Gasar kofin duniya 2026: Me kuke son sani kan wasan Faransa da Sifaniya?, Faransa da Sifaniya

Asalin hoton, Getty Images
Wasa ɗaya ya rage wa Faransa ta kai wasan ƙarshe a Gasar Kofin Duniya, kuma karo na uku a jere a tarihi tun daga 2018 a Rasha da 2022 a Qatar.
Sai dai tana fuskantar ƙalubale game da burin nata, domin za ta kara da Sifaniya a zagayen daf da ƙarshe ranar Talata a birnin Boston.
Tawagar da Didier Deschamps ke jan ragama ta yi fice a matakin wasannin rukuni a gasar ta bana, inda ta yi nasara a wasa uku a jere, wajen doke Senegal da Iraƙi da kuma Norway.
Daga nan kuma cikin sauƙi ta lallasa Sweden a zagayen ƴan 32 da Paraguay a zagayen ƴan 16, sannan Morocco a fafatawar kwata fainal.
A gefe guda kuma, Sifaniya ta fara gasar bana da canjaras karawar farko a cikin rukuni da Cape Verde, wasan da ya bayar da mamaki matuka, saboda kasa samun maki uku da Sifaniya ta yi a kan karamar ƙasa da a karon farko da ta fara halartar gasar a tarihi.
Daga nan ta kara ƙwazo ta kuma kai matakin zagaye na biyu, sakamakon doke Saudiyya da Uruguay, sannan ta yi waje da Austria a zagayen ƴan 32.
A zagayen ƴan 16, Sifaniya ta fitar da Portugal da kuma cin Belgium a kwata fainal, yayin da Merino ke shiga karawar a matsayin canji, sannan ya ci ƙwallon da ke kai Sifaniya zagayen gaba, kamar yadda ya yi wannan bajintar a wasan Portugal da na Belgium.

Asalin hoton, Getty Images
Mbappe na sa ran lashe kofi da ƙyautar takalmin zinare
Bayan da tawagar Faransa ta kai wasan daf da ƙarshe karo na takwas kenan a tarihi a gasar cin kofin duniya, tana da damar zama ta biyu daga Turai da za ta buga wasan karshe karo na uku a jere, bayan bajintar Jamus ta Yamma da ta yi hakan a shekarar 1982 da 1986 da kuma 1990.
Faransa na kan ganiya, saboda fitattun ƴan wasan da take da su, musamman Kylian Mbappe, saboda rawar da yake takawa.
Ya zura ƙwallo a wasan da Faransa ta caskara Croatia da ci 4-2 a gasar Rasha ta 2018, sannan ya ci uku rigis a wasan da suka tashi 3-3 da Argentina a Qatar 2022 da kuma cin ƙwallo a bugun fenaritin da Faransa ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Argentina, wadda ta lashe kofin.
A gasar bana tuni ya zura takwas a raga.
Hakan na nufin ɗan wasan mai shekara 27 ya ci ƙwallaye 20 a wasanni 20 da ya buga a Gasar Kofin Duniya.
Sai dai ba Mbappe ne kaɗai mai haɗari idan tawaga ta fuskanci Faransa ba, domin tana da wasu ƙwararrun ƴan wasan kamar Ousmane Dembele da Michael Olise da Desire Doue da kuma Bradley Barcola.
A ɓangaren tsaron baya ma, Faransa tana da ƙarfi sosai.
Dayot Upamecano da William Saliba suna taka rawar gani, domin ƙwallo biyu ne ya shiga ragar Faransa kawo yanzu.
kuma ba a zura mata ko guda ɗaya ba a matakin wasannin fitar-da-gwani.
A tsakiyar fili kuwa, Manu Kone da Adrien Rabiot suna suke buga wasan da tawagar ke samun kwanciyar hankali ba tare da shiga ruɗani ba.

