Ƴan sanda sun kama mutumin da ake zargi da kai harin wuƙa kan wasu Yahudawa a Landan
Ƴan sanda sun kama wani mutum da ake zargi da yunƙurin yin kisa, bayan an kai harin wuƙa kan wasu yahudawa biyu a yankin Golders Green da ke arewacin Landan.
Mutanen da aka kai wa hari na samun sauƙi a asibiti.
Wata ƙungiyar tsaro ta alummar Yahudawa ta ce ta kama tare da tsare wani mutum da ke gudu kan wani titi yana ƙoƙarin hai wa yahudawa hari da wuƙa.
Daga bisani sai ƴan sanda suka kama mutumin da ake zargi.
A yanzu ƴan sanda sashen yaƙi da ta'addanci ne ke jagorantar gudanar da binciken.
Suna ƙoƙarin gano tarihin mutumin, da asalinsa da kuma ko shi kaɗai ya kitsa harin.
Wannan ne hari na baya bayan nan kan jerin munanan hare haren da ake kai wa alummar Yauhudawa a Birtaniya.