KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 18/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Lahadi 18 ga watan Oktoban 2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. Rasha ta kai mana hari kan ɓangaren makamashinmu aƙalla sau 76 - Ukraine

    Zelensky

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya zargi Rasha da kai hare-hare a ɓangarorin man fetur da iskar gas na ƙasarsa har sau 76 tun bayan da Donald Trump ya sanar da yarjejeniyar tsagaita kai hare-hare kan cibiyoyin makamashi mako guda da ya gabata.

    A cewar Zelensky, Ukraine ta mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar, amma ta koma kai hare-hare bayan kwana uku da Rasha ta ci gaba da sabbin hare-hare.

    A sabon harin da ta kai cikin daren jiya, jirage marasa matuƙa na Ukraine sun kai hari kan wani matatar mai a birnin St Petersburg na Rasha, lamarin da rahotanni suka ce ya yi sanadin mutuwar mutum guda tare da jikkata wasu biyar.

    A nata ɓangaren, Rasha ta ce dakarun kariyar sararin samaniyarta sun harbo fiye da jirage marasa matuƙa 1,000 na Ukraine a sassa daban-daban na ƙasar.

    Sabbin zarge-zargen da hare-haren na nuna yadda rikicin da ke tsakanin Rasha da Ukraine ke ci gaba duk da ƙoƙarin samar da yarjejeniyoyin dakatar da kai hare-hare.

  2. Ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso sun amice su yi aiki da ƙasashen ECOWA

    AES

    Ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso, waɗanda ke ƙarƙashin mulkin sojoji, sun koma tattaunawa da ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) a ranar Asabar, sama da wata 18 bayan sun fice daga ƙungiyar.

    Ɓangarorin biyu sun amince su yi aiki tare domin samar da wani yarjejeniyar haɗin gwiwa.

    Ƙasashen uku, waɗanda sojoji suka ƙwace mulki a tsakaninsu daga shekarar 2020 zuwa 2023, sun fice daga ECOWAS a watan Janairun 2025 bayan sun kafa nasu ƙawancen mai suna Ƙungiyar Kasashen Sahel (Alliance of Sahel States - AES).

    Tun daga watan Janairun 2025 ake gudanar da tattaunawa tsakanin ECOWAS da AES, amma taron ministoci na ranar Asabar shi ne na farko da aka gudanar a hukumance.

    A cikin sanarwar haɗin-gwiwa da suka fitar a yammacin ranar Asabar, ɓangarorin biyu sun yaba da ƴan uwantaka, mutunta juna da kuma buɗe ƙofa ga tattaunawa da aka nuna yayin ganawar.

    Sanarwar ta jaddada muhimmancin ci gaba da kyakkyawar maƙwabtaka, musamman ta fuskar girmama ikon cin gashin kai na kowace ƙasa.

  3. An kama matar da ta yi yunkurin tafiya da tabar wiwi Saudiyya a Kano

    NDLEA

    Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) sun kama wata mata mai suna Fatimah Ahmad da tabar wiwi mai nauyin gram 511.75 da aka ɓoye a cikin galan mai, yayin da take shirin tafiya Saudiyya ta filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

    An kama ta ne ranar Juma’a, 16 ga Oktoba, 2026, yayin binciken fasinjojin jirgin Ethiopian Airlines da zai tashi zuwa Jiddah ta Addis Ababa.

    A cewar NDLEA, Fatimah ta ce ɗan uwanta, Abubakar Yahaya, ne ya ba ta galan ɗin, lamarin da ya kai ga kama shi a filin ajiye motocin filin jirgin.

    A wani samame daban a tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Legas, hukumar ta gano kilogram 8,725 na tramadol a matsayin hoda, wanda darajarsa ta kai sama da naira biliyan 6.98 a kasuwar miyagun ƙwayoyi.

    Hukumar ta kuma kama wata tsohuwa mai shekara 85 a Edo tare da ƙwace miyagun ƙwayoyi a wasu samame a jihohin Ondo, Bauchi, Kano, Kaduna da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

    NDLEA ta ce samamen na daga cikin ƙoƙarinta na dakile safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya. Waɗanda aka kama ana ɗaukar su a matsayin waɗanda ake zargi har sai an tabbatar da laifinsu a kotu.

  4. Jirgi mai saukar ungulu ya yi hatsari a Saudiyya

    Saudi

    Ƙawancen sojojin ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta ya ce hatsarin wani jirgin sama mai saukar ungulu a yankin Najran ya yi sanadin mutuwar ma’aikatan jirgin biyu.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa kakakin ƙawancen, Turki al-Maliki, ya bayyana a cikin wata sanarwa ranar Lahadi cewa jirgin saman na Saudiyya ya yi hatsari ne sakamakon matsalar fasaha a yankin Najran, lamarin da ya kashe ma’aikatan jirgin biyu.

