Wace ce Ilhan Omar kuma me ya sa take takun-saƙa da Trump?

Asalin hoton, Getty Images
Jami'an shige da fice na Amurka sun gudanar da bincike a gidan Ilhan Omar, 'yar Majalisar Wakilan Amurka mai wakiltar jihar Minnesota, a wani ɓangare na binciken laifuka.
Wani kakakin Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ya ce jami'an sashen binciken tsaron cikin gida (HSI) sun aiwatar da "umarnin binciken gida da kotu ta amince da shi" a wani gida da ke yankin Washington DC.
Kakakin ya ce matakin na daga cikin "binciken laifuka da gwamnatin tarayya ke ci gaba da gudanarwa", amma bai bayar da ƙarin bayani ba.
A halin yanzu, Majalisar Dokokin Amurka tana hutu, kuma ba a san ko Madam Omar tana gidan a lokacin da aka gudanar da binciken ba.
Madam Omar, 'yar Jam'iyyar Democrat kuma fitacciyar mai sukar Shugaba Donald Trump, ta bayyana binciken da ake yi kanta a shafukan sada zumunta a matsayin "ƙoƙarin kai hari ga abokan hamayyar siyasa da kuma amfani da jami'an tsaro na tarayya a matsayin makamin siyasa".
"Tsawon shekaru goma, Trump yana kai mini hari ta hanyar yaɗa ƙaryace-ƙaryace marasa tushe da kamfen na ɓata suna," in ji Madam Omar a saƙon da ta wallafa.
"Wannan shi ne sabon mataki na tsananta kamfen ɗinsa na tsoratar da abokan hamayyar siyasa. Ba zan yi shiru ba,"in ji ta.
Da yake magana da manema labarai a ranar Litinin, Trump ya ce ba shi da "wata alaƙa ko kaɗan" da binciken da Ma'aikatar Shari'a ke gudanarwa kan Madam Omar. Sai dai ya bayyana ta a matsayin mai yawan korafi da kuma "muguwar mutum".
Da yake magana kan 'yar majalisar, wadda aka haifa a Somaliya, shugaban na Jam'iyyar Republican ya ce: "Ta fito ne daga wata ƙasa da ba ƙasa ba ce."
Wace ce Ilhan Omar?

Asalin hoton, EPA
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An haifi Ilhan Omar a birnin Mogadishu, babban birnin Somaliya, a shekarar 1981. Ita ce auta a cikin yara bakwai na iyalinsu. Mahaifiyarta ta rasu lokacin da take da shekara biyu kacal.
Mahaifinta da kakanta ne suka raini Omar. Daga bisani iyalinsu suka tsere daga Somaliya sakamakon yakin basasar ƙasar, inda suka shafe shekara huɗu a wani sansanin 'yan gudun hijira a Kenya kafin su koma Amurka a shekarar 1995.
Kafin shiga siyasa, Omar ta yi aiki a fannin ilimi. Daga baya ta fara harkokinta na siyasa ta hanyar jagorantar kamfen ɗin neman zaɓen 'yan majalisar ƙananan hukumomi, sannan ta yi aiki a matsayin babbar mai ba da shawara kan manufofi ga wasu 'yan siyasa a jihar Minnesota.
A shekarar 2016, ta lashe zaɓen shiga majalisar dokokin jihar Minnesota, inda ta kayar da wani ɗan siyasa da ya shafe shekara 44 yana riƙe da kujerarsa.
A wata hira da ta yi da BBC a shekarar 2017, Omar ta ce matasa ne suka ƙarfafa mata gwiwar tsayawa takara saboda sun fi yarda da manufofinta da ra'ayoyinta da kuma abin da take tsayawa kai domin cimmawa.

