Za mu shafe Iran daga duniya - Trump

Hoton Donald Trump

Asalin hoton, Reuters

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban Trump ya sake yin gargadi ga Iran, yana mai kira gare ta, da ta fa hanzarta ta amince da yarjejeniyar zaman lafiya, idan ba haka ba lokaci na kure mata.

Shugaban na Amurka ya sake barazanar ne, bayan da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi magana da shi, a kan rikicin na Iran.

Kafofin yada labarai na Isra'ila, sun ruwaito cewa shugabannin biyu sun tattauna a kan komawa fagen yakin gadan-gadan, da kuma yuwuwar kai sababbin hare-hare na hadin guiwa, to amma dai babu tabbacin hakan a hukumance.

Wakilin BBC ya ce akwai jin cewa, yanzu Iraniyawa na jin cewa su suke da dama sosai da ta cewa, ganin yadda suka iya jurewa har lamarin ya kawo yanzu.

Tun da farko kafar yada labarai ta Iran ta ce Amurka ta gaza wajen yin sassauci a martaninta ga bukatun da Iran ta gabatar na tattaunawar zaman lafiyar, domin kawo karshen rikicin.

Kafar labaran ta Mehr ta ce, rashin sassauci daga gwamnatin Amurka zai kai ga kiki-kaka a tattaunawar.

Sakon shugaban na Amurka ya kara jaddada barazanarsa ta, ta watan Afirilu kafin sanar da dakatar da bude wuta, cewa zai shafe Iran baki daya daga doron duniya, muddin ba ta amince da yarjejeniyar kawo karshen yakin ba.

A farkon makon nan Trump ya ce yarjejeniyar dakatar da bude wutar, na cikin wani yanayi na kila-wa-kala, bayan da ya yi watsi da bukatun gwamnatin Iran, inda ya ayyana su a matsayin wadanda ba za a amince da su ba sam-sam.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghaei, ya jadadda cewa su dai kasarsu suna da sanin ya kamata da kuma kyautatawa.

Tun a watan da ya gabata aka ayyana dakatar da bude wuta a rikicin - domin bayar da damar tattaunawar zaman lafiya - wadda Pakistan ke shiga tsakani, kuma har yanzu bangarorin biyu sun yi hannun riga da juna sosai a matsayarsu.

Kamfanin dillancin labarai mai 'yar alaka da gwamnatin Iran Tasnim, ya ruwaito bukatun da Iran ta gabatar da suka hada da kawo karshen yakin ta kowane bangare - wanda hakan na nufin hare-haren da Isra'ila ke kai wa Hezbollah a Lebanon, da kawo karshen rufe tashoshin jiragen ruwa na Iran da Amurka ta yi, da kuma tabbacin cewa ba za a kara kai wa Iran hari ba.

Haka kuma Iran din ta nemi a biya ta diyya kan barnar da aka yi mata ta yakin, tare da jaddada 'yancinta na mallakar Mashigar Hormuz.

Kamfanin dillancin labarai na Fars, da ke Iran ya ruwaito a ranar Lahadi cewa, gwmnatin Amurka ta gindaya sharuda biyar a martaninta ga bukatan na Iran.

Waɗanne sharudda ne?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sharudan sun hada da cewa cibiya daya kawai Iran za ta bari ta nukiliya ta yi aiki, sannan ta mayar da dukkanin sinadarin yureniyom da ta inganta zuwa Amurka.

A ranar Juma'a Trump ya nuna cewa zai amince Iran ta dakatar da shirinta na nukiliya tsawon shekara 20 - wanda wannan batu ne da ya kawo kiki-kaka tsakanin kasashen biyu, wanda kuma wannan ya nuna alamun Amurka ta dawo daga rakiyar matsayarta ta hana Iran shirin nukiliya gaba daya.

Dakarun Amurka da na Isra'ila sun fara yi wa Iran luguden wuta a ranar 28 ga watan Fabarairu, 2026.

Dakatar da bude wutar da aka yi domin bayar da damar tattaunawar kawo karshen yakin na ci gaba da gudana duk da musayar wuta kadan-kadan da ake yi tsakanin bangarorin a lokaci zuwa lokaci.

Haka Iran ta ci gaba da rike iko da Mashigar Hormuz, inda kusan a ce ta rufe hanyar da ake bi da kusan kashi 20 cikin dari na mai da iskar gas na duniya.

Wannan mataki da Iran ta ce ta yi shi ne a martanin hare-haren da Amurka da Isra'ila ke kai mata, ya sa farashin mai ya yi tashin gwauron zabi a duniya.