Me ya sa yarjejeniyar nukiliya tsakanin Amurka da Saudiyya ke janyo ce-ce-ku-ce?

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
- Marubuci, Luis Barrucho
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Amurka da Saudiyya sun rattaba hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniya wadda rahotanni ke cewa za ta iya bai wa masarautar Saudiyya damar tace sinadarin uranium a cikin gida.
A cewar Ma'aikatar Makamashi ta Amurka, yarjejeniyar wadda aka bayyana a matsayin 'yarjejeniyar haɗin gwiwa kan makamashin nukiliya domin zaman lafiya za ta ba kamfanonin Amurka damar shiga da kuma taka muhimmiyar rawa a shirin makamashin nukiliya na Saudiyya."
A karkashin yarjejeniyar, Saudiyya za ta bunƙasa shirinta na makamashin nukiliya, sai dai har yanzu ba a bayyana abin da yarjejeniyar ta kunsa ga jama'a ba.
Ana iya amfani da uranium da aka tace a matsayin makamashi wajen tafiyar da tashoshin samar da wutar lantarki na da kuma wajen ƙera bama-baman nukiliya.
Masana sun ce akwai fargabar cewa yarjejeniyar na iya haifar da yaɗuwar fasahar nukiliya a nan gaba a yankin da tuni ke fama da rashin kwanciyar hankali.
Amurka da Isra'ila sun ce daya daga cikin dalilan da suka sa suka kai hari kan Iran shi ne domin hana ta samun damar kera makamin nukiliya a nan gaba.
Sai dai Iran ta musanta cewa tana da wani shiri na samar da irin wannan makami, tana mai cewa shirinta na nukiliya an tsara shi ne domin amfani da makamashin zaman lafiya.
Batun makamashin nukiliya ya kasance a tsakiyar rikicin da ya dauki watanni Amurka da Isra'ila na yi da Iran.
Saboda haka, duk wata yarjejeniya da ta shafi tace uranium a yankin Gabas ta Tsakiya na jawo hankalin duniya, musamman saboda yiwuwar amfani da wannan fasaha wajen samar da makamashin nukiliya ko kuma makaman nukiliya."
Ko za a amince wa Saudiyya ta tace uranium a cikin ƙasarta?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Idan rahotannin da kafafen yaɗa labarai na Amurka suka ruwaito suka tabbata, yarjejeniyar nukiliyar Saudiyya za ta kasance ɗaya daga cikin abubuwan da ba a saba gani ba.
A cewar hukumar Makamashi ta Amurka, ƙasar na da abin da take kira 'yarjejeniyoyin haɗin gwiwa kan makamashin nukiliya domin zaman lafiya' da kusan ƙasashe 50 a duniya.
Irin waɗannan yarjejeniyoyi na bai wa ƙasashen da abin ya shafa damar musayar kayayyaki da kayan aikin nukiliya, ciki har da makamashin da ake amfani da shi wajen sarrafa cibiyoyin nukiliya, na'urorin samar da makamashi, da fasahohin da suka shafi fannin, tare da gudanar da bincike tare a wannan fage.
Sai dai zuwa yanzu, ƙasashe biyu kacal watau Indiya da Japan ne aka bai wa damar tace uranium a cikin ƙasashensu, wadda wata muhimmiyar hanya ce da ake amfani da ita wajen samar da makamashin da cibiyoyin nukiliya ke amfani da shi, amma kuma ita ce fasahar da za a iya amfani da ita wajen ƙera makaman nukiliya.
Sauran ƙasashen kuwa dole ne su rika shigo da makamashin nukiliya daga ƙasashen waje, sannan kuma an hana su sake sarrafa makamashin nukiliya da aka riga aka yi amfani da shi a cibiyoyin samar da wutar lantarki.
Ta wannan hanya, ana iya sake samun sinadaran nukiliya masu amfani irin su plutonium da uranium daga makamashin da aka yi amfani da shi a cibiyoyin nukiliya.
