Za mu yi amfani da kuɗin Iran da muke riƙe da su wajen biyan kuɗin yaƙi - Trump

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce gwamnatinsa za ta yi amfani da kuɗaɗen Iran da ke ƙarƙashin ikon Amurka wajen biyan kuɗin ɓarnar da yaƙin baya-bayan nan ya haddasa.
Da yake magana da manema labarai a cikin jirgin shugaban ƙasa na Air Force One, Trump ya kuma yi watsi da rahotannin da ke nuna damuwa kan ƙarancin makamai a hannun Amurka bayan watanni ana kai hare-hare kan Iran.
Ya ƙara da cewa tsohon shugaban ƙasar Joe Biden ya aika makamai masu yawa zuwa Ukraine, lamarin da ya sa Amurka ke ƙoƙarin sake cike ma'ajiyarta a yanzu.
"Duk da haka, har yanzu muna da makamai masu yawa. A gaskiya muna da tarin makamai fiye da yadda za mu iya amfani da su," in ji Trump.

















