Shin yaƙin Iran da Amurka ya zo ƙarshe ne?

Iran iyo Maraykan

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Ana ci gaba da jiran tsammanin cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka kan yakin da ke gudana.

Kafar yada labaran Amurka, Axios ta ce fadar gwamnatin Amurka ta nuna cewa an kusa cimma yarjejeniya.

Haka nan shugaban Amurka Donald Trump ya ce yarjejeniyar tsagaita wita tsakanin kasashen biyu na nan daram duk da harkallar da aka samu kwanaki biyu da suka gabata a Mashigar Hormuz.

Rahotannin sun ce yarjejeniyar da Amurka ta gabatar shafi daya ce mai kunshe da sharudda 14.

Wasu daga cikin bukatun Amurkar sun hada da cewa Iran za ta kawo karshen shirinta na nukiliya, inda ita kuma Amurka za ta dage takunkuman da ta kakaba mata, sannan kuma za a bude Mashigar Hormuz.

Dakatar da shirin Iran na nukiliya da kuma bude Mashigar Hormuz su ne abubuwa biyu da ke yin cikas ga kawo karshen yakin.

Rahoton kafar yada labarai ta Axios ya ce bukatun da Amurka ta gabatar sun bayar da haske kan cewa Amurka na son a kawo karshen yakin.

Sai dai yayin da ake jiran jin martanin Iran, Amurka na ci gaba da toshe tashoshin jirgin ruwa na Iran.

Trump ya nuna cewa ana lalubo mafita

Shugaban majalisar tsaro ta Iran Ibrahim Rezaei, ya bayyana yunkurin da ake yi na lalubo hanyar zaman lafiya a matsayin mai ficewa.

Sai dai Rezaei ya ce a ankare suke idan har Amurka ta ki amincewa da sharuddan Iran.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Ismail Bakeei ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Iran ISNA cewa Iran na ci gaba da nazari kan sharuddan Amurka na kawo karshen yakin.

Bakei ya ce ita Iran ta gabatar da tata bukatun ne ta hannun masu shiga taakani na Pakistan.

Bugu da kari a wani bayani da ya wallafa a shafin sada zumunta na X, Bakei ya ce “masu shiga tsakani na da bukatar yin aiki tukuru wajen warware rikicin.”

“Ana bukatar yin tattaunawa da zuciya daya, kuma hakan na nufin tattaunawa ba gardama ba ce, ba kokarin tilastawa ba ne, ba yaudara ba ce ko kuma amfani da karfin tuwo ba, in ji shi.

Mene ne masana ke cewa?

Masana na cewa za a sha wahala wajen comma duk wata yarjejeniyar kawo karshen yakin, kuma za a dauki dogon lokaci, musamman idan aka zo kan maganar watsi da shirin nukiliya na Iran.

Wakili a fadar shugaban Amurka Bernd Debusmann da kuma mai sharhi kan siyasa Holly Dagres sun ce gwamnatin Donald Trump ba za ta amince da wata yarjejeniya ba har sai an cimma matsaya kan batun nukiliyar Iran.

Akwai kuma shakku kan ko dakatar da shirin Amurka na yi wa jiragen ‘yan kasuwa rakiya ta mashigar Hormuz ko kuma bude mashigar ba zai kawo cikas ga cimma yarjejeniyar ba.

Wani tsohon babban jami’i a ma’aikatar tsaro ta Amurka ya fada wa BBC cewa, “idan aka cimma wannan yarjejeniya hakan zai bayar da damar sakin jiragen ruwa da aka kama kuma zai zamo ginshiki wajen kawo karahen yakin.