Cutuka 5 masu alaƙa da zuciya da ke saurin kisa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Hukumar lafiya ta Birtaniya ta ce cututtukan zuciya matsaloli ne da suka shafi zuciya da kuma hanyoyin jini a wasu muhimman sassan jikin ɗan adam, ita kanta zuciyar da ƙwaƙwalwa da ƙoda da kuma idanu.

Hukumar ta bayyana hakan ne a lokacin da ake bikin tunawa da ranar zuciya ta duniya ta 2026 wadda ake gudanarwa duk ranar 29 ga watan Satumbar ko wacce shekara.

Taken ranar ta bana shi ne "Cutukan da ke da alaƙa da zuciya a boye suke, ka da ka yi wasa da bugun zuciyarka".

Matsalolin kan faru ne sakamakon kitse da ke taruwa a jijiyoyin jini da kuma ƙaruwar wasu abubuwa da ke janyo curewar jini.

Hukumar ta bayyana cewa, an fi samun haɗarin kamuwa da cutukan zuciya a tsakanin mutanen da suka haura shekara 50 a duniya, kuma hadarin na ƙaruwa ne idan mutum na ƙara manyanta.

Haka kuma jinsin mutane ƴan asalin kudancin Asia da Amurkawa ƴan asalin nahiyar Afrika da mutanen yankin Caribbean ƴan asalin Afrika sun fi hatsarin samun cututtukan zuciya.

A cewar hukumar lafiya ta duniya WHO ba kawai ana bikin ba ne domin jin dadi, sai don tunatar da mutane haɗuran da ke tattaure da zuciya lafiyar ta kuma kuma abubuwan da ka iya cutar da ita da mutum yake yi da sani ko kuma bisa rashin sani.

Alamun kamuwa da cutukan zuciya

Kwararren lilitan nan da Dr Tasi'u Ibrahim Malami a tsangayar koyar da aikin likita a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya ce wani babban haɗarin da cutukan da ke da alaƙa da zuciya ke da shi, shi ne rashin nuna alama ko kaɗan.

Ya ce daga lokacin da aka fara ganin alama babu shakka an kai wani mummunan yana yi da ba zai matuƙar bayar da wahala.

"Cutuka irinsu hawan jini, da Yawan kitse da kumburin zuciya da ciwon siga da dukansu ke da alaƙa da zuciya, sukan ɗaukar shekaru ba tare da mutum ya ji alamunsu ba".

Daga lokacin da mutum ya ji baya iya barci sai ya tara matashi da yawa, ko idan yana barci ya ji ya farka yana son shan iska, ko barci ya riƙa bashi wuya ko jiri, ko ciwon kai ko haki da sauransu, daga lokacin da aka fara jin wadan nan to cuta ta gama nisa, in ji likitan.

Ya ƙara da cewa "za a iya samun mutum lafiyayye yana komai ƙalau amma yana da matsalar zuciya ba tare da saninsa ba".

Hawan jini

Hawan jini ne nau'in cutar zuciya da ta fi shahara a nahiyar Afrika, kuma tana kashe mutane da dama a yankin, kamar yadda Dr Tasi'u ya bayyana

Hawan jini cuta ce da ake kamuwa da ita ta dalilin toshewar wasu jijiyoyin jini da suke kai wa ƙwaƙwalwa saƙo, kuma da zarar sun gaza ayyukansu to matsala ta faru.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, cikin wani rahotonta, ta ce akwai kimanin mutum biliyan 1.13 da ke fama da wannan cuta a duniya, kuma kashi biyu cikin uku masu matsakaicin samu ne.

Wani bincike da WHO ta yi a 2015 ya nuna cewa namiji 1 cikin 4 na fama da wannan cuta, yayin da 1 cikin 5 a mata ke fama da hawan jini.

Hawan jini cuta ce mai wahalar sha'ani wadda ba a warkewa daga gare ta da zarar an kamu da ita.

A Najeriya, wani bincike da aka yi ya ce sama da mutum miliyan 100 ne ke fama da wannan cuta, kuma maimakon raguwa kullum ƙaruwa adadin yake saboda tsarin yadda mutane ke rayuwa, da kuma irin abin da mutane ke ci ko sha, in ji shugaban asibitin Opal da ke Kaduna Dr Tasi'u Ibrahim.

