KAI TSAYE, Zan sake buga fenariti idan dama ta samu a Champions League - Gabriel

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin kai tsaye a BBC Hausa daga 11 zuwa 18 ga watan Oktoban 2026.

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. Teburin Champions League daga farko zuwa yan tsakiya, Champions League

    Champions League
  2. Teburin Champions League daga tsakiya zuwa karshe, Champions League

    Champions League
  3. Wasannin Champions League ranar Talata da Laraba, Champions League

    Ranar Talata 13 ga watan Oktoba

    • Lens v Sporting
    • Sabah FK v Slavia Prague
    • Arsenal v Lille
    • Atletico Madrid v Man Utd
    • Galatasaray v Barcelona
    • Inter Milan v Club Brugge
    • RB Leipzig v PSV Eindhoven
    • Viking v Bayern Munich
    • Villarreal v Napoli

    Ranar Laraba 14 ga watan Oktoba

    • Feyenoord v Como
    • LASK v Liverpool
    • Aston Villa v Fenerbahce
    • Bodo/Glimt v Borussia Dortmund
    • Man City v Paris St-Germain
    • Real Betis v Porto
    • Roma v Real Madrid
    • Shakhtar Donetsk v AEK Athens
    • Slovan Bratislava v Stuttgart
    Champions League
  4. Me ya faru da Hincapie da Zubimendi?, Arsenal da Lille

    An shiga damuwa kan lafiyar mai tsaron bayan tawagar Ecuador, Piero Hincapie, bayan da aka dauke shi bayan kammala atisayen shirya fuskantar Lille a Champions League.

    Har yanzu ba a tabbatar da girman raunin da Hincapie ya samu ba, amma an gan shi yana rike da idon kafarsa na dama yayin da golan kungiyar, Illan Meslier, ke taimaka masa fita daga fili.

    Hincapie ya koma kungiyar a matsayin cikakken dan wasa a wannan bazarar, bayan ya shafe kakar da ta gabata a wasannin aro daga Bayer Leverkusen.

    Tun farkon kakar wasa ta bana, mai tsaron bayan ya sha fama da matsalolin raunin tsoka, kuma yanzu yana jiran sakamakon gwaje-gwaje domin a tantance ko zai sake shafe wani lokaci yana jinya.

    A gefe guda kuma, kocin Arsenal Mikel Arteta ya bayyana cewa dan wasan tsakiyar kungiyar, Martin Zubimendi, shi ma ya samu rauni ne a lokacin atisaye.

    Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken bayani game da irin raunin da Zubimendi ya samu ko kuma tsawon lokacin da zai yi ba tare da buga wasa ba.

    Wannan na nufin Arsenal na fuskantar fargabar rasa wasu muhimman 'yan wasa gabanin wasan Champions League da Lille da kuma sauran muhimman wasannin da ke tafe.

    Arsenal
  5. Maresca ya ci wasa shida a jere a jere a Man City da fara Premier ta bana, Manchester City

    Kocin Manchester City, Enzo Maresca, ya fara jan ragamar kungiyar Etihad da rashin nasara 3-0 a hannun Arsenal Community Shield kan fara kakar bana, amma tun daga wannan lokaci ya jagoranci City zuwa nasara takwas a jere a dukkan fafatawa har da shida a Premier League.

    City yanzu tana jan ragamar teburin Premier League da tazarar maki uku a saman Arsenal mai rike da kofin gasar, bayan da ta lashe wasanninta shida na farko a jere.

    Baya ga haka, kungiyar ta kai zagayen 'yan 16 a gasar Carabao Cup bayan nasara da ta samu a gida a kan Norwich City mai buga Championship.

    Haka kuma, Manchester City tana matsayi na takwas a teburin gasar Champions League bayan da ta doke Porto da ci 2-0 a wasan farko a cikin rukuni.

    Wannan fara kakar da hawa kan ganiya ya kara karfafa matsayin Maresca a matsayin magajin Pep Guardiola, yayin da City ke ci gaba da nuna karfinta duk da kalubalen da take fuskanta kan tumarta da ake yi.

