Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙalubalen da ke gaban APCn Kano bayan naɗin Sule Garo
Tuni aka fara tafka muhawara kan matsalolin da ke gaban APC ɓangaren Kano musamman bayan da majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da tantance Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamna.
An sha gumurzu kan wanda zai ɗare kujerar domin maye gurbin tsohon gwamnan jihar, Kwamrade Abdulsalami Gwarzo wanda ya yi murabus bayan majalisar ta ƙaddamar da bincikensa.
Kafin a sanar da Sule Garo, siyasar Kano ta ɗauki zafi kan wanda zai maye gurbin mataimakin, inda aka yi hasashen cewa akwai shi Sule Garon da Kabiru Alhassan Rurum da Suleiman Bichi.
Batun wanda zai zama mataimakin gwamnan ya ja hankali matuƙa, inda aka samu rabuwar kai, har ɓaraka ta kunno kai a tsakanin wasu jagororin jam'iyyar APC na jihar.
A ranar 27 ga watan Maris ɗin 2026 ne Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo ya yi murabus bayan sauye-sauyen sheƙa da aka samu tsakanin gwamnan da mataimakinsa da wasu ƴan majalisar jihar da sauran masu ruwa da tsaki cikin gwamnatin.
Gwamna Abba Kabir da aka sani tare da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ci zaɓe ƙarƙashin jam'iyyarsu ta NNPP, sai ya koma jam'iyyar APC mai mulki, yayin da mataimakinsa Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo ya ƙi bin sa jam'iyyar ta APC ya koma ADC tare da Kwankwaso.
Wannan ya janyo wani sauyi mai yawa a siyasar Kano, inda mutanen da aka sani da tsohon Gwamnan Kano kuma shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje suka koma wajen Kwankwaso ciki har da tsohon ɗan takarar gwamna a APC na 2023 Nasiru Gawuna.
Rigingimun da ke gaban APC
Murtala Sule Garo ya kasance cikin mutum uku da aka yi ta tsammanin gwamnan zai ɗauki mataimakin nasa a cikinsu.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa naɗin nasa ya bar baya da ƙura, akwai ɗaɗaɗɗun rigingimu da suka daɗe suna ci wa APC tuwo a ƙwarya, waɗanda ake tunanin samun muƙamin gwamnati zai iya ta'azzarawa.
Daga cikin manyan rigingimun da ake hasashe akwai, kamar yadda fitaccen ɗanjarida Jafaar Jafaar ya wallafa a shafinsa na Facebook:
- Murtala Sule Garo da Sanata Barau I. Jibrin
- Alhassan Rurum da Sanata Kawu Sumaila
- Abdullahi Abbas da Murtala Sule Garo
- Abdullahi T. Gwarzo da Sanata Barau I. Jibrin
- Sa'adatu Salis da Ado Doguwa
A wani faifan bidiyo da yake ta yawo a kafofin sadarwa, an ji Sanata Kawu Sumaila yana cewa akwai falle ɗaya mai albarka, inda ya yi nuni da cewa ko sau ɗaya ya yi, yana godiya ga Allah.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara raɗe-raɗin cewa ɗanmajalisar wakilai, Kabiru Alhassa Rurum na shirin shiga takarar sanatan ta Kano ta Kudu domin fafatawa da Sanata Kawu domin samun tikicin APC.
A wata rigimar daban, an sha ganin yadda ake musayar yawu musamman a tsakanin shugabar ƙaramar hukumar Tudun-Wada, Sa'adatu Salis da ɗanmajalisa mai wakiltar Tudun-Wada da Doguwa Ado Doguwa.
A ɓangaren ta Arewa, tuni wasu matasa suka fara ƙaddamar da yaƙin neman Abdullahi T. Gwarzo ya tsaya takarar sanatan yankin domin fafatawa da Sanata Barau I. Jibrin.
Asali Sanata Barau yunƙurin shiga takarar gwamna a APC ya yi, inda tun a lokacin rikicin cikin gida a APCn ya fara fitowa, amma da komawar Gwamna Abba Kabir Yusuf, sai ya zama shi ne kan gaba wajen samun tikitin APC a jihar.
