Ƴaƴan fitattun ƴan siyasar Najeriya da ke takara a zaɓen 2027

    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

A daidai lokacin da ake ƙara tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, ana ganin yadda ƴaƴan wasu daga cikin fitattun ƴan siyasar Najeriya ke neman gadon kujerun siyasa da iyayensu suka taɓa riƙewa ko kuma suka yi fice a siyasar.

Akwai ƴaƴan tsoffin shugabannin ƙasa, zuwa na tsoffin gwamnoni da shugabannin majalisar dattawa, da ke neman tikitin takara a manyan jam'iyyun siyasar ƙasar domin wakiltar al'ummominsu a majalisar ƙasa.

Lamarin na ƙara haifar da muhawara kan ko siyasar Najeriya na neman komawa kamar gado?

Sai dai wasu na ganin suna da ƴancin neman mulki kamar kowane ɗan Najeriya, yayin da masu suka ke ganin yawan bayyanar sunayen ƴaƴan manyan 'yan siyasa a jerin masu neman muƙamai na cewa an dabaibaye tsarin a waje ɗaya.

Bayanan da hukumar zaɓen ƙasar, INEC ta fitar sun nuna cewa mutum 20 daga cikin ƴaƴan fitattun ƴan siyasa a Najeriya ke neman muƙamai daban-daban. Wasu sun riga sun shiga harkokin siyasar, har ma sun riƙe muƙamai, yayin da wasu ke shirin fara takara a 2027.

Daga cikinsu, biyar na takarar kujerun Sanatoci, yayin da sauran 15 ke neman kujerun Majalisar Wakilai ta tarayya.

To, su waye waɗannan ƴaƴan fitattun 'yan siyasar da ke neman shiga da ɗorawa daga inda iyeyensu suka tsaya?

Ƴaƴan tsofaffin shugabannin ƙasa

Mutum uku waɗanda ƴaƴan tsofaffin shugabannin ƙasa da mataimakan shugaban ƙasa ne suke neman takara a zaɓen 2027.

Daga cikinsu, akwai mai neman kujerar Sanata, yayin da biyu ke neman kujerun Majalisar Wakilai ta tarayya.

Iyabo Obasanjo – Ogun

Iyabo Obasanjo ƴar tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ce. Ta yi takara a baya, inda ta taɓa zama Sanatar Ogun ta Tsakiya a Majalisar Dattawa.

A zaɓen 2027 ma tana neman kujerar Sanatar Ogun ta Tsakiya, a ƙarƙashin jam'iyyar PDP.

Ta rasa tikitin takarar gwamna a jam'iyyar APC, inda daga baya ta samu tikitin takarar Sanata a PDP.

An kai ruwa rana sosai kafin ta samu tikitin, inda wasu daga cikin jam'iyyar da kuma masu adawa da ita suka yi ta kai korafi ga hukumomi domin hana ta takarar.

Yusuf Buhari – Katsina

Yusuf Buhari ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne. Mahaifinsa ya shugabanci Najeriya daga 2015 zuwa 2023, a ƙarƙashin jam'iyyar APC.

Yusuf na takarar kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar Daura, Sandamu da Mai'adua a jihar Katsina.

Zai yi takara ne a ƙarƙashin jam'iyyar APC.

Adamu Atiku – Adamawa

Ɗa ne ga tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar a lokacin mulkin Olusegun Obasanjo.

Mahaifinsa ya daɗe yana cikin manyan ƴan siyasar da ake damwa da su aaƙasar, kuma ya taɓa neman shugabancin Najeriya sau da dama a jam'iyyu daban-daban.

Yanzu haka mahaifinsa ne ke takarar shugaban ƙasa a babbar jam'iyyar adawa ta ADC a zaɓen 2027 da ke tafe.

Adamu Atiku kuma yana neman wakiltar mazabar Ganye/Jada/Toungo/Mayo Belwa a Adamawa a majalisar wakilai ta tarayya ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulki.

Ƴaƴan tsofaffin gwamnoni

Mafi yawan waɗanda ke cikin wannan rukunin ƴaƴan tsoffin gwamnoni ne.