Yana da nau'uka da dama amma wanda ya fi shahara shi ne (Primary hypertension) hawan jini na yau da kullum da aka fi sabawa da shi.

"Ana kamuwa da shi ne a hankali ba tare da wani dalili ba. Ba kamar wanda ake kamuwa da shi ba dalilin gado ko shekaru ko salon yadda muke rayuwa da kuma cimarmu", in ji Likitan

Yawan kitse

Wannan na sabuwa ne sakamakon dalilai da dama, da suka hada da rashin mota jiki yawan cin abinci mai kitse da dai sauransu.

Masanin lafiyar ya ce wannan ba shi da wuyar sha'ani kamar hawan jini, da mutum ya koma atisaye ya rage yawan kitsen da ke jikinsa sai cutar ta gushe.

Yawan haki da yawan gajiya na cikin alamun wannan cuta idan ta ci jikin mutum da yawa.

Masana irinsu Dr Tasi'u na ba da shawarar kiyaye duk wasu abubuwa da ka iya ta'azzara wannan cuta.

Sannan kuma suna ba da shawarar a rungumi duk wani mataki da ka iya kai mutum ga kaucewa cutar.

Toshewar jijiyoyin jini

Wannan wata cuta ce itama mai rikita dan adam saboda yawan rikiɗar da take yi idan ana magance ta.

Jijiyoyin zuciya ne suke toshewa dalilin kitse da yake curewa ya hana jini kaiwa inda ake so.

Ita kuma aikin zuciya shi ne tura jinin kaiwa sauran sassan jiki, zuwa kwakwalwa.

Duk lokacin da hakan ya gaza, sai wadannan jijiyoyi su toshe sai su gaza aikinsu.

Duka wannan abubuwa kan faru ba tare da sanin mutum ba, amma a ranar da za su nuna suna da matsala to tabbas sun yi raunin da ɗan adam zai tabbatar da cewa ba shi da lafiya.

Kumburar jijiyoyin zuciya

Wannan na da alaƙa kai tsaye da toshewar zuciya saboda toshewar ce ke haifar da kumbrin zuciyar.

Masanin lafiyar ya ce " idan wadannan biyun suka haɗu cikin sauki suke kai ɗan adam ga halaka".

A cewarsa idan matakin rashin lafiyar zuciya ya kai wannan mataki to babu shakka samun sauki ɗan adam abu ne mai kamar wuya.

Hujewar zuciya

Mannan matsala ce da ba a fiye samunta tsakanin manyan mutane ba, tafi ƙamari tsakanin yara, kuma ana haifarsu ne da wannan cuta.

"Bangon zuciyarsu ne ke zuwa a ɓule, za a ga alamar leɓensu kullum ya yi ja, sannan kuma za su riƙa shan wuya a yayin numfashi," kamar inda Likitan yabayyana.

Masanin ya ƙara da cewa ana yi wa yara masu fama da wannan cutuka aiki, kuma ana yin dace a mafi yawan lokutan da ake yinsu.

Yara da dama a faɗin duniya an haife su da wannan matsala, amma a yau sun warke suna rayuwarsu ba tare da wata matsala ba.

Mafita

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO kimanin mutane miliyan 19.8 ne suka mutu dalilin cutukan da ke da alaƙa da bugun zuciya a 2022, kimanin kashi 32 na yawan mutanen da suka mutu a faɗin duniya.

Kimanin kashi 85 na wadanda suka mutu daga irin wannan cutuka sun mutu ne sakamakon bugun zuciya take yanke ko kuma mutuwar ɓarin jiki.

Masana sun bayar da shawarar zuwa asibiti a-kai-a-kai domin tabbatar da sassaan zuciya na aiki daidai, tun da rashin lafiyarsu a lokuta da dama ba sa nuna alama.

Sun kara bayar da shawarar a riƙa motsa jiki aƙalla sau uku a mako.

Sannan a riƙi cin abinci mai inganci ga jiki, a ci ganyaye a ci kayan marmari.