    Sanarwar ta kuma ce jirgin ya faɗi ne a wani yanki da ke ƙarƙashin ikon Ma’aikatar Rundunar Tsaron Ƙasa ta Saudiyya.

    Ba a ƙarin bayani kan musabbabin matsalar fasahar da ta jawo hatsarin ba.

  5. Jirgi mai saukar ungulu ya yi hatsari a Saudiyya

    Saudi

    Ƙawancen sojojin ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta ya ce hatsarin wani jirgin sama mai saukar ungulu a yankin Najran ya yi sanadin mutuwar ma’aikatan jirgin biyu.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa kakakin ƙawancen, Turki al-Maliki, ya bayyana a cikin wata sanarwa ranar Lahadi cewa jirgin saman na Saudiyya ya yi hatsari ne sakamakon matsalar fasaha a yankin Najran, lamarin da ya kashe ma’aikatan jirgin biyu.

    Sanarwar ta kuma ce jirgin ya faɗi ne a wani yanki da ke ƙarƙashin ikon Ma’aikatar Rundunar Tsaron Ƙasa ta Saudiyya.

    Ba a ƙarin bayani kan musabbabin matsalar fasahar da ta jawo hatsarin ba.

  6. 'Hare-haren Saudiyya sun kashe aƙalla mutum 12 a yankin Houthi'

    Kafofin yaɗa labaran ƙungiyar Houthi sun ruwaito a ranar Asabar cewa hare-haren sama da Saudiyya ke jagoranta a Yemen, waɗanda suka fara tun daren jiya, sun kashe aƙalla mutum 12, ciki har da yara uku.

    Kamfanin dillancin labaran Houthi ya bayyana cewa jiragen yaƙin Saudiyya sun kai hari kan abin da ya kira “gidajen fararen hula” a lardin Taiz a ranar Asabar, inda suka kashe mutum tara tare da jikkata wasu 16.

    A cewar kamfanin, har yanzu akwai mutane da dama da ke maƙale a ƙarƙashin baraguzan gine-ginen da suka rushe sakamakon hare-haren.

    Tun da farko, kamfanin ya kuma ruwaito cewa yara uku sun mutu yayin da wasu 17 suka jikkata a hare-haren da Saudiyya ta kai da daddare a lardin Dhamar.

    Kafofin Houthi sun yi zargin cewa an yi amfani da manyan bama-baman gungu, waɗanda aka haramta amfani da su a ƙasashen duniya, wajen kai waɗannan hare-hare.

    A gefe guda kuma, yayin da ake ci gaba da sabon salon hare-haren Houthis, Saudiyya ta sanar a ranar Asabar cewa ta kakkabo jirage marasa matuƙa guda huɗu da ƙungiyar ta harba.

  7. 'Sojoji 8 sun mutu bayan motarsu ta taka nakiya a Borno'

    Sojoji

    Wasu majiyoyin tsaro sun shaida wa AFP cewa sojojin Najeriya takwas sun mutu bayan wata motar sintirin soji ta taka nakiya da mayaƙan ƙungiyar ISWAP suka dasa a kusa da iyakar Najeriya da Kamaru.

    Lamarin ya faru ne a ranar Asabar a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, a daidai lokacin da Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ke ziyartar Maiduguri bayan wani hari da aka kai wa sansanin soji kwanaki kaɗan da suka gabata, wanda ya kashe sojoji 15 da kuma mambobin ƙungiyar sa-kai masu yaƙi da masu tayar da ƙayar baya biyar.

    Ko da yake tashe-tashen hankulan ƴan jihadi da suka fara a Najeriya a shekarar 2009 sun ragu idan aka kwatanta da yadda suka yi ƙamari kusan shekara goma da ta gabata, ana ganin hare-haren sun fara ƙaruwa a cikin shekaru biyu da suka gabata.

    A sabon harin, sojojin na duba ayyukan wasu mambobin ƙungiyoyin sa-kai da ke share dazuzzuka da ciyayi a gefen babban titin da ke wajen garin Gamboru, lokacin da motarsu ta taka nakin, wanda ya tarwatse tare da kashe dukkan sojojin takwas da ke cikinta.

    Majiyoyin sun zargi ƙungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) da kai harin, kasancewar tana da ƙarfi a yankin.

    Mayaƙan jihadi kan yi amfani da dazuzzuka da ciyayi da ke gefen manyan tituna domin ɓuya su kai wa sojoji da matafiya hari ba-zata.

    Wani jami'in soji a yankin ya ce harin ya faru ne a ƙauyen Kinuba, mai tazarar kilomita 25 daga Gamboru, inda ya tabbatar da cewa dukkan sojojin takwas sun mutu nan take a fashewar.

    Ibrahim Liman, wanda ke cikin ƙungiyar sa-kai da ke taimakawa sojoji wajen yaƙi da 'yan ta'adda, shi ma ya tabbatar da adadin waɗanda suka mutu.

    Ya ce an binne abin fashewar ne a kan titin ƙasa kuma an tayar da shi daga nesa ta hanyar wata igiyar fashewa.