Aƙalla mutum takwas zuwa goma ke son su gaji iyayensu a jihohinsu.

Wasu daga cikinsu na neman kujerun Sanata ne yayin da mafi yawansu ke neman kujerun Majalisar Wakilai.

Bello El-Rufai – Kaduna

Ɗan tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ne. Yanzu haka shi ne ke wakiltar Kaduna ta Arewa a Majalisar Wakilai tun bayan da doke ɗan majalisar da ke kai a 2023 a jam'iyyar APC.

Sai dai yanzu yana neman komawa majalisar, amma a ƙarƙashin jam'iyyar ADC mai adawa.

Hakan ya biyo bayan saɓanin da ya faru tsakaninsu da APCn musamman ma yadda ba a ga maciji da mahaifinsa da jam'iyyar.

Mustapha Sule Lamido

Mustapha Sule Lamido ɗa ne ga tsohon gwamnan Jihar Jigawa kuma tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, Sule Lamido.

Ya shiga siyasa a shekarar 2019 inda ya yi takarar kujerar Majalisar Dattawa mai wakiltar Jigawa ta Tsakiya a ƙarƙashin jam'iyyar PDP.

A shekarar 2023, Mustapha ya sake fitowa takarar gwamnan Jigawa a ƙarƙashin PDP, inda ya fafata da Umar Namadi na APC, wanda ya lashe zaɓen.

Yanzu ma a zaɓen 2027, Mustapha na sake neman kujerar gwamnan Jigawa. A watan Mayun 2026, PDP ta amince da shi a matsayin ɗan takararta na gwamna, ba tare da hamayya ba.

Chinedum Orji – Abia

Chinedum Orji ɗan tsohon gwamnan jihar Abia, Theodore Orji, ne.

Yana takarar kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar Ikwuano, Umuahia ta Arewa da Umuahia ta Kudu.

Erhiatake Ibori-Suenu – Delta

Erhiatake Ibori-Suenu 'yar tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori, ce.

Ita ma ta taɓa lashe zaɓen Majalisar Wakilai, inda take wakiltar mazabar Ethiope ta Gabas da Ethiope ta Yamma.

Tana cikin waɗanda za su yi takarar Majalisar Dokokin Tarayya na 2027.

Olumide Osoba – Ogun

Olumide Osoba ɗa ne ga tsohon gwamnan Ogun, Olusegun Osoba. Yana wakiltar mazabar Abeokuta ta Arewa, Odeda da Obafemi-Owode a Majalisar Wakilai.

Yana cikin ƴaƴan manyan ƴan siyasar da ke neman kujerun majalisa a 2027.

Adegboyega Adefarati – Ondo

Adegboyega Adefarati ɗan marigayi tsohon gwamnan Ondo, Adebayo Adefarati, ne. Yana wakiltar mazabar Akoko ta Kudu maso Gabas da Akoko ta Kudu maso Yamma a Majalisar Wakilai.

Yana neman sake komawa kujerarsa a zaɓen 2027.

Olamiju Alao-Akala – Oyo

Olamiju Alao-Akala ɗa ne ga marigayi tsohon gwamnan jihar Oyo, Adebayo Alao-Akala, ne. Mahaifinsa ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ƴan siyasar jihar.

Yana takarar kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar Orire, Ogbomoso ta Arewa da Ogbomoso ta Kudu a majalisar wakilai ta tarayya.

Ƴaƴan Sauran Fitattun 'Yan Siyasa

Baya ga iyalan shugabannin ƙasa da gwamnoni, akwai wasu da suka fito daga gidajen manyan 'yan siyasa masu tasiri.

Daga cikinsu akwai:

Natasha Akpoti-Uduaghan (Jihar Kogi): 'Yar marigayi Jimoh Abdul Akpoti, tsohon ɗan Majalisar Wakilai, ce. Ita ce Sanatar Kogi ta Tsakiya mai ci kuma tana neman komawa kujerarta a jam'iyyar PDP.

Sadiq Ango Abdullahi (Jihar Kaduna): Ɗan fitaccen ɗan siyasa Ango Abdullahi ne. Shi ne ke wakiltar mazaɓar Sabon Gari a majalisar wakilai ta tarayya kuma yana neman kujerar a karo na biyu.

