Ƙasashen Gulf za su fara biyan mu kan tsaron da muke ba su - Trump

Asalin hoton, Aaron Schwartz/CNP/Bloomberg via Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce dole ne ƙasashen yankin Gulf su biya Amurka saboda kariyar da za ta ba su daga hare-haren Iran.
Iran ta fara kai hare-hare kan sansanonin sojij Amurka da ke ƙasashen yankin, a matsayin martani kan hare-haren Amurka.
Yayin da yake magana game da batun a Fadar White House, Shugaba Trump ya ce Amurka za ta ci gaba da bai wa ƙasashen na yankin Gulf tsaro, amma kuma dole ne su biya.
"Ina so su biya, saboda muna aikin kare yanki mai arziki ne a duniya, don haka ya kamata a biya mu wannan aiki,'' in ji shi.
Shugaban na Amurka ya ci gaba da cewa ƙasashen na buƙatar taimakon Amurka.
"Za mu samu kuɗi daga ƙasashe irin su Saudiyya da UAE da Qatar da Bahrain da Kuwait da sauran ƙasashen, Ba mu muke buƙatarsu ba, su ne suke buƙatarmu. Mu muna da wadataccen mai, ciki har da na Venezuela,'' kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Shugaban na Amurka ya kuma bayyana cewa ƙasarsa za ta rufe tasoshin ruwan Iran.
Ya kuma bayyana cewa za a ɗora wa kowane jirgin dakon mai da zai wuce ta mashigar Hirmzu harajin kashi 20.

