Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 29/09/2026

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba

  1. Za a naɗa ɗanjarida a matsayin Sarki a Uganda

    Gaba a yau ne za a yi bikin naɗin Yarima Edward Kijanangoma a matsayin Sarkin Masauartar Tooro a Uganda.

    Bikin naɗin sarautar na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsaka da takaddama mai zafi game da wanda zai gaji karagar mulki a gidan sarautar.

    Ga ’yan Uganda da dama, ba a san shi a matsayin magajin karagar mulki ba, sai dai a matsayin ɗan jarida, wanda ya shafe shekaru yana aiki a matsayin mai gabatar da labarai a gidan rediyo da talabijin na gwamnati.

    A jiya Litinin ne, Yarima Edward ya gudanar da wasu al'adun gargajiya da aka daɗe ana yi tsawon ƙarnuka, a wani ɓangare na bukukuwan naɗin sabon sarki.

    A daren jiya kuma Yarima Edward ya samu rakiyar ɗaruruwan mutane zuwa Fadar Karuziika inda za a naɗa shi a matsayin sabon sarki.

    A ƙofar fadar, an shirya wasan nuna bajinta tsakanin magoya bayan wani yarima da kuma na sabon sarkin.

    Bisa al'adar Tooro, wasan nuna bajintar wanda sabon sarkin ya yi nasara, yana alamta miƙa ragamar mulki ga sabon sarki. Haka kuma, al'adun suna nuna amincewa da sabon sarkin.

    Da dama daga cikin mutanen sun riƙe fitilun gargajiya inda suke haska hanya yayin tattakin.

    A yau kuma ana sa ran sarkin zai halarci taron addu'oi a coci kafin ya gabatar da jawabi. Daga bisani kuma zai koma Fadar Karuziika inda za a naɗa shi sarki kuma ya karɓi sunan Sarki Edward Rukidi Kijanangoma Nyabongo I.

    Ƴan majalisar sarki ne suka naɗa Yarima Edward Kijanangoma domin ya gaji marigayi Sarki Oyo Nyimba Kabamba Iguru, wanda ya rasu a watan da ya gabata sakamakon cutar daji.

  2. Ƴaƴan manyan ƴansiyasar Najeriya da ke takara a 2027

    A daidai lokacin da ake ƙara tunkarar zaɓen 2027, ana ganin yadda ƴaƴan wasu daga cikin fitattun ƴan siyasar Najeriya ke neman gadon kujerun siyasa da iyayensu suka taɓa riƙewa ko kuma suka yi fice a siyasar. Lamarin na ƙara haifar da muhawara kan ko siyasar Najeriya na neman komawa kamar gado?

  3. OpenAI ya soke ƙudirin sakin sabon tsarin fasahar saboda tsaro

    Kamfanin ƙirƙirarriyar basira na OpenAI, ya sanar da dakatar da shirin sakin wani sabon tsarin basirar saboda matsalolin da suka shafi tsaro.

    A cikin wata sanarwa, kamfanin ya ce tsarin, mai suna GPT-6.1 Astra, bai cika ka'idojin da aka gindaya ba wajen kasancewa cikin iyakokin da aka amince da su, da kuma yadda yake bayyana wa masu amfani irin aikin da ya gudanar.

    An tsara fitar da sabon tsarin ne a wata mai zuwa.

    Wannan mataki na zuwa ne a lokacin da kamfanonin da ke samar da kirkirarriyar basirar AI ke fuskantar ƙarin bincike da kuma kiraye-kirayen samar da ƙa'idojin da za su daidaita ayyukansu.

  4. Firaiministan Faransa ya yi gargaɗi kan tsananta zanga-zangar ɗalibai

    Firaministan Faransa, Sebastien Lecornu, ya yi gargaɗin cewa duk wani yunkuri na tsananta zanga-zangar ɗalibai da ake yi a makarantun sakandare a faɗin ƙasar zai kasance marar amfani.

    Fiye da mutum 160 aka kama a ranar Litinin dangane da zanga-zangar.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Lecornu ya yi misali da rahotannin da ke cewa an yi amfani da tartsatsin wuta da kuma tashe-tashen hankula a yayin zanga-zangar.

    Gangamin ya fara ne a birnin Paris a makon da ya gabata, inda ɗalibai suka shafe kwanaki suna kulle makarantunsu domin nuna rashin amincewa da halin da suke ciki.

    Daga cikin dalilan zanga-zangar akwai cunkoson ɗalibai a ajujuwa, da yawan ayyuka da kuma ƙarancin malamai.

    Tun daga lokacin ne zanga-zangar ta bazu zuwa wasu sassa na kasar.

  5. 'Akwai hannun ƴan ƙasar waje a hari kan sansanin sojin Birtaniya'

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce abin da ya faru a wani sansanin sojin sama na Birtaniya da dakarun Amurka ke amfani da shi, inda aka kama wasu maza biyar bisa zargin shirya aikata ta'addanci, ya bayyana a fili cewa akwai hannun wasu 'yan kasar waje.

    Da yake magana da gidan talabijin na Fox News, Rubio ya ce ana sa ran samun karin bayanai a cikin kwanaki masu zuwa.

    Tun da farko, sakataren harkokin tsaron Birtaniya, ya ce ya yi wuri a tabbatar da cewa akwai hannun wasu 'yan kasar waje a cikin lamarin.

    Tuni dai shugaban Amurka Donald Trump, ya soki matakin 'yan sandan yaki da ta'addancin Birtaniya wanda suka bayar da belin mutanen biyar.

    Sansanin sojin da abin ya shafa na daga cikin wuraren da Amurka ta yi amfani da su wajen kai hare-hare kan Iran. Sai dai gwamnatin Iran ta musanta zargin cewa tana da hannu a harin da ake bincike a kansa.

  6. Trump ya musanta tayin sassauta wa Iran takunkumi

    Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta rahotannin kafafen yaɗa labarai da ke cewa ya yi wa Iran tayin sassauta mata takunkuman da aka kakaba mata da kuma sakin wasu kuɗaɗen ƙasar da aka rike, domin ta amince da wasu sharuɗɗan da suka shafi shirinta na nukiliya.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump ya bayyana wani rahoto da kafar yaɗa labarai ta Axios ta wallafa a matsayin zancen kanzon kurege.

    Rahoton na kafar yada labaran wanda ya ambato wasu jami'an gwamnatin Amurka, ya ce Washington ta miƙa wannan tayi ne yayin da masu shiga tsakani daga ƙasashen Qatar da Pakistan ke ƙoƙarin kulla yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran a birnin New York.

    Ana sa ran masu shiga tsakanin za su tattauna a lokuta daban-daban da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, da kuma jami'an gwamnatin Amurka a ƙoƙarin rage zaman dar-dar da ke tsakanin kasashen biyu.

  7. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye daga BBC Hausa

    Ku biyo mu domin sanin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sauran sassan duniya.

    Akwai shafukanmu na sada zumunta da za ku iya zuwa domin kallon bidiyo har ma ku tafka muhawara kan labaran da muka wallafa.