    Enzo Maresca
  6. Gabriel: Zan sake buga fenariti idan dama ta samu a Champions League, Arsenal

    Mai tsaron bayan Arsenal, Gabriel, ya bayyana cewa a shirye yake ya sake daukar nauyin bugun fenariti a gasar Champions League, duk da cewa ya kasa cin kwallon da ta kai Arsenal ta yi rashin nasara a wasan karshe a kakar da aka kammala da Paris St Germain.

    Burin Arsenal na lashe kofin zakarun Turai karo na farko a tarihinta ya rushe ne bayan Gabriel ya buga fenaritin da ya tashi sama ta yi waje, bayan kammala wasa da Paris Saint-Germain (PSG) da ci 1-1.

    Sai dai, yayin da yake magana gabanin wasan da Arsenal za ta karbi bakuncin Lille, Gabriel ya ce abin da ya faru a Budapest bai sa ya ji tsoron sake daukar wannan nauyi ba.

    Arsenal ta kai wasan karshe a Champions League a karon farko cikin shekaru 20 a kakar da ta gabata, amma ta kasa lashe kofin bayan rashin nasara a hannun PSG.

    A kakar bana kuma, kungiyar ta fara kamfen din da nasarar 1-0 a gidan Napoli.

    Kungiyar Mikel Arteta za ta karbi bakuncin Lille a filin Emirates Stadium ranar Talata, kafin ta ziyarci Bayern Munich a mako mai zuwa a wani wasan da ake sa ran zai dauki hankali.

    Ana kallon Arsenal a matsayin daya daga cikin kungiyoyin da ke da karfin lashe gasar ta bana.

    Gabriel mai shekara 28 ya ce kungiyar na cike da karsashi da kwarin gwiwa.

    Gebriel
  7. Har yaushe daukaka karar Manchester City za ta dauka?, Manchester City

    Za a saurari daukaka karar da Manchester City ta shigar ne a wani zaman sirri gaban sabon kwamitin bincike mai zaman kansa da ya kunshi mutane uku, wadanda dukkansu kwararru ne a fannin shari'a.

    A karkashin wani sashe na dokokin Premier League, an tanadi cewa ya kamata a kammala sauraron daukaka kara cikin makonni 12 daga ranar da aka fara sauraronta, sannan a sanar da hukunci cikin kwanaki 30 bayan kammala aikin.

    Idan aka kirga daga ranar 1 ga Oktoba, ranar da Manchester City ta ce ta shigar da daukaka karar, cikar makonni 12 zai kasance ne a ranar 24 ga Disamba.

    Sai dai kuma dokokin sun ba da damar tsawaita wannan wa'adi idan an ga akwai bukatar hakan. Saboda haka, har yanzu ba a san takamaiman lokacin da za a kammala dukkan tsarin ba.

    An saka wannan tanadi cikin kundin dokokin Premier League ne a wannan bazarar da ta gabata.

    Abubuwan da suka faru a irin wadannan shari'o'i a baya sun nuna cewa duk wani hukunci da za a dauka kan Manchester City zai fi yiwuwa ya jira sai an kammala daukaka karar. Sai dai babu tabbacin cewa haka ne zai faru a wannan karon.

    Haka kuma, akwai yiwuwar bayan an yanke hukunci kan daukaka karar a sake samun wata sabuwar daukaka kara dangane da duk wani hukunci da aka kakabawa kungiyar din.

    Wannan na nufin cewa batun na iya daukar lokaci mai tsawo kafin a samu hukunci na karshe game da makomar Manchester City da duk wani matakin ladabtarwa da za a dauka a kanta.

    Manchester City
  8. "Mun yarda da Khaldoon" - Magoya bayan Man City sun mayar da martani da tasu tutocin, Liverpool 0-3 Manchester City

    Magoya bayan Manchester City sun mayar da martani ga magoyan Liverpool a Anfield ta hanyar daga tutoci da sakonnin goyon baya ga kungiyarsu.

    A yayin wasan, wasu magoya bayan City sun rika daga ayaba a matsayin nuna rashin amincewa da abin da magoya masu masaukin baki suke yi musu, tare da daga manyan tutoci dauke da sakonni daban-daban.

