'Abin da ya sa Perez ke neman Mourinho ya koma Real Madrid'

    • Marubuci, Guillem Balague
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Columnist
  • Lokacin karatu: Minti 4

A yanzu da aka yi waje da ƙungiyar Real Madrid a gasar zakarun turai, sannan kuma ƙungiyar Barcelona ta ba ta tazarar maki 11 a teburin gasar La liga ta Spain, hankali ya fara komawa kan tambayar ko kocin ƙungiyar, Alvaro Arbeloa ba zai iya ba ne?

Arbeloa ne ya maye gurbin Xabi Alonso a matsayin kocin ƙungiyar, inda ake ganin babu wani sauyi da aka samu musamman a gasar La liga.

Alonso ya raba gari da Barnabeu ne da nasarar kashi 74 a wasannin da ya jagoranta, amma shi kuma Arbeloa, wanda ya jagoranci ƙungiyar a wasannin da suka yi ƙasa da na Alonso da wasa biyar, yanzu haka yana da nasarar kashi 64 ne kawai.

Da wasan da ƙungiyar Albacete ta doke Real Madrid ne Alonso ya fara, inda ƙungiyar wadda ke rukuni na biyu a ƙasar ta doke Real Madrid.

Ɗaya daga cikin waɗanda ake ambatawa za su iya maye gurbin Arbeloa akwai tsohon kocin ƙungiyar, Jose Mourinho, wanda yanzu haka yake horas da ƙungiyar Benfica da ke Portugal.

Mourinho ya horas da Real Madrid ne a tsakanin 2010 zuwa 2013, inda ya lashe gasar La liga da Copa del Rey da kofin Super Cup ta Spain.

Mai sharhi kan harkokin wasanni, Guillem Balague ya bayyana wa BBC dalilan da suka sa shugaban ƙungiyar, Florentino Perez ke ƙaunar Mourinho.

Mourinho zai iya komawa Madrid?

Yanzu haka dai Madrid ba ta da tsayayyen koci a kakar baɗi.

Kwantiragin shekara ɗaya tal ne ya rage wa Arbeloa, sannan a bayyane yake shugaban ƙungiyar Perez ya fara neman sabon mai horaswa.

Duk da cewa Perez na yaba aikin Arbeloa, sakamako mai kyau ne kaɗai zai tabbatar da koci a ƙungiyar.

Amma domin fahimtar irin kocin da ƙungiyar ke so, yana da kyau a fahimci irin tunanin Perez.

Shi dai Perez bai cika damuwa da yanayin murza leda ba. Bai cika damuwa ba don wai ƙungiyarsa ba ta kai hare-haren zura ƙwallaye ba, ko kuma don an fi ta raba ƙwallo. Shi dai kawai burinsa a samu nasara.

Abu na biyu da yake da matuƙar muhimmanci a wajensa shi ne jagoranci. Yana so a sa ido da jagorantar zaratan ƴanwasa da sauran abubuwa.

Akwai saɓani tsakanin jagorori a ƙungiyar kan waye ya fi dacewa da jagorantar ƙungiyar. Mataimakin Perez, Jose Angel Sanchez yana da fahimtar cewa zai fi kyau ƙungiyar ta nemo wanda zai tsara ƙungiyar ya ɗaura ta hanyar komawa ganiya.

Saboda irin wannan tunanin ne Madrid ta ɗauki Rafa Benitez da Julen Lopetegui da kuma Alonso na baya-bayan nan. Sai dukansu ba su daɗe ba.

Kuma tun farko shugaban ba ya tare da irin tsarin, don haka da zarar ya ga ba a samun sakamakon da ake buƙata, sai ya yi waje da su.

A nasa ɓangaren, Perez na son koci ne mai ƙarfin faɗa a ji, wanda ake girmamawa sosai irin su Zinedine Zidane da Carlo Ancelotti.

Yanzu mutumin da aka fi ambata domin cigaba da jan ragamar ƙungiyar shi ne Jose Mourinho, wanda ya yi daidai da irin tunani da tsarin Perez.

Perez na da tunani da tsarin fitar da abu domin jira tare da jin abubuwan da za a ce kafin ya yanke shawara.

Yanzu haka Mourinho na da kwantiragi da Benfiza har zuwa shekarar 2027, amma zai iya haƙuri da ƙungiyar ta Portugal. Sannan ko ma me ya faɗa, ni dai ina da yaƙin yana matuƙar sha'awar komawa Real Madrid.

Da Mourinho, Perez na ganin ya samu kocin da ya sani, wanda yake tunanin zai iya magana a ji a tsakanin ƴanwasa, wanda da zarar an bayyana shi, duniya za ta ɗauka.

Sauran waɗanda Madrid ke zawarci

Mauricio Pochettino na cikin masu horaswa da ƙungiyar ke tunani. Yanzu haka shi ne kocin tawagar Amurka, kuma shi ne zai jagoranci tawagar a gasar cin kofin duniya.

Sai dai akwai tunanin idan har Amurka ta yi nisa a gasar kofin na duniya, wanda hakan ke nufin har zuwa kusan Yuli ba zai samu komawa ba, ballantana ya samu zuwa wasannin atisaye.

Wani kocin kuma shi ne Didier Deschamps. Yanzu haka horas da tawagar Faransa ne, kuma shi ne zai jagoranci tawagar a gasar cin kofin duniya. Shi ma dai yana fuskantar ƙalubalen kammala gasar kofin duniya kafin ya koma.

Akwai kuma kocin AC Milan Massimiliano Allegri wanda ke da irin tunanin taka leda irin na yanayin Ancelotti.

Haka kuma akwai tsohon kocin Liverpool Jurgen Klopp kuma yana cikin na gaba-gaba wajen zama kocin ƙungiyar ta Madrid.