"Me ya sa aka umarci jarumin Bollywood Imran Khan ya bar Indiya?"

Cimraan Khan
Bayanan hoto, A ranar 10 ga Oktoba, 'yan sanda sun tsare Imran Khan na ɗan lokaci yayin da yake halartar wata zanga-zanga da aka gudanar a Mumbai.
    • Marubuci, Meryl Sebastian
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Mahukuntan Indiya sun umarci fitaccen taurarom Bollywood, Imran Khan, da ya bar ƙasar kafin ranar 28 ga Oktoba, bayan da ya halarci wata zanga-zanga da ke kira da a yi gyara ga tsarin zaɓe.

A wata sanarwa da 'yan sandan Indiya suka fitar a ranar Alhamis, sun ce Imran Khan ya shiga zanga-zangar da aka gudanar a August Kranti Maidan da ke Mumbai, inda masu zanga-zangar suka buƙaci shugaban Hukumar Zaɓe ta Indiya, Gyanesh Kumar, ya yi murabus.

A cewar 'yan sandan, Imran Khan ya halarci zanga-zangar ne duk da cewa ba ɗan ƙasar Indiya ba ne.

Imran Khan ɗan ne ga fitaccen jarumin Bollywood Aamir Khan. Yana da shaidar zama ɗan ƙasar Amurka kuma yana riƙe da katin zama dan India shi ma.

Katin OCI yana bai wa mutanen da suka fito daga asalin Indiya damar shiga da zama a ƙasar, amma ba ya ba su damar kaɗa ƙuri'a ko tsayawa takara a zaɓe.

'Yan sandan Indiya sun ce ofishin kula da 'yan kasashen waje ya aika wa Imran Khan takardar sanarwa, inda ake zarginsa da karya dokokin da suka shafi 'yan ƙasashen waje bayan da ya shiga zanga-zangar.

Jarumin, wanda ya shahara bayan fitowarsa a fim ɗin soyayya na shekarar 2008 mai suna "Jaane Tu... Ya Jaane Na", har yanzu bai fitar da wani martani ba game da sanarwar da aka aika masa.

Khan
Bayanan hoto, Imran Khan ya kuma wallafa wani hoto a shafinsa na Instagram, wanda ke nuna shi a cikin motar da ake jigilar fursunoni, bayan an tsare shi na ɗan lokaci yayin zanga-zangar da aka gudanar a Mumbai.

Imran Khan ya fara fitowa a fina-finai tun yana ƙarami, inda ya taka rawa a manyan fina-finan Bollywood masu farin jini kamar Qayamat Se Qayamat Tak (1988) da Jo Jeeta Wohi Sikandar (1992).

Bayan ya fara fitowa a matsayin babban jarumi a shekarar 2008, ya samu karɓuwa sosai ta hanyar fina-finai masu nasara kamar I Hate Luv Storys, Mere Brother Ki Dulhan, da Delhi Belly.

Wannan sabuwar sanarwar da hukumomin Indiya suka aika masa na zuwa ne a lokacin da Imran Khan ke shirin komawa harkar fim a wannan shekara bayan ya shafe fiye da shekaru goma baya fitowa sosai a masana'antar.

Ana sa ran dawowarsa za ta fara ne da fim ɗin Netflix mai suna Adhoore Hum Adhoore Tum, wanda ya jawo hankalin masoya fina-finan Bollywood da dama da ke jiran sake ganin sa a majigi.

"Da alama ana bibiya ta"

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jarumin Bollywood Imran Khan ya halarci wata zanga-zanga da jam'iyyar Cockroach Janta Party (CJP) ta shirya a ranar 10 ga Oktoba. Zanga-zangar na daga cikin wani gagarumin yunkuri da matasan Gen Z suka jagoranta, inda suka shafe kwanaki suna gudanar da zanga-zanga domin neman a yi gyara ga tsarin zaɓe tare da neman shugaban Hukumar Zaɓe ta Indiya ya yi murabus.

Masu zanga-zangar sun yi ikirarin cewa an samu kura-kurai da magudin zaɓe a tsarin kaɗa ƙuri'a. Sai dai Hukumar Zaɓe ta Indiya ta yi watsi da waɗannan zarge-zarge, tana mai cewa babu hujjojin da ke tabbatar da zarge-zargen.