    Liman ya kuma ce wani ɗan ƙungiyar sa-kai da ke kula da aikin share ciyayin ya samu raunuka sakamakon gutsattsarin ƙarfen da fashewar ta watsa.

  8. Amurka ta buƙaci Isra’ila ta dakatar da hare-hare a Yammacin Kogin Jordan

    Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce Washington ta bukaci Isra’ila ta magance hare-haren da Yahudawa ƴan kama wuri zauna ke kaiwa a yankin Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ke mamaye da shi.

    Rubio ya shaida wa manema labarai cewa hotunan yadda aka doki wata ƴar jaridar Amurka a ranar Juma’a abin damuwa ne, kuma ba su nuna Isra’ila a kyakkyawan yanayi ba.

    Kalaman nasa sun zo ne bayan jakadan Amurka a Isra’ila, Mike Huckabee, ya bayyana harin da aka kai wa Heidi Levin a matsayin “abin kyama da kuma aikin ta’addanci.”

    Ana kai wa Levin harin ne yayin da take bayar da rahoto kan hare-haren da wasu ƴan kama wuri zauna ke kai wa Falasdinawa da ke girbin zaitun.

    A jiya ma, wasu jami’an diflomasiyya daga kasashen Turai da suka kai ziyara yankin Yammacin Kogin Jordan sun fuskanci hari.

  9. 'Sauƙaƙa takukuman Rasha ba laifi ba ne'

    Marco Rubio

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya kare matakin da Donald Trump ya dauka na dakatar da kakaba sabbin takunkumi kan Rasha da kuma kasashen da ke sayen man fetur daga Rashan.

    Rubio ya ce an dauki matakin ne domin ba da damar nazarin irin tasirin da kudirin dokar takunkumin da aka amince da shi kwanan nan zai iya yi kan farashin man fetur a duniya.

    Ya shaida wa manema labarai cewa ba yakin da Trump ke yi da Iran ne kadai ke kara tsadar man fetur ba. Matakin dakatar da takunkumin ya janyo suka daga 'yan siyasar manyan jam'iyyun biyu na kasar ciki har da wasu sanatocin jam'iyyar Republican.

    Rubio ya kuma musanta cewa an bayar da umarni daga Fadar White House na rage saurin tsarin sadarwar Starlink da Ukraine ke amfani da shi wajen sarrafa jiragen da ke tare hare-haren jirage marassa matuka. break

  10. An kama mutum 1,200 kan zanga-zangar tsadar rayuwa a Faransa

    Faransa

    Firaministan Faransa, Sebastien Lecornu, ya ce an kama mutum 1,200 bayan zanga-zangar da aka gudanar a ranar Asabar kan taɓarɓarewar ayyukan gwamnati da tsadar rayuwa ta rikiɗe zuwa tarzoma.

    Lecornu ya ce jami'an tsaro 150 sun jikkata a arangamar, yana mai cewa abin mamaki ne yadda adadin wadanda suka jikkata bai zarce haka ba.

    Magajin garin Paris, Emmanuel Gregoire, ya ce an yi barna sosai a wasu tituna, inda aka fasa shaguna tare da cinnawa motoci wuta.

    A birnin Limoges, gobara ta kone ginin majalisar birnin da aka gina tun karni na 19.

    Fiye da mutum dubu dari biyar ne suka shiga zanga-zangar, wadda ke cikin jerin zanga-zangar nuna fushin jama'a da ke kara kamari kan gwamnatin Shugaba Emmanuel Macron.

  11. Ba za mu bari Iran ta sake farfaɗo da shirinta na nukiliya ba - Trump

    Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake bayyanawa a ranar Asabar yayin wani jawabin yaƙin neman zaɓe a jihar Kentucky cewa matsalar Iran za ta zo ƙarshe nan ba da jimawa ba, kuma farashin mai zai dawo yadda aka saba.

    Ya kuma ce: "Ba ma son mu riƙa dawowa duk bayan shekara biyu. Muna son mu kammala dukka aikin ne gaba ɗaya."

    Donald Trump ya ƙara da cewa: "Ya kamata a kai wa Iran hari domin tana ƙoƙarin sake ƙera makaman nukiliya."

    Sai dai Iran ta dade tana musanta zargin cewa tana neman mallakar makaman nukiliya.

    Trump ya kuma ce: "Muna bukatar tabbatar da cewa Iran ba ta sake farfaɗo da shirinta na nukiliya ba, kuma wannan ne abin da muke aiki a kai a halin yanzu."

  12. Buɗewa

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa, barkanmu da safiyar yau Lahadi.

    Kamar kullum, yau ma shafin zai kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar, da yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya bakiɗaya.

    Za kuma ku iya leƙa shafukanmu na sada zumunta kamar Fesbuk da X da Instagram da ma Youtube domin kallon bidiyo da tafka muhawara.

    Da fatan za ku kasance tare da mu.