Yadda aka zargi ƴansanda da ƙona gidaje da dukiya a jihar Kano

xxx

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Al'ummomin wasu garuruwa a yankin ƙaramar hukumar Wudil a jihar Kano, da ke Najeriya, sun zargi ƴansanda da ƙone musu gidaje da wuraren sana'a da kayan abinci da kuma dabbobi a sanadiyyar wata hatsaniya kan mallakar gonaki.

Rikicin, wanda yanzu haka yake gaban ƙotu, na da alaƙa da batun mallakar gonakin wata fadama a yankin Wudil da Bunkure.

Al'ummun ƙauyuka sun kwashe ɗaruruwan shekaru suna zama tare, inda auratayya da harkoki na tattalin arziƙi ke haɗa su, kasancewar suna zaune ne kan iyakar ƙananan hukumomin Wudin da Bunkure.

Sai dai wani rikici kan filayen noma, wanda ya samo asali sama da shekara 20 da suka gabata na neman kawo cikas ga wannan dangandata.

Mutanen yankin sun shahara ne wajen noman rani da na damina, sai kuma kasuwanci jifa-jifa.

Ba kasafai ake samun rikicin filaye mai muni ba a arewa maso yammacin Najeriya, yankin da ke fama da matsalar rashin tsaro na ƙungiyoyin ƴan bindiga.

Kano ce jiha mafi yawan al'umma a arewacin Najeriya, kuma ita ce babbar cibiyar kasuwanci a yankin, wadda take da tarihin hada-hadar kasuwanci tun a cikin ƙarnoni da dama da suka gabata.

Ramuwar gayya?

xxx

Daga tattaunawar da BBC ta yi da al'ummar ƙauyukan, lamarin ya faru ne bayan wasu "jami'an tsaro" sun ziyarci ƙauyukan Katai da Faudan da Gaba-Gaɗi a ƙaramar hukumar Wudil domin kama wasu da ke kan gaba-gaba a shari'ar da ake yi kan filayen da ake taƙaddama a kai.

Jami'an sun je ƙauyukan ne a makon da ya gabata, sai dai an samu hargitsi a lokacin da wasu matasa suka bijire wa yunƙurin jami'an na kama mutanen ƙauyen.

Hakan ya kai ga cewa an riƙa jifar jami'an da duwatsu, inda suka fice babu shiri.

Sai dai azal ta faɗa wa ɗaya daga cikin jami'an, inda mutanen ƙauyen suka kama, kuma ake zargin sun masa duka har rai ya yi halinsa.

A washegari, ranar Juma'a ne wasu mutane da al'ummar ƙauyen ke zargin ƴansanda ne suka dawo ƙauyen, inda suka ƙona gidaje da ɗakunan ajiye hatsi da kuma dabbobi.

Mazauna ƙauyukan sun zargi ƴansanda da aikata lamarin a matsayin ramuwar gayya sanadiyyar kisan ma'aikacin da aka yi a makon da ya gabatan.

Wane hali ake ciki a ƙauyukan?

xxx

Bayan al'amarin da ya faru a makon da ya gabata, yanzu haka al'ummun waɗannan ƙuyuka na rayuwa cikin tsoro da fargaba.

Gidaje da dama sun ƙone ƙurmus, an ƙona rumbunan hatsi har ma da dabbobi.

Muhammad Yakubu, mazaunin Katai ya ce an ƙona masa wurin sana'a da kuma gidansa.

Tsaye a wurin rumfarsa da aka ƙona, Yakubu mai sana'ar niƙa, wanda ya fashe da kuka a lokacin da yake tattaunawa da BBC ya ce an ƙona duk wani abu da ya mallaka.

Katai

''An ƙone min komai, babu sauran abin da ya rage min," in ji Yakubu.

Ya bayyana wa BBC cewa babu abin da ya tsira da shi daga cikin kayan hatsi da ya noma, baya ga "wanda na fitar na yi zakkar fidda-kai".

A yanzu mazauna ƙauyen Katai na zargin mazauna ƙauyukan da ke maƙwaftaka da jagorantar jami'an tsaro domin ƙona musu ƙauye da kayan amfanin gona da suka tara.

Me jami'an tsaro suka ce?

Duk wani ƙoƙari da BBC ta yi na ji daga bakin ƙaramar hukumar Wudil kan wannan lamari, ya ci tura, domin mahukuntan sun ƙi cewa komai.

Shi ma kakakin rundunar 'yansandan jihar Kano CSP Abdullahi Haruna Kiyawa da wakilin namu ya tuntuɓe shi kan lamarin da kuma zarge-zargen da ake yi wa 'yansandan, ya ce za su fitar da sanarwa, wadda har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton BBC ba ta ji daga gare shi ba.

Haka su ma hukumomin jihar Kano ba su ce komai ba kan lamarin.

Ƙarin bayani daga Zahradden Lawan a Kano