Abba Dahiru Mangal (Jihar Katsina): Ɗa ne ga fitaccen hamshaƙin ɗan kasuwa kuma mai kamfanin jiragen sama na Max Air, Dahiru Barau Mangal. Ko da yake mahaifinsa bai taɓa riƙe wani babban muƙamin siyasa ba, ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin mutane mafi tasiri a siyasar Jihar Katsina.

Ɗansa Abba Mangal ya samu tikitin takara a jam'iyyar APC na mazaɓar Katsina ta tsakiya a majalisar wakilai ta tarayya, lamarin da ya haifar da cece-kuce saboda ya kayar da ɗan majalisar wakilai mai ci, Sani Aliyu Danlami.

Blessing Onuh (Jihar Benue): 'Yar tsohon shugaban Majalisar Dattawa David Mark ce. Tana wakiltar Otukpo/Ohimini a Majalisar Wakilai kuma tana neman wa'adi na biyu

Gabriella Omosede Igbinedion (Jihar Edo): 'Yar fitaccen ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa Gabriel Igbinedion ce. Tana takarar Ovia North-East/Ovia South-West.

Sani Ibrahim Tanko (Jihar Bauchi): Ɗan fitaccen jigo a siyasar Bauchi ne kuma yana neman kujerar Shira/Giade. a majalisar wakilai ta tarayya.

Sirajo Ibrahim Tanko (Jihar Bauchi): Yana neman kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu.

Asuquo Ekpenyong (Jihar Cross River): Yana daga cikin ƴaƴan fitattun ƴan siyasa da ke neman kujerar Sanatan Cross River ta Kudu.

Adamu Abubakar (Jihar Neja): Yana neman wakiltar Chanchaga a Majalisar Wakilai daga jihar Neja.

Beni Lar (Jihar Plateau): 'Yar marigayiya Solomon Lar, wanda ya yi gwamna na farko na Filato kuma jigo a siyasar Najeriya. Tana neman takarar wakiltar Langtang North/Langtang ta Kudu

Wasu ƴaƴan fitattun mutanen da suka nemi takara ba su samu ba

Akwai wasu ƴaƴan fitattun mutane a Najeriya da suka so yin takara a 2027 amma kuma ba su samu nasara ba.

Wasu ba su samu tikitin takarar ba, ko kuma sun janyae aniyarsu, amma kuma sun takara muhimmiyar rawa a zaɓen fidda gwani.

Ga wasu daga cikinsu:

Fahad Dankabo — Kano

Fahad Muhammad Adamu Dankabo, ɗa ne da ya fito daga ahalin attajirin ɗankasuwa marigayi Alhaji Dankabo, wanda ya kafa kamfanin jiragen sama Kabo Air.

Ya nemi tikitin APC na takarar Majalisar Wakilai mai wakiltar Gwarzo/Kabo.

Sai dai bayan zaɓen fitar da gwani, Abdullahi Muazu Babangandu ne ya samu tikitin ta hanyar maslaaha.

Daga baya Fahad Dankabo ya bayyana goyon bayansa ga Babangandu tare da cewa zai mutunta matakin jam'iyyar.

Idris Isa Yuguda — Bauchi

Idris Isa Yuguda, ɗan tsohon gwamnan Bauchi Isa Yuguda, ya nemi tikitin takara a APC na Majalisar Wakilai a Bauchi.

A zaɓen fitar da gwani da aka gudanar na jam'iyyar PC a watan Mayun 2026, Jibrin Abdullahi Sirajo ne ya samu tikitin da kuri'u 13,190, yayin da Idris Isa Yuguda ya zo na biyu da 4,053.

Rasheed Kashamu — Ogun

Rasheed Kashamu, ɗan marigayi tsohon sanatan Ogun, Buruji Kashamu, ya nemi tikitin APC na Majalisar Wakilai a 2027.

Sai da zaɓen fitar da gwani na APC da aka gudanar a Ogun, ya samu ƙuri'u 265, yayin da Joseph Adegbesan ya samu 18,884 kuma ya lashe tikitin takarar.