Wannan ya sa Sanata Barau ya koma shirye-shiryen tsayawa kujerarsa ta sanata, amma sai aka fara tunanin T. Gwarzo shi ma ya shirya shiga takarar kujerar sanata da arewa.
Rigingimun za su shafi jam'iyyar?
Shi dai Murtala Sule Garo yana cikin tsagin waɗanda ake kira da 'ƴan tsohuwar APC' a Kano, sannan na hannun damar tsohon gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje ne.
Ya kasance ɗaya daga cikin kwamishinoni masu faɗa a ji a zamanin mulkin Ganduje, inda ya jagoranci ma'aikatar ƙananan hukumomi.
Wannan ya sa wasu suke zargin wataƙila zamansa mataimakin gwamna ba zai yi wa wasu daga cikin ƴan ɓangaren Sanata Barau. Jibrin ba, da kuma wasu ɓangarorin da suka fito a lokacin da ake maganar mataimakin gwamna.
Dr Kabiru Sufi, masanin harkokin siyasa ne a Najeriya ya ce ana zaton naɗin ya zama sanadiyar ɗinke ɓarakar da ke cikin jam'iyyar.
"Bayan an ba shi ba a ga turjiya ba sosai, amma dai samun haɗakar na cikin ababen da suka kamata a lura a daidaita su, ka ga kafin a ba shi an samu turjiya daga wani wani ɓangaren musamman Abdullahi Abbas wanda wani daban ya so."
Sufi ya ce akwai buƙatar samar da daidaito duk da cewa ba a samu tayar da jijiyar wuya ba an sanar da shi, sai dai ya ƙara da cewa akwai buƙatar su haɗa kai su yi aiki tare.
A game da matsalar da ake hangowa bayan zaɓen fitar da ƴantakara, masanin siyasar ya ce za a iya rage matsalar idan aka ba kowa dama.
"Idan har uwar jam'iyyar da jiha suka yi ƙoƙarin shawo matslar da samar da daidaito da ba kowa dama. Sannan bayan an yi zaɓen cikin gida, waɗanda suka rasa ba a watsar da su ba," in ji Sufi.
Ya ƙara da cewa dole za a samu ɓaraka "saboda irin cika da tumɓatsar da jam'iyyar ta yi. Don haka ƙoƙarin da aka yi wajen rage matsalar ne yake da muhimmanci," in ji Sufi.
A ɓangaren sabuwa da tsohuwar APC, Sufi ya ce abin da ya bayyana shi ne za su iya aiki tare.
"Ganin yadda aka fitar da mataimakin gwamna akwai alamar za su iya ajiye bambancinsu su yi aiki tare duk da a kan samu wasu matsaloli da ba a rasa ba. Amma ana buƙatar jajircewa musamman daga ɓangaren shugabanni domin samun nasarar haka," in ji shi.
Asarar muƙamai saboda bambancin siyasa
A watan Agustan 2023 ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cire sunan Maryam Shetty daga Kano, a matsayin wadda za a naɗa kan muƙamin minista, inda ya maye ta da sunayen mutum biyu.
Wani ɗan jihar Kano da ya ga samu ya ga rashi sakamakon rikicin siyasa shi ne tsohon ƙaramin ministan gidaje, Abdullahi T. Gwarzo wanda bai daɗe ba aka cire shi daga ministan a 2024.
Abdullahi Tijjani Gwarzo ya ce ya yi mamakin sauke shi da a aka yi daga muƙaminsa.
Yayin wata hira da BBC kwanaki bayan sauke shi , T Gwarzo ya ce babu wani laifi da ya yi, wanda ya janyo aka sauke shi daga muƙamin nasa, saboda a cewarsa ya yi iya baƙin ƙoƙarinsa a muƙamin da aka ba shi.
Wata kujerar da jihar Kano ta rasa baki ɗaya ita ce ta shugabancin hukumar da ke sa ido kan harkar wutar lantarki wato NERC sakamakon rikicin siyasa da ƴan jihar da dama suke zargi.