    Daga cikin sakonnin da aka gani akwai:

    "Mun yarda da Khaldoon"

    wato nuna cikakken goyon baya ga shugaban kungiyar, Khaldoon Al Mubarak.

    Sauran sakonnin sun hada da:

    "Ba mu da laifi"

    Wannan sako na nuni ne ga tarihin Manchester City da hawan da ta yi daga matakan baya na kwallon kafa zuwa zama daya daga cikin manyan kungiyoyin duniya, tun bayan da ta lashe wasan neman zuwa babbar rukunin gasar a shekarar 1999.

    Martanin magoya bayan City ya zo ne bayan da magoya bayan Liverpool suka cika Anfield da sakonnin suka da zarge-zargen da suka shafi tuhumar da aka samu City din da laifin karya wasu dokokin kudi na Premier League.

    Lamarin ya kara zafafa yanayin wasan, wanda ya kasance cike da hayaniya da musayar sakonni tsakanin magoya bayan kungiyoyin biyu, kafin daga bisani Manchester City ta yi nasara da ci 3-0.

    Liverpool
    Liverpool
    Liverpool
    Liverpool
  9. Kyallayen da magoya bayan Liverpool suka nuna, Liverpool 0-3 Man City

    Man City
    Man City
    Man City
    Man City
    Man City
    Man City
  10. Magoya bayan Liverpool sun bayyana ra'ayinsu kafin wasan Man City, Liverpool 0-3 Manchester City

    Magoya bayan Liverpool sun bayyana ra'ayinsu karara kafin fara wasa da kuma yayin fafatawar Premier League ranar Lahadi, inda suka rika yi wa Manchester City kirari da kalmar "masu magudi" a filin Anfield.

    An fara wasan cikin yanayi mai zafi kamar yadda aka yi tsammani, yayin da bangaren magoya bayan Liverpool ya rika yi wa City habaici kana samun ta da laifin karya dokokin kudi.

    Magoya bayan sun daga manyan alluna dauke da sakonni irin su:

    "An yaudari kungiyoyi da magoya baya."

    Haka kuma, hatta kyallen da ke dauke da Liverpool da Manchester City da ake sayarwa a irin wadannan manyan wasanni ya jawo hankali, bayan an lura cewa bangaren da ke dauke da launin shudi na City an rubuta masa:

    "Shamchester City - Masu Magudi."

    Lokacin da ake karanta sunayen 'yan wasan Manchester City kafin a fara wasan, sai kawai ihu kake ji ta ko ta ina daga magoya bayan masu masaukin baki da ya mamaye filin.

  11. Man City ta lashe dukkan wasa shida da fara Premier League ta bana, Premier League

    Erling Haaland

    Manchester City ta ci da taka leda a karon farko ga gagarumar nasarar doke Liverpool a Anfield ranar Lahadi, bayan da aka sameta da laifin karya dokokin kudi na Premier League.

    Kungiyar karkashin jagorancin Enzo Maresca ta sake bayar da tazarar maki uku a saman teburin gasar Premier League. Duk da haka, har yanzu akwai rashin tabbas kan makomar kakar wasanta yayin da take jiran hukuncin da za a yanke mata, wanda zai iya hadawa da korar kungiyar daga Premier League ko kuma cire mata maki masu yawa ko a hada biyu da sauransu.

    Manchester City ta fuskanci kalubale a wasan, kafin daga bisani ta mamaye Liverpool, wadda ta karasa fafatawar da 'yan wasa 10 bayan da aka bai wa Ryan Gravenberch jan kati.

    Erling Haaland ne ya fara bude cin kwallo a minti na 65, Jeremy Doku, ya kara ta biyu bayan mintuna uku kacal tsakani, sannan Rayan Cherki ya ci ta ukun.

    Sakamakon ya kara karfafa matsayin Manchester City a saman teburin gasar, yayin da Liverpool ta fuskanci koma baya a yunkurinta na ci gaba da takarar kofin Premier League na kakar nan.

