Jihohi 12 da Tinubu ya zaɓa don zuwa yaƙin neman zaɓe da kansa

Asalin hoton, Bola Tinubu/X
Jam'iyyar APC ta bayyana wasu jihohi 12 da ta ce Shugaba Bola Tinubu zai halarci yaƙin nemansa.
A lokacin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa a tsakiyar mako a fadarsa da ke Abuja, shugaban Tinubu ya ce ba duka jihohin ƙasar zai samu zuwa yaƙin neman zaɓen da kansa ba, saboda ayyukan mulki da ke gabansa.
Cikin wata sanarwar da jam'iyyar ta fitar a ranar Alhamis ta lissafa jihohi 12 da ta ce su en shugaban ƙasar zai halarta domin yaƙin neman zaɓen da kansa, yayin da ta ce sauran kwmaitin yaƙin neman zaɓensa zai wakilce shi.
A siyasar Najeriya, zaɓen shugaban ƙasa na da alaƙa da tasirin yankuna da ƙarfin jam'iyya, da kuma yadda ake tattara goyon bayan masu zaɓe a wuraren da ake ganin za su iya sauya akalar sakamako.
Zaɓen jihohin da ɗan takara zai fi mayar da hankali a kai na nuni da dabarun da jam'iyyarsa ta tsara.
Wasu daga cikin jihohin da APC ke son maida hankali a kansu na da muhimmanci saboda yawan masu rajistar zaɓe, yayin da wasu kuma ke da tasiri saboda tarihin yadda ake kaɗa ƙuri'a ko kuma matsayinsu a siyasar yankunansu.
Haka kuma akwai jihohin da ake kallon su a matsayin filin fafatawa tsakanin manyan jam'iyyu.
Waɗanne jihohi ne Tinubu zai je?
Jam'iyyar ta bayyana jihohin 12 da Shugaban Tinubun zai halarta kamar haka:
- Kaduna, (Bikin ƙaddamarwa)
- Rivers
- Plateau
- Oyo
- Borno
- Enugu
- Bauchi
- Sokoto
- Delta
- Kano
- Adamawa
- Lagos (Bikin rufewa)
Mece ce hikimar zaɓen waɗannan jihohi?

Asalin hoton, Bola Tinubu/X
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk da cewa Shugaba Tinubu ya kafa hujjar ayyukan gudanar da mulki kan dalilinsa na zaɓar wasu jihohin, masu bibiyar siyasa na ganin akwai wata dabara ta siyasa kan hakan.
Dr Kabiru Sa'id Sufi, Malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke Kano, kuma mai sharhi kan al'amuran siyasar Najeriyar ya ce zaɓar waɗannan jihohi ba ya rasa nasaba da sakamakon zaɓen 2023 da kuma muhimmancin jihohin ga zaɓen.
Daga cikin jihohin 12, Tinubu ya samu nasara ne a jihohi uku kawai a zaɓen 2023, wato Rivers da Oyo da kuma Borno.
''A sauran jihohi taran kuwa, manyan abokan hamayyarsa, Atiku Abubakar da Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso ne suka kayar da shi', a cewar Sufi.
Dr Sufi ya ce dabarar siyasa ce ta sa Shugaba Tinubu zaɓen waɗannan jihohi.
''Idan ka duba jerin jihohin za ka fahimci cewa kowane yanki na ƙasar nan ya samu wakilci, ta yadda babu yankin da zai ce ba a yi da shi ba'', in ji shi.
''Zaɓen Jihar Borno, kamar karrama mataimakinsa Kashim Shettima ne tun da jiharsa ce ta haihuwa, haka ma Rivers ina ganin ya zaɓe ta ne domin karrama Ministan Abuja, Nyesom Wike'', in ji shi.
Kusan a iya cewa, kashi 75 cikin 100 na jihohin da Shugaba Tinubu zai je da kansa za su gudana ne a jihohin da ya sha kaye a zaɓen 2023.
A lal misali, Atiku Abubakar ya kayar da Tinubu a jihohin Kaduna da Bauchi da Sokoto da kuma Adamawa, yayin da Peter Obi ya yi nasara a Plateau da Enugu da Delta da kuma jiharsa ta Legas.
A nasa ɓangare, Rabiu Musa Kwankwaso ya lashe jihar Kano, inda ya samu kusan ƙuri'a miliyan ɗaya a ƙarƙashin jam'iyyar NNPP.
Kuma yanzu haka duka Atiku a ADC, yayin da Peter Obi da Kwankwaso ke takara a NDC.
Jihohin Atiku da Kwankwanso
Wasu ma na ganin Tinubu ya zaɓi zuwa jihohin da wasu daga cikin jiga-jigan hamayya ke da ƙarfi a cikinsu.
Dr Sufi ya ce yana ganin Tinubu ya zaɓi Adamawa ne saboda jiha ce ta babban ɗantakar hamayya Atiku Abubukar.
''Alal Misali Adamawa ce mahaifar ɗantakarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, yayin da Kano ta kasance gida da Injiniya Rabi'u Kwankwanso, wanda ke yi wa Peter Obi mataimaki, to ina ganin ya zaɓe su ne domin wata dabarar siyasa'', in ji shi.
Yawan masu zaɓe
Haka ma akwai masu ganin cewa Tinubu ya zaɓi jihohin da ke kan gaba a yawan masu kaɗa ƙuri'a.
A bayanin alƙaluman yawan masu rajistar zaɓe da INEC ta fitar Legas ce kan gaba a yawan masu rajistar zaɓe fiye da miliyan bakwai.
Sai Kano da ke biye da yawan masu rajistar zaɓe fiye da miliyan shida, da kuma Kaduna a matsayi na uku da yawan masu rajistar zaɓe fiye da miliyan 4.5.
A taƙaice dai jihohi takwas cikin 10 mafiya yawan masu rajistar zaɓen na cikin jerin jihohin da Tinubun zai halarta.
Wani abu da masana ke kallo a matsayin dabarar zuwa jihohin da suka fi yawan masu kaɗa ƙuri'a.
Dr Sufi ya ce yana ganin yawan masu kaɗa ƙuri'a a jihohin na daga cikin abubuwan da Tinubun ya yi la'akari da shi wajen zaɓen waɗannan jihohin
Ko zuwansa jihohin zai yi tasiri?
Dr Sufi ya ce zuwan nasa waɗannan jihohi za ta iya yin tasiri ga sakamkon zaɓen 2027, saboda wasu dalilai da ya bayyana.
Ya ce idan mazauna waɗannan jihohi suka kalli zaɓensu da Tinubu ya yi a matsayin alfarma, hakan zai sa su ba shi ƙuri'unsu ganin cewa kamar ya karrama su ya y.
''Haka ma idan ya yi amfani da ziyarar tasa wajen ƙaddamar da manyan ayyuka a jihohin, musamman waɗanda za su inganta rayuwar al'ummar yankunan hakan ka iya ƙara masa goyon baya a jihohin'' in ji masanin siyasar.
Sai dai a gefe guda jam'iyar ADC mai hamayya na ganin cewa ziyarar Tinubun waɗannan jihohi babu abin da za ta sauya ko ƙara masa.
Faisal Kabir, ɗaya daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar ya shaida wa BBC cewa abin da Tinubu ya kasa samu na goyon baya cikin shekara fiye da uku ba yadda za a yi ya same shi cikin wuni ɗaya da zai je jiha.




























