Zarge-zarge 5 da shugaban Nijar ya yi kan Faransa da ƙasashe maƙwafta

Nijar

Asalin hoton, CCPRN

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban mulkin Sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tciani ya zargi Faransa da hannu wajen kitsa ayyukan ta'addanci a ƙasarsa.

Cikin wata hira da manema labarai a wani ɓangaren na cikarsa shekara uku kan karagar mulki, Janar Tiani ya ce Faransa ce ke kitsa mafi yawan ayyukan ta'addanci a ƙasarsa.

A ranar 26 ga watan Yulin 2023 ne Janar Tiani ya ƙwace mulkin Nijar ta hanyar juyin mulki, inda har yanzu yake ci gaba da tsare tsohon zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum.

Tun bayan hawansa mulkin ne kuma, Janar Tiani ya raba gari da Faransa, wadda ta kasance uwar gijiya ga jamhuriyar Nijar.

Jamhuriyar Nijar na fama da matsalolin ƴanbindiga waɗanda ke kai hare-hare kan cibiyoyin gwamnati da fararen hula a ƙasar.

Shugaban na Nijar ya jima yana zargin ƙasashen yamma da hannu wajen rashin zaman lafiya da jamhuriyar Nijar ke fuskanta.

Cikin jawabin nasa, Janar Tiani ya zayyano wasu manya-manyan zarge kan Faransa da wasu ƙasashen yamma.

Manyan zarge-zargen

A jawabin da ya kwashe kusan sa'o'i biyu yana yi wa manema labarai, shugaban na Nijar ya fi mayar da hankali kan Faransa da shugabanta da wasu ƙasashen Turai, inda ya zarge su da hannu a ayyukan ƴanbindiga a ƙasar.

Sai dai bai bayar da ƙwararan hujjoji da ke tabbatar da zargen-zargen nasa ba.

Zarge-zargen sun haɗar da:

Harin filin jirgin saman Yamai

Janar Tiani ya zargi Faransa da kitsa hare-hare biyu da ƴanbindiga suka kai wa babban filin jirgin saman Yamai har sau biyu.

Babban filin jirgin sama na Diori Hamani da ke Yamai ya fuskanci hare-hare har guda biyu a wannan shekarar da muke ciki daga ƙungiyoyin IS a watan Janairu da kuma JNIM a watan Yuni.

Shugaban na Nijar ya ce Faransa ta ɗora wa ƙungiyar JNIM da ƙawayenta alhakin lalata babban filin jirgin saman.

Ya kuma zargi hukumomin leƙen asirin Faransa da horas da mayaƙan ƙungiyar NJIM da ƙawayenta.

Shugaban Nijar

Asalin hoton, CCPRN

Harin fadar shugaban ƙasa

Shugaban na Nijar ya kuma zargi Faransa da kitsa wani hari da ya ce bai yi nasara ba kan fadar gwmanatin ƙasar da wani sansanin soji da ke kusa da fadar.

''Mun samu bayanin cewa sun kitsa kawo hari fadar shugaban ƙasa, an a kawo hari sansanin soji na Tundubiya'', in ji shi.

Janar Tiani ya caccaki ƙungiyoyin da ya ce suna fakewa da iƙirarin jihadi wajen kai hare-harensu.

''In jihadi suke iƙirari, Nijar ce ke buƙatar jihadi ko Faransa, in jihadi da sunan Musulunci Nijar ta kai shekara 1,400 da addinin Musulunci, tun ma kafin Musulunci ya shiga wasu yankunan Saudiyyya'', in ji shi.

Amfani da sojojin haya

Shugaban mulkin na Nijar ya kuma zargi Faransa da wasu ƙasashen Turai da ɗaukar sojojin haya daga cikin ƙasar da maƙwabtanta domin aiwatar da muradunsu.

''Ai ba su ne ke zuwa ba, kamar yadda suka yi a Vietnam da aka yi yaƙi aka kusan ƙarar da dakarunta, sun yi yaƙi da Aljeriya da suka ga za su ƙare suka daina, to amma mu nan matsalar ba su ne suke zuwa ba''.