Asalin hoton, EPA
Madam Ocasio-Cortez ta wallafa saƙon goyon baya ga Madam Omar a shafinta na Twitter, bayan wata mahawara mai zafi tsakaninta da wakilin musamman na Amurka kan Venezuela, Elliott Abrams, ta yaɗu sosai a kafafen sada zumunta.
A yayin zaman sauraron ra'ayoyi na kwamitin harkokin wajen Majalisar Wakilan Amurka, Madam Omar ta yi tambayoyi kan rawar da Mista Abrams ya taka a badakalar Iran-Contra, inda Amurka ta sayar wa Iran da makamai a ɓoye, sannan ta karkatar da kuɗin da aka samu zuwa ga ƙungiyoyin da ke adawa da Kwaminisanci a Nicaragua.
Ta kuma tambayi Mista Abrams kan kalaman da ya yi game da manufofin Amurka a El Salvador, ciki har da lokacin da ya yi magana kan kisan kiyashin da aka yi a garin El Mozote a shekarar 1981, inda ya bayyana kalamansa ta yadda ake ganin ya rage girman lamarin.
"Ganin yadda take yi wa wakilin Trump tambayoyi ... yana sa mutum ya ji kamar an yi adalci," in ji Madam Ocasio-Cortez.
Mista Abrams ya bayyana musayar kalaman a matsayin "abin dariya", inda ya ce ba zai mayar da martani kan abin da ya kira "hari na kashin kai" ba.
"Ba na ganin cewa duk waɗannan tambayoyin an yi su ne da niyyar neman amsoshi na gaskiya, don haka ba zan ba da amsa ba," in ji shi yayin zaman sauraron ra'ayoyin.
Me masu sukar ta ke cewa?
Sai dai duk da dimbin magoya bayanta, Madam Omar ba ta samu sauƙin fara aikinta a birnin Washington DC ba.
Ta sha shiga cikin ce-ce-ku-ce sakamakon kalaman da masu suka suka bayyana a matsayin masu nuna ƙiyayya ga Yahudawa.
A shekarar 2012, wani saƙonta da ta wallafa a shafukan sada zumunta ya sake bayyana, inda ta yi zargin cewa Isra'ila ta "yi wa duniya sihiri", lamarin da ya jawo fushin mutane da dama waɗanda suka ɗauki kalaman a matsayin cin mutunci ga al'ummar Yahudawa.
Ce-ce-ku-cen ya ƙara tsananta ne bayan ta soki kwamitin hulɗa da jama'ar Amurka da Isra'ila (AIPAC), inda ta yi zargin cewa ƙungiyar masu matsin lamba tana biyan 'yan siyasa kuɗi domin su kaɗa ƙuri'a don amincewa da manufofin da ke goyon bayan Isra'ila.
'Yan siyasa daga jam'iyyun Republican da Democrat sun yi Allah-wadai da kalamanta. Kakakin Majalisar Wakilan Amurka a lokacin, Nancy Pelosi, ta soki abin da ta kira "zarge-zargen da ke nuna son zuciya", tare da neman Madam Omar ta ba da haƙuri nan take.
Daga bisani, Madam Omar ta nemi afuwa, inda ta wallafa saƙo a Twitter tana cewa wasu abokan aikinta sun yi mata bayani kan "tarihin raɗaɗi na kalaman da ake amfani da su wajen nuna ƙiyayya ga Yahudawa".
Sai dai 'yan takarar shugabancin Amurka na Jam'iyyar Democrat a lokacin, Bernie Sanders, Kamala Harris da Elizabeth Warren, duk sun fito sun kare ta a lokacin da ce-ce-kucen ya tsananta.
Kamar takwararta, Madam Tlaib, Madam Omar ta taɓa bayyana goyon bayanta ga ƙungiyar fafutukar kaurace wa Isra'ila, janye zuba jari da kakaba mata takunkumi, wato BDS. Ƙungiyar na kira da a kaurace wa Isra'ila gaba ɗaya saboda manufofinta kan Falasɗinawa.
Sai dai ɗan jaridar bincike, Alex Kotch, wanda ya rubuta wani ra'ayi a jaridar The Guardian bayan kalaman Madam Omar, ya ce sukar da ta yi wa AIPAC da goyon bayanta ga ƙungiyar BDS suna da hujja.
"Abin da ta yi na fito da ayyukan AIPAC fili abu ne mai muhimmanci," kamar yadda ya shaida wa BBC.
Ya ce a siyasar Amurka, kusan an hana mutane sukar Isra'ila, inda ya ƙara da cewa Madam Omar tana amfani da haƙƙinta ne na sukar wata ƙungiyar masu tsauttsauran ra'ayi.

Asalin hoton, EPA
Zargin kashe kuɗin yaƙin neman zaɓe ba bisa ƙa'ida ba
Ko a lokacin da Ilham Omar ta zauna a gwamnatin jihar Minnesota ba ta tsira daga masu suka.
Steve Drazkowski, wani ɗan majalisar wakilai na jihar Minnesota, ya yi zargin cewa Madam Omar ta yi amfani da kuɗin yaƙin neman zaɓenta a zaɓen ƙananan hukumomi wajen biyan lauyanta na ƙashin kai, da kuma yin tafiye-tafiye da dama a cikin Amurka, ciki har da tafiya guda zuwa ƙasar Estonia, waɗanda ba su da alaƙa da yaƙin neman zaɓenta.
"Ba ta mutunta doka kawai," in ji Mista Drazkowski a zantawarsa da BBC.
Ɗan majalisar na Jam'iyyar Republican ya ce a yanzu haka hukumar kula da kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe ta jihar Minnesota tana gudanar da cikakken bincike kan waɗannan korafe-korafe biyu.
Sai dai kakakin hukumar ya shaida wa BBC cewa hukumar ba ta tabbatarwa ko musanta kasancewar korafe-korafe ko bincike kan irin waɗannan batutuwa.
A nata ɓangaren, Madam Omar ta shaida wa jaridar Star Tribune ta yankin cewa Mista Drazkowski yana da "tsananin son sanin abubuwan da ke cikin fayilolina, har ya kai ga rashin hankali".
A lokacin, tawagar yaƙin neman zaɓenta ta ce zarge-zargen Mista Drazkowski na da alaƙa da siyasa, ba wai gaskiya ba.
Ta kuma shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa: "Ya kamata al'ummar da yake wakilta su damu da yadda yake amfani da kuɗaɗen masu biyan haraji wajen musgunawa wata 'yar takara Musulma."




