  12. Wasa nawa za a dakatar da Vinicius, bayan jan kati, Real Madrid 1-0 Villareal

    Dan wasan Real Madrid Vinicius Jr ya nemi afuwar abokan wasansa da kuma magoya bayan Real Madrid, bayan da aka ba shi jan kati a wasan da suka doke Villarreal da ci 1-0 a gasar La Liga a filin Santiago Bernabeu ranar Asabar.

    Yanzu Vinicius na jiran hukuncin kwamitin ladabtarwa, wanda zai iya sa ya rasa babbar karawar da Real Madrid za ta yi da abokiyar hamayyarta Barcelona a ranar 25 ga Oktoba a filin Camp Nou.

    Dan wasan na Brazil ya ci wa Real Madrid kwallo ta biyu, amma alkalin wasa ya soke ta bayan duba bidiyo (VAR), inda aka gano cewa ya kamata a kore shi saboda ja wa Nathan Saliba gashi a lokacin da aka kai harin da ya kai ga kwallon.

    Bayan kammala wasan, Vinicius wanda ya shiga fafatawar a minti na 52 kafin a kore shi, ya wallafa sako a kafafen sada zumunta yana cewa:

    "Ina ba kungiya da magoya baya hakuri."

    Dokokin Hukumar Kwallon Kafa na Sifaniya sun tanadi cewa jan gashin abokin hamayya ana daukarsa a matsayin mummunan hali na tashin da'a a filin wasa.

    A karkashin Mataki na 130 na dokokin ladabtarwa, hukuncin irin wannan laifi idan bai jawo rauni ga abokin hamayya ba shi ne dakatar da dan wasa daga wasa daya zuwa uku.

    Wasanni uku masu zuwa na Real Madrid a La Liga za su kasance da Sevilla da Barcelona da kuma Racing Santander.

    Sai dai rasa damar buga El Clasico da Barcelona zai zama babban koma baya ga Vinicius mai shekaru 26, wanda ke cikin manyan taurarin kungiyar da kuma tawagar kasar Brazil.

    Vinicius Junior
  13. Wasa ya ƙare Manchester City ta samu maki uku

    .

    Manchester City ta haɗa maki uku a Anfield, ta hannun 'yan wasanta uku.

    Haaland ne ya fara zuwa kwallo a wasan a mintina na 65 da fara wasan, bayan jan kantin da aka bai wa ɗan wasan tsakiya na Liverpool ɗin Gravenberch a mintina na 52.

    Mintina uku da cin kwallon Haaland shi ma ɗan wasa Duko da ya shiga wasan a canji ya ci wa City kwallo ta biyu a wasan, wanda ya ƙara tabbatar da nasarar City a Anfield.

    A mintina na 78 wato mintina 10 bayan kwallo ta biyu da Manchester City ta samu, Rayan Cherki ya ci wata kwallo mai cike da birgewa da kuma mamaki, wanda da ita ne kuma aka cike lissafin kwallo uku da City ta yi nasara da su.

    Magoya bayan Liverpool sun yi ta waƙe suna cewa "City ta saba cuta" tun daga farkon wasan har zuwa lokacin da aka tashi.

    Ƙididdigar kamfanin nan da ke samar da bayanan kwallon ƙafa na OptaJoe, ta ce an tafka laifuffuka (fouls) 18 a rabin farko na wasan tsakanin Liverpool (10) da Manchester City (8), wanda shi ne mafi yawan adadin laifuffuka a rabin farko na wasan Premier League da aka buga a Anfield tun lokacin wasan Liverpool da Arsenal a watan Nuwamban 2021, wanda shi ma aka tafka laifuffuka 18.

    Wannan ƙididdigar na nuna irin tsananin fafatawar da aka yi a wasan tun daga farko, inda 'yan wasan ɓangarorin biyu suka rika yin ƙalubale masu ƙarfi da kuma kokarin hana juna samun sarari.

    Hakan ma ya bayyana a wasu lokutan wasan, ciki har da takaddamar da ta taso tsakanin Alexis Mac Allister da Elliot Anderson, da kuma katunan gargadi da aka bai wa 'yan wasa, kafin daga bisani Ryan Gravenberch ya samu jan kati sakamakon katin gargadi na biyu.

