Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙasashe 10 da suka fi yawan masu fama da yunwa a duniya
Wani sabon rahoto da ƙungiyar Global Network Against Food Crises (GNAFC) mai yaƙi da ƙarancin abinci a duniya ta fitar, ya nuna damuwa kan ƙaruwar matsalar yunwa a faɗin duniya.
Cikin rahoton ƙungiyar na 2026, da ta saba fitarwa shekara-shekara ya nuna cewa fiye da mutum miliyan 266 a ƙasashe 47 na duniya fuskantar matsananciyar yunwa.
GNAFC ta lissafo ƙasashe 10, ciki har da Najeriya da aka fi samun masu fama da matsalar yunwa a duniya, a rahoton nata na 2026.
Ƙungiyar ta kuma yi gargaɗin samun ƙaruwar matsalar idan ba a yi ƙoƙarin magance matsalolin da ke haddasa ƙaruwar yunwar ba.
La'akari da rahoton ƙungiyar, GNACF da kuma na shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya, WFP, mun lissafo ƙasashe 10 da ke kan gaba a yawan masu fama da yunwa a duniya.
Najeriya - Mutum miliyan 35
Najeriya na cikin jerin ƙasashe na farko-farko da rahoton na GNAFC ya ambato a matsayin waɗanda suka fi yawan masu fama da yunwa a duniya.
Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya WFP ya bayyana cikin wani rahoto da ya fitar a watan Maris na 2026, cewa mutum miliyan 35 ne ke fama da matsalar yunwa a Najeriya.
Rahoton na WFP ya ce yankin arewa maso gabashin Najeriya ne inda matsalar ta fi katutu, inda ƙananan yara da mata suka fi fuskantar matsalar.
WFP ya ce jihohin Borno da Yobe da Adamawa ne matattarar matsalar, inda kusan mutum miliyan 5.8 ke fuskantar matsalar yunwa a jihohin uku.
DR Congo - Mutum miliyan 26.6
A cewar alƙaluman Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya da Shirin lura da wadatar abinci a ƙasashen duniya (IPC) kimanin mutum miliyan 26.6 ne ka fama da matsalar yunwa a ƙasar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
IPC ta ce daga cikin waɗannan alƙaluma akwai kimanin mutum miliyan 3.9 da ke cikin tsananin yunwa.
Ƙungiyar Abinci da Noma ta Duniya (FAO) da kuma shirin WFP sun yi gargaɗin cewa ƙaruwar matsalar jin ƙai a ƙasar ta DR Congo ka iya ƙara tsananta matsalar yunwa a ƙasar, wadda ke fama da rikici.
Sudan - Mutum miliyan 19
Cikin rahoton da Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar a watan Afrilun da muke ciki ya nuna cewa fiye da mutum miliyan 19 ne ke fama da matsalar yunwa a ƙasar Sudan.
Rahoton ya bayyana rikicin da ƙasar ke ciki da hana ƙungiyoyin agaji kai kayan tallafi a matsayin abubuwan da suka ƙara ruruta matsalar.
Shirin na WFP ya ce kusan rabin al'ummar Sudan na fama da matsalar yunwa, musamman a wuraren da ake fama da yaƙe-yaƙe, kamar El-Fasher, inda fiye da mutum miliyan shida ke kan hanyar faɗawa ƙangin yunwa.
Ƙasar Sudan na fama da yaƙin basasa tun 2023, lamarin da ya tilasta wa al'umomi da dama barin gidajensu.
Afghanistan - Mutum miliyan 17.4
Wani rahoton haɗin gwiwa na Majalisar Dinkin Duniya da Ƙungiyar Tarayyar Turai a 2025 ya nuna cewa Afghanistan ce ƙasa ta biyar cikin ƙasashen da mutanensu suka fi fama da yunwa a duniya.
Rahoton ƙungiyar da ke lura da matsalar abinci ta duniya, GRFC ya nuna cewa kimanin mutum miliyan 17.4 ne ke fama da matsalar yunwa a ƙasar ta Afghanistan.
A cewar GRFC kusan kashi 36 na al'ummar ƙasar na fuskantar matsalar yunwa.
Yemen - Mutum miliyan 17
Yaƙin basasar da aka kwashe fiye da shekara 10 ana gwabzawa a ƙasar Yemen ya jefa ta cikin halin matsalar yunwa kamar yadda MDD ta bayyana.
Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya ce kimanin mutum miliyan 17 ne ke fama da matsalar yunwa a ƙasar da ke yankin Gabas ta Tsakiya.
Rahotonni na cewa kimanin mutum miliyan 4.8 ne suka rasa muhallansu sakamakon yaƙe-yaƙen da ƙasar ke fuskanta.
Bangladesh - Mutum miliyan 15
Ƙasar Bangladesh da ke yakin kudancin Asiya na daga cikin wannan jeri na inda aka fi fama da yunwa a duniya.
