Ko gwamnatin jihar Kano za ta iya kawar da matsalar daba?

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da ake ci gaba da samun ƙaruwar matsalolin daba da amfani da makamai a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, ma'aikatar shari'ar jihar ta ce za ta fara gaggauta gurfanar da wadanda aka kama da laifin aikata daba.
Abdulkarim Kabiru Maude, babban lauya a Najeriya, wanda kuma shi ne kwamishinan ma'aikatar, ya ce saboda yadda matsalar ke neman kazancewa za su yi aiki da dukkan jami'an tsaro ba-sani-ba-sabo wajen gurfanar da duk wanda aka samu da hannu.
Cikin wata hira da ya yi da BBC, babban lauyan ya ce," Mun fuskanci cewa fadace-fadace na daba a Kano sun fara yawa, a idon haka yanzu akwai rawar da ma'aikatarmu za ta taka domin shawo kan wannan matsala."
" A ma'aikatarmu akwai masu bincike don haka idan har suka yi bincike suka gano cewa akwai kwakkwaran zargi a kan mutum to sai a kawo mana idan aka kawo za mu duba sosai idan har muka tabbatar da abin da ake zargi mutum ya aikata kamar daba, to za mu gurfanar da shi daga nan kuma za a yi masa abin da ya dace daidai da abin da ya aikata." In ji shi.
Abdulkarim Kabiru Maude, ya ce: "Gwamnatin Kano da ma ma'aikatarmu ta shari'a shirye suke su yaki duk wani mai laifi a jihar har ma da wanda yake goya masa baya."
" Wani abu da nake so al'ummar jihar Kano su sani shi ne duk wata harka ta tsaro ba wai jami'an tsaron kawai ta shafa ba, dole sai an hadu da jami'an tsaro da al'ummar gari domin a yaki wannan abin." In ji shi.
Ya ce: "Dole sai an kawar da tsoro na san inda wadannan mutanen suke a dinga kamo su ana kawo su, dole sai al'ummar gari sin shiga wannan lamari domin a taimaki gwamnati dama al'ummar jihar baki daya."
Kwamishinan ma'aikatar shari'ar, ya ce," idan har 'yan unguwa suka hada kansu to babu 'yan dabar da za su gagaresu, domin idan aka hada kai da 'yan unguwa da jami'an tsaro ba karamin yakar 'yan daba za a yi ba."
" Ya kamata mutane su sani suna da damar da za su kama masu laifi su kai su gaban hukuma, ba wai sai lallai jami'an tsaro ne kadai ke da wannan dama ba, 'yan unguwa za su iya fitowa su yi yaki da wannan dabar a kama masu laifi a kai su gaban hukuma mu kuma mu gurfanar da su gaban kuliya." In ji shi.
Abdulkarim Kabiru Maude, ya ce: "Za mu tabbatar da cewa idan har aka kawo mana masu laifi musamman daba za mu tabbatar da doka ta yi halinta ko da kuwa jami'in gwamnati ne ba sani ba sabo."