    'Yan wasan Liverpool sun karaya gaba ɗaya kuma sun sunkuyar da kawunansu ƙasa.

    A gefe guda kuma, akwai babban murmushi a fuskar Enzo Maresca. Ya ji daɗin wannan bajintar da ƙungiyarsa ta nuna.

    Wannan ce rashin nasara ta farko ga Andoni Iraola a kowace gasa, kuma abin mamaki, wakar da magoya bayan Liverpool ke yi wa kungiyar da ke saman teburin gasar ita ce: "Za ku sauka, za ku sauka.".

  14. An ƙara bai wa Liverpool katin gargaɗi, Liverpool 0-3 Man City

    Virgil van Dijk ya samu katin gargadi a ƙarshen wasan bayan wani ƙalubale da bai dace da lokaci ba kan Rayan Cherki, wanda ke da matuƙar sauri da motsi a fili.

    Kyaftin ɗin na Liverpool ya yi ƙoƙarin dakatar da harin Cherki, amma ya makara wajen shiga ƙalubalen, lamarin da ya sa alkalin wasa ya nuna masa katin rawaya.

    Wannan ya ƙara nuna irin matsalolin da Cherki ya jefa tsaron Liverpool a ciki a rabin na biyu na wasan. Saurinsa, dabararsa da motsinsa tsakanin layukan wasa sun sa masu tsaron Liverpool suka sha wahala wajen dakatar da shi ba tare da yin kuskure ba.

    Van Dijk ya zaɓi ya aikata laifin ne domin hana wani harin mai haɗari, amma hakan ya zo da sakamakon samun katin gargadi.

  15. , Liverpool 0-3 Man City

    Manchester City na kan gaba da tazarar ƙwallaye uku, kuma suna dab da ɗora maki uku a saman teburin gasar.

    Ko da City ta ci gaba da tara maki kuma ta jagoranci teburin gasar, takaddamar da ke kewaye da kulob ɗin a wajen fili na nufin akwai rashin tabbas game da abin da zai faru nan gaba.

    Wannan rashin tabbas ba ya amfani ga kowa. Ba ya amfani ga Manchester City, ba ya amfani ga abokan hamayyarta, kuma ba ya amfani ga magoya bayan ƙwallon ƙafa gaba ɗaya.

    A filin wasa, City na nuna ƙarfi kuma tana samun sakamako. Amma har sai an samu cikakken bayani kan abubuwan da ke faruwa a wajen fili, za a ci gaba da samun tambayoyi kan yadda za a fassara waɗannan nasarori da matsayinsu a teburin gasar

  16. Bayanan OptaJoe

    18 - An tafka laifuffuka 18 a mintina 45 na farko na wasan tsakanin Liverpool (10) da Manchester City (8), wanda shi ne mafi yawan adadin laifuffuka a mintina 45 na farko na wasan Premier League da aka buga a Anfield tun lokacin wasan Liverpool da Arsenal a watan Nuwamban 2021, wanda shi ma aka tafka laifuffuka 18.

    Wannan ƙididdigar na nuna irin tsananin fafatawar da aka yi a wasan tun daga farko, inda 'yan wasan ɓangarorin biyu suka rika yin ƙalubale masu ƙarfi da kuma kokarin hana juna samun sarari.

    Hakan ma ya bayyana a wasu lokutan wasan, ciki har da takaddamar da ta taso tsakanin Alexis Mac Allister da Elliot Anderson, da kuma katunan gargadi da aka bai wa 'yan wasa, kafin daga bisani Ryan Gravenberch ya samu jan kati sakamakon katin gargadi na biyu.

  17. Cherki ɗan wasan fita kunya, Ra'ayi - Jamie Carragher

    Za mu iya magana kan Manchester City, yawan kuɗin da ta kashe wajen sayen 'yan wasa, ko kuma muhawarar ko an yi hakan bisa ƙa'ida ko a'a. Amma Rayan Cherki na ɗaya daga cikin 'yan wasa masu matuƙar inganci.