Daga cikin ƙasashen da aka hana yin hakan har da maƙwabciyar Saudiyya, wato Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE)
Rosemary Kelanic, daraktar shirin Gabas ta Tsakiya a cibiyar bincike ta Defense Priorities da ke Amurka, ta ce zai zama abin mamaki matuƙa idan har yarjejeniyar ta ƙunshi amincewar Amurka ga Saudiyya ta gina cibiyoyin tace uranium a cikin ƙasarta.
Amurka ba ta taɓa yin irin wannan ba a baya. Ba mu taɓa taimakawa wata ƙasa ta samu damar tace uranium a cikin ƙasarta ba," in ji ta.
Ta ƙara da cewa dalilin hakan shi ne saboda, "idan ƙasa na iya samar da makamashin nukiliyarta da kanta, haɗarin cewa za ta iya amfani da wannan damar wajen ƙera makaman nukiliya yana ƙaruwa sosai.

Asalin hoton, Getty Images
Mene ne uranium da aka tace ?
Uranium wani sinadari ne da ake samu a cikin ɓawon ƙasa.
Yawancinsa ya ƙunshi nau'o'in sinadari guda biyu da ake kira isotopes, wato uranium-238 (U-238) da uranium-235 (U-235).
Fiye da kashi 99 cikin 100 na uranium nau'in uranium-238 (U-238) ne, wanda ba ya samun sauƙin ci gaba da samar da jerin martanin nukiliya (nuclear chain reaction) da kansa.
Bambancin uranium na samar da nukiliya da kuma na ƙera makamai
Mabambantan matakan tace uranium ne ke sa ya dace da amfani iri daban-daban
Uranium da aka tace zuwa ƙaramin mataki , wanda yawanci ke ɗauke da tsakanin kashi 3 zuwa 5 cikin 100 na uranium-235 (U-235), ana amfani da shi a matsayin makamashi a tashoshin samar da wutar lantarki na nukiliya na kasuwanci."
Wannan adadi ya isa wajen ci gaba da samar da makamashin nukiliya da ake sarrafawa cikin aminci, amma zai iya ƙasa matakin da ake buƙata wajen ƙera makaman nukiliya.
Shin ko Saudiyya za ta ƙera bam ɗin nukiliya?
A cikin sanarwar da ta bayyana yarjejeniyar a ranar 22 ga watan Yuli, Ma'aikatar Makamashi ta Amurka ta lura cewa baya ga yarjejeniyar haɗin gwiwar, an kuma rattaba hannu kan wata 'yarjejeniyar kariya ta bai-ɗaya tsakanin ƙasashen biyu'
"Tare, waɗannan yarjejeniyoyi biyu sun kafa tubalin doka na wata haɗin gwiwa ta dogon lokaci da za ta ɗauki shekaru masu yawa kuma darajarta ta kai biliyoyin daloli'' in ji sanarwar.
Gwamnatin Saudiyya ita ma ta fitar da sanarwa, inda ta ce yarjejeniyar 'na wakiltar ci gaba da faɗaɗa haɗin gwiwar da ta daɗe tana gudana tsakanin ƙasashen biyu a fannin makamashi'.
Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa yarjejeniyar ta zo ne bayan ziyarar , Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, ya kai Washington a watan Nuwamban bara.
Bin Salman ya shaida wa CBS News a shekarar 2018 cewa ƙasarsa ba ta da shirin mallakar makamin nukiliya. Sai dai ya ƙara da cewa, 'ba tare da wata shakka ba, idan Iran ta ƙera bam ɗin nukiliya, mu ma za mu bi sahunta da wuri-wuri.'"
Yana da muhimmanci a lura cewa ƙasar Saudiyya ta fara ƙoƙarin bunƙasa shirinta na makamashin nukiliya tun daga shekarar 2010.
Sai dai a halin yanzu Saudiyya ba ta da wata tashar makamashin nukiliya da ke aiki.
A cewar Ƙungiyar Makamashin Nukiliya ta Duniya (World Nuclear Association), wadda ke wakiltar masana'antar makamashin nukiliya ta duniya, Saudiyya ba ta da damar samar da makamashin nukiliya a halin yanzu."