Korafin da ya jawo bincike kan Imran Khan ya fito ne daga Kirit Somaiya, wani jigo a jam'iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) mai mulki, wadda ke jagorantar gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jiha inda lamarin ya faru.

Somaiya ya zargi tauraron na Bollywood da shiga cikin abin da ya bayyana a matsayin wata "makarkashiya da nufin tayar da rikici da hargitsi a cikin Indiya."

Lamarin ya ƙara jawo cece-kuce ne saboda Imran Khan ba ɗan ƙasar Indiya ba ne, duk da cewa yana da katin OCI (Overseas Citizen of India) da ke ba shi damar shiga da zama a ƙasar. Hukumomi na zarginsa da karya dokokin da suka shafi 'yan ƙasashen waje ta hanyar shiga harkokin siyasar cikin gida.

Wannan cece-kucen na zuwa ne a daidai lokacin da Imran Khan ke shirin komawa harkar fim bayan dogon lokaci, inda ake sa ran zai dawo ta fim ɗin Netflix mai suna "Adhoore Hum Adhoore Tum."

Jarumin Bollywood Imran Khan bai mayar da martani kai tsaye ga zarge-zargen da Kirit Somaiya ya yi masa ba, amma ya bayyana wa manema labarai dalilin da ya sa ya halarci zanga-zangar.

Ya ce "Ba ni da wata buƙata ta musamman. Na zo nan ne a matsayin ɗan ƙasa kuma mutum da ke zaune a wannan birni. Na zo ne domin ganin dalilin da ya sa ake takaita wa mutane 'yancin zirga-zirga da kuma hana a ji muryoyinsu."

Ya kuma jaddada cewa bai halarci zanga-zangar a madadin wata ƙungiya ko jam'iyya ba, illa dai a matsayinsa na mutum mai sha'awar abin da ke faruwa a cikin al'umma.

Bayan zanga-zangar, 'yan sanda sun tsare Imran Khan na ɗan lokaci tare da sauran masu zanga-zangar. Daga baya ya wallafa wani hoto a shafinsa na Instagram, wanda aka ɗauka a cikin motar 'yan sanda da ake jigilar waɗanda aka tsare.

Ya sanya wa hoton taken: "Ina ganin ana yawo da ni ne kawai ana ɗana ni a mota."

Wannan magana ta kasance cikin salon barkwanci, domin a Turanci kalmar "being taken for a ride" na iya nufin ana kai mutum wani yawo ba tare da ya shirya ba. A nan Imran Khan ya yi amfani da kalmar ne cikin raha yana nuni da yadda 'yan sanda ke kai shi yayin da yake tsare.

Cimraan Khan

Sakon da Imran Khan ya wallafa a shafinsa na sada zumunta mutane sun danna masa alamar so fiye da miliyan biyu (likes).

A ƙarshen makon da ya gabata, bayan kiran da jam'iyyar Cockroach Janta Party (CJP) ta yi, dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a Delhi, Mumbai da sauran biranen Indiya, suna neman shugaban Hukumar Zaɓe ta Indiya, Gyanesh Kumar, ya yi murabus kafin muhimman zaɓukan jihohi masu zuwa.

A ranar Litinin, ɗan majalisar dokoki na jam'iyyar Congress, Rahul Gandhi, tare da wasu manyan shugabannin jam'iyyun adawa, sun jagoranci dubban masu zanga-zanga a wani tattaki daga Connaught Place zuwa Kotun Koli ta Indiya, domin nuna goyon baya ga buƙatar yin gyaran tsarin zaɓe.

A ranar Laraba, an tura manyan shugabanni biyu na CJP zuwa tsarewar kotu na tsawon kwanaki biyar bayan an zarge su da shiga wani wurin zanga-zanga a Delhi ba tare da izini ba.

Haka kuma, jam'iyyar CJP ta sanar da shirin sake gudanar da wata zanga-zanga a babban birnin ƙasar, Delhi, a yammacin ranar Juma'a.

Waɗannan abubuwa na nuni da cewa rikicin siyasar da ya shafi zarge-zargen magudin zaɓe da kuma buƙatar sauye-sauye a tsarin zaɓen Indiya na ci gaba da ɗaukar hankali, yayin da gwamnati, 'yan adawa da masu zanga-zanga ke ci gaba da musayar ra'ayi kan batun.