''Sojojin haya ne suke ɗauka waɗanda suke juya wa tunani, suke ba su kuɗi da makamai domin su zo su yi yaƙi'', in ji shugaban na Nijar.

Zargin maƙwabtan ƙasashe

Janar Tiani ya kuma zargi maƙwabtan ƙasashe da bin umarnin shugaban Faransa, Emmanuel Macron wajen ingiza ayyukan ƴanbindiga a Sahel.

''Ƙasashe irin su Benin da Mauritania da Cote d'Ivoire na aiki da umarnin Macron wajen kitsa hare-hare a ƙasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso'', in ji shi.

Ya yi zargin cewa hare-haren da ƙungiyar JNIM ta kai Mali a watan Afrilu an shirya shi ne daga ƙasashen uku.

"Sun kai wa Mali hare-hare daga ɓangarori uku, na farko daga arewacin Benin ɗayan kuma daga gefen Côte d'Ivoire, sai ɗayan daga yankin Mauritania," in ji shi.

'Yaƙi da ƙasashen yamma'

Shugaban na jamhuriyar Nijar ya ce ba masu riƙe da makamai kawai ƙasarsa ke yaƙi da su ba, suna yaƙi ne da ƙasashen yamma.

''Ba Faransa ce kawai muke yaƙi da ita ba, akwai wasu ƙasashen Turai da muke zargi suna taimaka wa waɗannan ƙungiyoyi'', in ji shi.

Ya ce wasu ƙasashen suna taimaka wa ƙungiyoyin da kuɗaɗe, wasu kuma suna taimaka musu da horas da mayaƙa.

Shugaban na Nijar ya ce duka shugabannin ƙungiyoyin ƴanbindigar babu ɗan yankin Sahel ko ɗaya.

''Ko da wancan ɗan Mali, shi ma umarni kawai yake karɓa, ba shi ne ke aiwatar da abin da yake so ba,''in ji shi.

Ba wannan ne karon farko da shugaban na Nijar ke zargin Faransa ko ƙasashen yamma da hannu a hare-haren ƴanbindiga a ƙasar ba.

Ko a shekarar 2024 ma shugaban na Nijar ya zargi Faransa na Ecowas da ma Najeriya da hannu a taɓarɓarewar tsaron ƙasarsa.

Kawo yanzu dai Faransa ba ta yi wani martani ba game da waɗannan zarge-zargen.

WHR ta soki gwamnatin Nijar

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

To sai dai a gefe guda ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Human Rights Watch ta zargi gwamnatin mulkin sojin Nijar ɗin da ƙara ƙarfafa ikonta a kan mulki da kuma ƙaddamar da abin da ta bayyana da tauye ƴancin ƴanjarida.

Ƙungiyar ta ce gwamnatin sojin ta ruguza cibiyoyin dimokuraɗiyya da ƙuntata yancin ɗan'adam tare da raunana hukumomin sa ido masu zaman kansu.

Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a daidai lokacin da Janar Tiani ke cika shekara uku da hawa mulki, ta zargi gwamnatinsa da ruguza jam'iyyun siyasa da ƙungiyoyin fararen hula da kuma tauye ƴancin ƴanjarida a ƙasar.

Human Right Watch ta kuma zargi gwamnatin Janar Tiani da cire Nijar daga zama mamba a Kotun Duniya ta ICC da kuma tsawaita wa'adin mulki ba tare da ayyana jadawalin zaɓe ba.

''Fita daga ƙungiyar Ecowas da Kotun ICC wani shiri ne na raunana sanya idanu daga ƙungiyoyin sanya idanu na ƙasashen waje'', in ji ƙungiyar.

HWR ta kuma zargi shugabannin mulkin sojin na Nijar da faɗaɗa ikonsu ta hanyar toshe ƙofofin ƴancin ɗa'adam.

Ƙungiyar ta kuma soki ci gaba da tsare tsohon shugaban ƙasar, Mohammd Bazoum da mai ɗakinsa da kuma tsohon Minista Hamma Amadu Sule da fitaccen mai fafutikar kare haƙƙin bil'adama Moussa Sangare.