Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Jihohin Najeriya 24 da ka iya fuskantar ambaliya a watan Oktoba'
Cibiyar Gargaɗi Kan Ambaliyar Ruwa ta Ƙasa, wadda ke ƙarƙashin Ma'aikatar Muhalli ta Najeriya, ta yi gargaɗin cewa an za a iya samun ambaliya ruwa a jihohin ƙasar 24 cikin watan Oktoba mai kamawa.
Cikin wani rahoto da cibiyar ta fitar, ta ce jihohin da abin zai shafa na iya samun ƙasa mai yawan danshi, ruwan sama mai yawa, saurin kwararar ruwa a saman ƙasa, cunkoson ruwa a magudanan ruwa da kuma tashin matakin koguna.
A cewar rahoton haɗuwar waɗannan abubuwa na iya haifar da ambaliyar ruwa a lokacin da hasashen ya shafa.
''Akwai fargabar sake fuskantar gagarumar ambaliyar a jahohin na Najeriya da gwamnatin ƙasar ta bayyana da mai matuƙar haɗari, da kuma ta gargaɗi al'umomin da ke jihohi 24 da Babban Birnin Tarayya Abuja kan yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwan ranar daga 27 ga watan nan na Satumba zuwa 10 ga Oktoban wannan shekara ta 2026'', in ji rahoton..
Cibiyar ta ce wuraren da abin ya shafa na iya samun ƙasa mai yawan danshi da ruwan sama mai tarin yawa da cunkushewar magudanar ruwa da kuma cikowar koguna.
Jihohin da ke cikin hatsarin
Jerin jihohin da ambaliyar za ta fi shafa su ne:
- Benue
- Kogi
- Kwara
- Niger
- Adamawa
- Bauchi
- Taraba
- Rivers
- Edo
- Delta
- Cross River
- Bayelsa
- Akwa Ibom
- Abia
- Anambra
- Ebonyi
- Enugu
- Imo
- Ekiti
- Lagos
- Ogun
- Ondo
- Osun
- Oyo.
A jihar Ekiti, wuraren da aka ambata sun haɗa da Ado-Ekiti, Ijero, Ikere, Ekiti Southwest, Ekiti ta Gabas da Ise Orun da Ekiti ta Yamma.
A Lagos, wuraren sun haɗa da Apapa da Badagry da Epe da Eti-Osa da Ikeja, Ikorodu da Ikoyi da Lagos Island da Lekki da Ojo da Orile Agege da Surulere da Agege da Alimosho da kuma Kosofe.
An sanya Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT) cikin rukunin da suka fi fuskantar gagarumin haɗarin ambaliyar ta wannan shekara.
Wuraren da aka ambata sun haɗa da Abuja Municipal, Abaji, Asokoro, Bwari, Garki, Gwarinpa, Gwagwalada, Kuje, Kubwa, Maitama, Nyanya da Wuse.
Sauran jihohin da aka ambata cikin wannan rukuni sun haɗa da Nasarawa, Plateau, Bauchi, Taraba, Adamawa da Kebbi.
Cibiyar ta kuma sanya wasu al'ummomi a Bauchi, Borno, Gombe, Yobe, Zamfara, Sokoto, Katsina, Kano, Kaduna da Jigawa cikin jerin wuraren da ake sa ido saboda matsakaicin haɗarin ambaliya.
Me ke janyo ambaliya?
Ana iya samun ambaliya saboda ruwan sama mai ƙarfi, ko narkewar ƙanƙara ko kuma mummmunar guguwa, musamman a gaɓar teku.
Ambaliyar da aka fi sani ta kasu gida uku:
Ambaliyar da ke faruwa saboda ruwan sama mai ƙarfin gaske, har ta cika rafi ko kogi ko kuma sauran magudanan ruwa ta yadda ruwa zai tumbatsa kuma fita daga hanyoyon sa.
Ambaliya daga rafi, inda rafin ke cika ya wuce ƙa'ida saboda ƙarfin ruwan sama, ko narkewar dusar ƙanƙanra.
Ambaliyar bakin kogi, wadda guguwar tsunami da iska mai ƙarfi ke haifarwa.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi 80% zuwa 90% na annobar da ake samu a duniya, cikin shekara 10 da ta gabata tana da alaƙa da ammbaliya da kwararar hamada da guguwar tsunami da tsananin zafi da kuma iska mai ƙarfin gaske.
Yadda mamakon ruwan sama ke janyo ambaliya
Idan rafi zai yi ambaliya, yana ɗaukar lokaci yana nuna alama saboda a hankali yake cik har ya shanye gaɓar da aka tsara tare ruwan rafin.
Amma idan ruwan sama ne ya haddasa ambaliyar, tana faruwa ne cikin ƙanƙanin lokaci daga fara ruwan saman zuwa lokacin da wurare za su cika nhar a samu ambaliyar.
Hukumar hasashen yanayi ta Birtaniya ta ce "Ambaliyar ruwa ta fi faruwa a wuraren da rafi baya da faɗi sosai, yanayin da ke bai wa ruwa damar kwarara cikin sauri. Tana kuma faruwa a ƙananan ƙoramu da a gefen su akwai ko dai titin mota da aka yiwa kwalta, ko ginin kankare musamman a birane, inda yake da wahalar gaske a samu ƙasar wajen ta shanye ruwan da ya kwararo.''
Ta ƙara da cewa "A haka ne sai ruwan ya ci ƙarfin magudanan da aka yi, har ya yi ambaliya.''
Shuka bishiyoyi da ciyawa na taimakawa sosai wajen hana ambaliya, musamman a birane domin kuwa suna tsotse ruwan.
Yadda za ku kare kanku a lokacin ambaliya
Ƙwararru sun zayyana abubuwan da ya kamata a yi idan ambaliya ta faru:
- Idan akwai barazana ga rayuwar wani ko wata, to a gagguta kiran lambobin agajin gaggawa domin samun ɗauki
- Kada ku yi tafiya ko tuƙi cikin ruwan da yake ambaliya ko kuma neman shiga cikin ruwan domin tsallakewa. Ruwan yana zuwa da ƙarfin gaske ta yadda zai iya janye mota.
- Kada a yi tafiya a kan katangar da ta kange rafi, ko kuma a gaɓar rafin
- A guji duk wani abu da zai a shiga cikin ruwan da ke ambaliya domin kuwa zai iya yaɗa cutuka. Idan kuma har aka taɓa ruwn, to a gaggauta wanke hannu ko wajen da ruwan ya taɓa da ruwa mai tsafta
- Kada a bari ƙananan yara su yi wasa a kusa da wajen da ake mbaliya
Madatsun ruwa shida da suka fi janyo ambaliyar ruwa a Najeriya
- Madatsar ruwa ta Lagdo - Kamaru
- Madatsar ruwa ta Kainji - Jihar Neja
- Madatsar ruwa ta Jebba - Jihar Neja
- Madatsar ruwa ta Shiroro - Jihar Neja
- Madatsar ruwa ta Alau - Jihar Borno
- Madatsar Kashinmbila – Taraba