Yadda mutanen wasu garuruwan Sokoto suka watse bayan sace sama da mutum 100

Lokacin karatu: Minti 3

Al'umma da dama ne ke ci gaba da gudun hijira suna barin garuruwansu sakamakon karuwar hare-haren 'yan bindiga a garuruwan Wurno da Achida da makwabtansu da ke jihar Sokoto.

Hukumomi a yankin sun ce kwanan nan 'yan bindigar sun yi garkuwa da akalla fiye da mutum 100 baya ga kisan wasu da dama.

Bayanai na cewa jama'a na cikin fargabar yadda 'yan bindigar ke ci gaba da afka musu, abin da ya tilastawa da damansu ciki har da mata da tsofaffi da ma kananan yara yin hijira zuwa wasu wurare na daban domin tsira da rayukansu.

Honarabul Abba Isa Sadiq‑Achida, shugagabn karamar hukumar ta Achida a jihar ta Sokoto, ya shaida wa BBC Hausa cewa 'yan bindigar sun kwashi mutane da dama a yankin da kewayensa, kuma yanzu haka suna cikin daji tare da su.

Ya ce mutane da yawa ba sa iya kwana a gidajensu, sai da rana suke zuwa, sakamakon fargabar abun da ka je ya zo.

''Babban abun da muke ji ma tsoro shine tun daga Marnona in ka taso, duk kauyukan da ke nan har zuwa Achida duka sun watse, a Achida mutanen ke kwana, kiranmu ga gwamnatin tarayya shine a shiga a yaki wadannan 'yan ta'adda a cikin dazuzzukan nan, dajin da yake kewaye da mu shine ya kai har Zamfara'' inji shi.

'Yan bindigar dai na tare galibin manyan hanyoyin isa ga gari da dare, tun ma ba ranakun da kasuwannin Achida da Goronyo ke ci ba.

A farkon watan nan na Afrilu ma wasu gungun 'yan fashin dajin sun kai hari a garin na Achida inda suka kashe akalla mutum biyu tare da yin garkuwa da fiye da ashirin da biyar.

Yankin na gabashin Sokoto dai na cikin wadanda 'yan bindiga suka fi addaba a shiyar arewa maso yamma, duk kuwa da matakan da jami'an tsaro ke bayyana cewa suna dauka.

Mazauna garin Achida da ke ƙaramar hukumar Wurno a jihar Sokoto sun yi suna wajen dakile wani harin 'yan bindiga, inda ko a baya bayan nan dai da suka kashe ɗaya daga cikin maharan a yayin wata arangama.

A cewar Zagazola Makama, wani mai bayar da rahotannin tsaro a yankin Afrika, lamarin ya faru ne lokacin da 'yan bindiga masu ɗauke da makamai suka kai hari cikin garin, amma mazauna yankin tare da 'yan sintiri na sa-kai suka tare su.

Rahotanni sun nuna cewa mazauna garin sun yi gaggawar haɗa kai domin tunkarar maharan, lamarin da ya tilasta musu ja da baya bayan ɗan gajeren fafatawa.

A yayin artabun, an kashe ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin 'yan bindigar ne, yayin da sauran suka tsere, wasu daga cikinsu na ɗauke da raunuka.