    Tun lokacin da ya iso kulob ɗin, ya nuna cewa yana da ƙwarewa ta musamman. Yana da hangen nesa, iya sarrafa ƙwallo da kuma basirar ƙirƙirar damammaki da ke bambanta shi da sauran 'yan wasa.

    Amma game da Jeremie Frimpong, abin da ya fi alheri shi ne kada a yi magana sosai a kansa. Ya kasance ba shi da daidaito a wasan, yana yawan fita daga matsayinsa kuma hakan ya sa ya yi kama da wanda ke yawo a ko'ina cikin fili ba tare da cikakken tasiri ba.

    A gefe guda, Cherki ya nuna kwanciyar hankali da inganci a lokutan da suka fi muhimmanci, kuma ya kasance ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka sa Manchester City ta samu nasara a wannan wasan.

  18. Labarai da dumi-dumi, GOAL - Liverpool 0-3 Man City, Rayan Cherki

    ,

    Elliot Anderson ya aika da ƙwallo zuwa ga Rayan Cherki, wanda ya bari ta wuce tsakaninsa da ƙafafunsa zuwa ga Josko Gvardiol. Daga nan kuma Cherki ya juya cikin sauri ya shiga cikin akwatin bugun fenariti domin karɓar ƙwallon da abokin wasansa ya mayar masa.

    Sai ya zura ƙwallon cikin nutsuwa ta wuce Alisson zuwa cikin raga.

    A wannan lokaci, za a iya cewa an gama da wasan, idan har ba a riga an gama ba.

    Manchester City ta nuna ƙwarewa da fahimtar juna a wannan harin, inda motsi da musayar ƙwallo tsakanin 'yan wasan suka tarwatsa tsaron Liverpool. Cherki ya nuna hazaƙa da natsuwa wajen kammala harin, yayin da Gvardiol ya taka muhimmiyar rawa a ginin ƙwallon.

    City na da cikakken iko a wasan yanzu, kuma Liverpool za ta buƙaci mu'ujiza idan tana son dawowa daga wannan yanayi.

  19. Labarai da dumi-dumi, GOAL - Liverpool 0-2 Man City, Jeremy Doku

    Bayan rawar da ya taka wajen bai wa Erling Haaland ƙwallar farko, ɗan wasan Belgium ɗin ya sake nuna bajinta. An ba shi sarari ya kutsa ciki daga gefe, sannan ya mayar da ƙwallon kan ƙafarsa ta dama kafin ya saki wani gagarumin harbi mai karkata wanda ya shiga saman kusurwar raga.

    Wannan ƙwallo ce ta musamman matuƙa.

    Mai tsaron gida bai da wata dama ta tare ta saboda yadda aka harba ta da ƙarfi da kuma daidaito. Doku ya nuna ƙwarewa, sauri da kwarin gwiwa a lokacin da ƙungiyarsa ta fi buƙatar hakan.

    A yanzu haka, Manchester City tana da cikakken iko a wasan, kuma tasirin Doku yana fitowa fili kasancewar ya taka muhimmiyar rawa a duka ƙwallayen biyu. Magoya bayan City kuwa za su yi farin ciki sosai da yadda ya canza alkiblar wasan cikin ɗan lokaci kaɗan.

  20. Jan kati ga Ryan Gravenberch

    .

    An kori Ryan Gravenberch bayan ya samu katin gargadi na biyu, kuma da wuya ya samu hujjar yin ƙorafi kan hukuncin.

    Wannan wani babban sauyi ne a wasan.

    Liverpool za ta buga sauran lokacin wasan da 'yan wasa 10 kawai, lamarin da zai ƙara musu wahala wajen tinkarar matsin lambar Manchester City.

    Ga City, wannan wata babbar dama ce ta ƙara matsawa gaba da neman ƙwallar nasara, musamman idan suka yi amfani da ƙarin ɗan wasan da suke da shi a fili.

    A yanzu, dukkan idanu za su koma kan yadda Liverpool za ta kare kanta da kuma ko Manchester City za ta iya amfani da wannan gagarumar dama.