Asalin hoton, Getty Images
Sau uku Sifaniya ta kai zagayen daf da ƙarshe a gasar kofin duniya
Wannan shi ne karo na uku da Sifaniya ta kai matakin daf da karshe a Gasar Cin Kofin Duniya.
Tawagar ta La Roja ta fara yin wannan bajintar a shekarar 1950, sannan ta lashe kofin duniya a 2010 a gasar da Afirka ta Kudu ta gudanar.
Tun daga wannan lokacin Sifaniya ta gaza kai wa matakan ƙarshe a gasar, bayan da aka fitar da ita tun a matakin rukuni a 2014, sannan kuma ta tsaya a zagayen ƴan 16 a gasa biyu baya, wato a 2018 a Rasha da kuma 2022 a Qatar.
Sai dai tawagar ƙarƙashin koci, Luis de la Fuente za ta shiga wannan wasa cike da kwarin gwiwa, bayan da ta yi nasara a haɗuwarta biyu a baya a kan Faransa.
Duka wasannin sun kasance a matakin zagayen kusa da na ƙarshe, inda Sifaniya ta yi nasara da ci 2-1 a Gasar Cin Kofin Nahiyar Turai ta UEFA EURO 2024, sannan ta sake doke Faransa da ci 5-4 a UEFA Nations League a kakar 2024/25.
Tawagar Sifaniya tana alfari da rawar da Rodri da Pedri da Dani Olmo ke takawa, wajen mamaye wasan da suke bugawa ta hanyar riƙe ƙwallo da sarrafa fafatawar.
A ɓangaren tsaron baya kuwa, ƙwallo ɗaya ne kacal ya shiga ragar golan Sifaniya, Unai Simon kawo yanzu.
Haka kuma haɗin kai tsakanin Aymeric Laporte da Pau Cubarsi ya ƙara ƙarfin wasannin Sifaniya.
Masu tsaron baya daga gefen hagu da dama, Marc Cucurella da Pedro Porro, suna taka muhimmiyar rawa wajen kai hare-hare.
Hakan yana ƙara ƙarfi ga ƴan wasan gaba da ya haɗa da Lamine Yamal da Nico Williams da Mikel Oyarzabal da sauransu.
Me suka ce kafin wasan nan na hamayya?
Kylian Mbappe, ɗan wasan tawagar Faransa.
"Hanya ɗaya ce kawai da za ta sa mu samu nutsuwa, ita ce yin nasara kawai a kansu. Kuma ba za mu sassauta ba. Mun kai wasan kusa da ƙarshe kuma muna matuƙar farin ciki, amma har yanzu akwai sauran aiki mai yawa a gabanmu. Mun san abin da ke tafe zai yi wahala fiye da abin da muka riga muka fuskanta a baya, amma muna shirye mu tunkari kowanne irin ƙalubale."
Luis de la Fuente, kocin Spain.
"Ya dace mu yi tunanin cewa za mu iya doke Faransa; za mu yi aiki tuƙuru domin cimma hakan. Mu ne kaɗai tawagar da ta samu nasarar doke su sau biyu. Babbar kasa ce za ta kara da wata babbar tawagar."
Ƴan wasan da ake sa ran za su buga karawar
Ƴan wasan tawagar Faransa da ake sa ran fara karawar da su:
Maignan; Kounde, Upamecano, Saliba, Digne; Kone, Rabiot, Olise, Dembele, Doue; Mbappe
Ƴan ƙwallon Sifaniya da ake sa za a fara fafatawar da su:
Unai Simon; Porro, Cubarsi, Laporte, Cucurella; Rodri, Pedri; Lamine Yamal, Dani Olmo, Baena; Oyarzabal
Wasan da suka buga a baya tsakanin Faransa da Sifaniya
Duk da cewa Faransa da Sifaniya sun buga Gasar Cin Kofin Duniya ta FIFA sau 17 kowacce, abin mamaki ne cewa wannan ne karo na biyu da za su kara da juna a wannan babbar gasa ta duniya.
Haɗuwarsu ta farko a baya ta kasance ne a zagayen ƴan 16 a gasar da aka gudanar a Jamus a shekarar 2006.
A wannan wasan, David Villa ne ya fara ci wa Sifaniya ƙwallo a bugun fenariti.
Sai dai daga baya Faransa ta dawo da ƙarfi, inda Franck Ribery da Patrick Vieira da kuma Zinedine Zidane suka ci ƙwallaye, waɗanda suka tabbatar wa Faransa nasara da ci 3-1.
Yanzu, bayan shekaru 20 da wannan haɗuwa ta tarihi, Faransa da Sifaniya za su sake fafatawa a matakin wasan kusa da ƙarshe, domin neman gurbin zuwa wasan ƙarshe na Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026.

Asalin hoton, Getty Images
Filin wasa na Dallas da za a buga karawar
Katafaren filin wasa na Dallas na ɗaya daga wajen da yake ɗaukar hankali a duniya ta fuskar gine-gine, kuma zai karɓi bakuncin wasansa na tara kuma na ƙarshe a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026.
Tun bayan buɗe shi a shekarar 2009, filin ya kasance gida ga ƙungiyar Dallas Cowboys, wadda ta lashe kofin Super Bowl sau biyar.
Haka kuma ya karɓi bakuncin wasannin Concacaf Gold Cup da kuma wasannin tawagar ƙasar Mexico.
Wannan fitaccen filin wasa ya karɓi bakuncin wasa biyar a matakin rukuni a gasar ta bana, inda daga cikin fitattun fafatawar da aka buga a cikinsa akwai:
Canjaras da ya kayatar da aka tashi 2-2 tsakanin Netherlands da Japan.
Nasarar da Ingila ta samu kan Croatia da ci 4-2.
Nasarori biyu na Argentina waɗanda hazikin ɗan wasanta Lionel Messi ya taka muhimmiyar rawa a cikinsu.
Bayan matakin rukuni, filin ya kuma karɓi bakuncin wasan zagayen ƴan 32 tsakanin:
Côte d'Ivoire da Norway.
Australia da Masar.
Haka kuma filin ne ya shaida nasarar da Sifaniya ta yi a kan Portugal a zagayen ƴan 16, inda aka samu ƙwallar da ta yanke hukunci a lokacin da aka ƙarin lokaci bayan cikar mintuna 90 na wasa.