A cewar rahoton ƙungiyar GNAFC na 2026, kusan mutum miliyan 15 ne ke fama da matsalar yunwa a wannan shekara da muke ciki.
Shirin WFP na tallafa wa ƴangudun hijirar Rohingya kusan miliyan 1.2 a ƙasar, waɗanda suka tsallako daga Myanmar.
Rahoton ya nuna cew a kashi 33 cikin 100 na al'ummar Bangladesh na fuskantar barazanar yunwa.
Myanmar - Mutum miliyan 12
Ƙasar Myanmar mai maƙwabtaka da Bangladesh na cikin jerin ƙasashen duniya da ke fama da matsalar yunwa a wannan shekara ta 2026, a cewar sabon rahoton na ƙungiyar GNAFC.
Fiye da al'ummar ƙasar miliyan 12 ke fama da yunwa kamar yadda rahoton Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna.
A ƙasar Myanmar - wadda ta jima tana fama da yaƙe-yaƙe - iyaye mata ba sa iya samun abincin da za su kula da lafiyarsu, lamarin da ke jefa dubban ƙananan yara cikin matsalar tamowa.
Siriya - Mutum miliyan 9.1
Shekaru kusan 13 da aka shafe ana tafka yaƙin basasa a Siriya, sun jefa wasu al'ummar ƙasar da dama cikin halin yunwa.
Bayanai na cewa al'ummar Siriya na shan wahalar gaske wajen samun damar ciyar da iyalansu.
A cewar rahoton, Siriya ce ƙasa ta biyu mafi yawan ƴangudun hijiya a faɗin duniya.
Pakistan - Mutum miliyan 7.5
Cikin wani rahoto da Majalisar Dinikin duniya ta fitar cikin watan Fabrairun da ya gabata ya nuna cewa kusan mutum miliyan 7.5 na fama da yunwa a ƙasar Pakistan.
Pakistan ta tsinci kanta cikin wannan hali ne sakamakon mummunar ambaliya ruwa da ta auku a ƙasar a shekarar da ta gabata, lamarin da ya haifar da mummunar asara ga fannin noman ƙasar.
Baya ga ambaliya, Pakistan ta kuma fuskanci mummunan fari, wanda shi ma ya gurgunta harkokin noman ƙasar.
Sudan ta Kudu - Mutum miliyan 7.5
usan mutum miliyan 7.56 ke fama da yunwa, kusan rabin al'ummar ƙasar kenan.
Rahoton ya nuna cewa fiye da ƙananan yaran ƙasar miliyan biyu ne ake fargabar za su fuskanci matsalar tamowa a shekara mai zuwa.
A cewar IPC kusan mutum 28,000 ne za su faɗa halin matsanciyar yunwa a wasu yankunan da ke fama da rikice-rikice.
Abubuwan da ke haifar da ƙaruwar yunwa a duniya
Rahoton ya ambato wasu abubuwa da ya ce su ke haifar da matsalar yunwa a fadin duniya da suka haɗa da:
- Rikice-rikice da yaƙe-yaƙe
- Rashin tsaro
- Ƙaruwar ƴangudun hijira
- Hauhawar farashi
- Ɗumamar yanayi
- Ambali ruwa da fari
- Tsadar kayayyakin noma
Hanyoyin magance matsalar
Rahoton ya ce domin magance wannan matsala ta yunwa da ke yi wa duniya barazana akwai buƙatar haɗin kai da aiki tare tsakanin manyan ƙasashen duniya da waɗanda ke fama da matsalar.
''Akwai buƙatar inganta samar da abinci a duniya da ɗaukar matakan bai ɗaya da rage matsalolin jiƙai da kuma jajircewa wajen magance abubuwan da ke haifar da ƙaruwar matsalar'', kamar yadda rahoton ya yi ƙarin haske.
Haka kuma rohoton ya ce akwai buƙatar gwamnatoci a matakai daban-daban da masu bayar da tallafin kuɗi da sauran cibiyoyi su ƙara ƙaimi wajen inganta fannin noma a duniya.
''Yana da kyau a magance matsalolin ɗumamar yanayi da inganta rayuwar mazauna yankunan karkara da samar da ayyukan yi da ƙarfafa hanyoyin gargaɗin mutane domin ba su damar ɗaukar matakan kariy a duk lokacin da aka fitar da sabon hasashe'', in ji rahoton na GNAFC.
Daga ƙarshe kuma rahorton na GNAFC ya ce akwai buƙatar bai wa ƙungiyoyin bayar da agaji kariya, ta hanyar ƙarfafa dokokin duniya kan masu bayar da agaji da kuma jaddada ƙudurorin gwamnatoci domin magance abubuwan da ke haifar da yunwa.