Abin da muka sani kan yawan masallatai da masana'antu a Kano

..

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Wannan tambayar ce yanzu haka a bakin mutane da dama ƴan asalin jihar Kano da ma masu lura da al'amura a jihar.

Batun dai ya taso bayan wasu alƙaluma da wani mai suna Aliyu Nuhu ya wallafa a shafinsa na Facebook sun rinƙa karakaina a shafukan sada zumunta da ke nuna cewa akwai masallatai kimanin rabin miliyan ɗaya fiye da yawan masana'antun da ke jihar da ake yi wa take da "cibiyar kasuwancin" Najeriya.

Idan aka yi la'akari da yawan jama'ar Kano, wanda yanzu haka ya kai miliyan 18 bisa alƙaluman hukumar ƙididdiga ta jihar, KSBS, ikirarin masallatai kusan 500,000 na nuna duk masallaci guda ɗaya zai zama na amfanin mutum 40-45, abin da ya sa adadin ya zama abin tambaya matuƙa.

To sai dai kuma masu wannan iƙrari na cewa suna da nasu hujjojin da ke nuna yawaitar masallatai a Kano fiye da masana'antu.

Iƙirarin masallatai sun fi masana'antu yawa a Kano

Wani shafin Facebook na wani mai suna Aliyu Nuhu ya wallafa rubutun da ya ce wani mai suna Garba Adamu ne ya rubuta alƙaluman da ake taƙaddama a kansu kamar haka:

  • Yawan al'ummar Kano: Miliyan 18
  • Yawan masana'antu: 58
  • Yawan masallatai: 435,389
  • Yawan majami'a: 674
  • Yawan yara marasa iyaye da ke gararamba: Miliyan 3.67
  • Yawan zawarawa: 857,443
  • Yawan marasa aikin yi: Miliyan 3.8

Sai dai kuma wani abu da ya rage ƙimar wannan bincike shi ne rashin bayyana majiya ko kuma hukumar da ta gudanar da binciken da ma hanyoyin gudanar da shi wannan bincike.

Sannan kuma hukumomi na saka shakku dangane da haƙiƙanin mutumin ko kuma ƙungiyar da ta samar da alƙaluman.

'Masana'antu 3,632 ba 58'

A martaninta, hukumar ƙididdiga ta jihar Kano, KSBS ta ƙaryata alƙaluman da shafin na Aliyu Nuhu da aka alaƙanta da wani mai suna Garba Adamu ya wallafa, inda ta nemi da ya janye alƙaluman "cikin sa'o'i 48 ko kuma a ɗauki matakin shari'a."

Hukumar ta bakin shugabanta, Dakta Surajo Sulaiman ta ce ita kaɗai ce kawai mai alhakin fitar da alƙaluma da ƙididdiga da suka shafi jihar Kano.

Ta kuma ƙalaubalanci shafin da ya bayyana hanyoyin da ya bi wajen tattara alƙaluman kamar yadda ya yi iƙirari.

Dakta Surajo ya ce "alƙaluman da muke da su a hannunmu waɗanda muka kwashe dogon lokaci muna haɗawa su ne akwai masallatan Juma'a guda 2,333 a faɗin jihar Kano."

Dangane kuma da masana'antu, shugaban hukumar ƙididdigar ta jihar Kano ya ce "alƙaluman da hukumar da ke kula da harka zuba jari ta Kano, KANINVEST da KSBS muka tattara sun nuna akwai masana'antu guda 3,632 saɓanin 58 da shafin ya bayyana."

Hukumar ta tsefe yawan masana'antun da suka haɗa da ƙanana da matsakaita da kuma manyan masana'antu;

  • Ƙananan Masana'antu: 2,048
  • Wuraren sana'a: 1,301
  • Matsakaita: 215
  • Manyan masana'antu: 68

Jadawalin masallatan Juma'a a kano

..

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar ƙididdgar ta Kano, KSBS ta fitar da jadawalin masallatai da ke ƙananan hukumomin jihar 44 na jihar, inda wasu ƙananan hukumomin suka fi wasu yawan masallatan.

  • Ajingi - 46
  • Albasu - 42
  • Bagwai - 39
  • Bebeji - 52
  • Bichi - 60
  • Bunkure - 51
  • Dala - 34
  • Dambatta - 64
  • Dawakin Kudu - 72
  • Dawakin Tofa - 61
  • Doguwa - 54
  • Fagge - 27
  • Gabasawa - 61
  • Garko - 54
  • Garun Mallam - 34
  • Gaya - 41
  • Gezawa - 70
  • Gwale - 61
  • Gwarzo - 54
  • Kabo - 42
  • Kano Municipal - 28
  • Karaye - 38
  • Kibiya - 41
  • Kiru - 48
  • Kumbotso - 119
  • Kunchi - 36
  • Kura - 43
  • Madobi - 44
  • Makoda - 35
  • Minjibir - 45
  • Nasarawa - 63
  • Rano - 40
  • Rimin Gado - 28
  • Rogo - 67
  • Shanono - 33
  • Sumaila - 210
  • Takai - 64
  • Tarauni - 39
  • Tofa - 39
  • Tsanyawa - 50
  • Tudun Wada - 59
  • Ungogo - 96
  • Warawa - 36
  • Wudil - 23

Jimillar yawan masallatai = 2,333

Yawan masana'antun Kano a shekarun 1990

..

Asalin hoton, Getty Images

Alƙaluma daga ƙungiyar masu masana'antu a Kano, (MAN) sun nuna cewa har zuwa shekarun 1990, akwai manyan masana'antu fiye da 300 da suke a yankunan masana'antu uku a Kano da suka haɗa da Sharaɗa da Challawa da Bompai.

Ƙididdiga ta nuna cewa al'amarin masana'antu a Kano ya fara taɓarɓarewa ne a farko-farkon shekarun 2000 inda fiye da manyan masana'antu 200 suka daina aiki tare da rufe kamfanonin sakamakon wasu matsaloli da suka haɗa da rashi tare da wutar lantarki.

Kuma wannan dalilin ne ake ganin shi ne babban dalilin komawar wasu kamfanonin zuwa kudancin Najeriya musamman jihohin Ogun da Legas.

Tun daga lokacin ne gwamnatocin jihar daban-daban ke ta bayyana ƙoƙari da tsare-tsarensu wajen ganin jihar ta sake komawa matsayinta na baya to amma da alama har kawo yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.