da bincike da ɗaukar matakan tsaro.
A ranar da aka kai harin, shugaban makarantar Mussa Central Primary School, Abdu Dunama, ya ce ya fara jin karar harbe-harbe ne daga nesa kafin maharan ɗauke da makamai su kutsa cikin makarantar tare da kwashe yaran.
Ya ce maharan sun tafi da yara 34, mafi yawansu ɗaliban ajin yara ƙanana masu shekaru biyar zuwa ƙasa.
Mazauna yankin sun ce maharan sun isa makarantun ne a kan babura jim kaɗan bayan sojojin da ke sintiri sun bar garin.
"Jim kaɗan bayan sojojin sun tafi, bai wuce minti 30 ba sai maharan suka iso," in ji Buba.
Shaidun sun ce maharan sun riƙa harbe-harbe ta ko'ina, abin da ya sa jama'a suka tsere domin neman mafaka. Wasu daga cikin iyayen yaran suna tsaye kan wani tudu suna kallon yadda aka ɗora ƴaƴansu a kan babura aka tafi da su, ba tare da sun iya yin komai ba.
Ko da yake babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin harin, wasu rahotanni sun nuna cewa salon harin na kama da irin na ƙungiyar Boko Haram, wadda ke da alaƙa da ƙungiyar ISWAP domin faɗaɗa ikonta a yankin.
Al'ummar jihar Borno dai sun shafe shekaru suna fama da hare-haren ƴan ta'adda da sace-sacen mutane, lamarin da ya jefa yankin cikin matsanancin rashin tsaro.
Sai dai rundunar sojin Najeriya ta ce ta daƙile wani hari da mayaƙan ISWAP suka yi ƙoƙarin kai wa yankin Cross Kauwa da ke jihar ta Borno a ƙarshen mako, inda ta kashe wasu daga cikinsu tare da tilasta wa sauran tserewa.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar ranar Lahadi 12 ga watan Yuli, ya ce lamarin ya faru ne a daren Asabar lokacin da mayaƙan suka yi yunƙurin kutsawa cikin sansanin sojoji.
Ya ce binciken ya nuna cewa maharan sun kuma yi ƙoƙarin sace kayan aikin jinya da magungunan cutar kwalara da ke yankin.
Jihar Borno da wasu sassan arewacin Najeriya na fama da ɓullar cutar kwalara a lokacin damina, saboda yadda aka raba mutane da muhallansu lamarin da ya lalata hanyoyin samar da tsaftataccen ruwa da muhalli.
Kyaftin Goni ya ce sojoji sun gano motsin maharan tun kafin su kai hari, inda suka "mayar da martani wanda hakan ya tilasta musu janyewa."
Rundunar ta ce ta gano bayan an kashe manyan kwamandojin ISWAP huɗu tare da mayaƙa baƙi uku da suka jagoranci harin.
Rundunar ta ce ta gano ɗaya daga cikinsu mai suna Abu Ishaq, wani Bafalasɗine da ta bayyana a matsayin babban mai horas da mayaƙan ISWAP.
Haka kuma ta ce akwai Abu Thaiba, ɗan asalin ƙasar Maroko, wanda ake zargin likita ne da ke aiki tare da ƙungiyar, inda ta ce har yanzu ana binciken wani mutum na uku da ake zargin ɗan ƙasar waje ne.







