Yadda INEC za ta yi amfani da AI a zaɓen Najeriya na 2027

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Hukumar zaɓen Najeriya (INEC) ta za ta yi amfani da ƙirƙirarriyar basirar AI domin tabbatar da an gudanar da sahihin zaɓe a babban zaɓen ƙasar na watan Janairun 2027.

Kwamishinan zaɓe na INEC a jihar Enugu, Chukwuemeka Chukwu, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis, yayin da yake wakiltar shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, a taron ƙungiyar editocin Najeriya da aka gudanar a Enugu.

Chukwu ya ce amfani da AI zai taimaka wa hukumar wajen "gano saɓani da kura-kurai a sakamakon zaɓe".

Wannan matsayar na zuwa ne yayin da ya rage kusan watanni huɗu kafin ranar 16 ga Janairun 2027, lokacin da za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar dokoki ta ƙasar.

Hakan na zuwa ne kuma a daidai lokacin da ƴan Najeriya da dama ke nuna shakku kan ko INEC za ta gudanar da zaɓen cikin gaskiya ba tare da maguɗi ba.

Ta yaya INEC za ta yi amfani da AI a zaɓen 2027?

INEC, ta ce za ta yi amfani da fasahar AI, wajen inganta tsarin gudanar da zaɓen 2027 tare da ƙarfafa matakan kariya daga bayanan ƙarya da aka ƙirƙira da wannan fasaha.

Shugaban INEC, Farfesa Amupitan, ya ce hukumar na ƙara tsaurara tsarin tsaron fasaharta domin dakile yiwuwar amfani da AI wajen ƙirƙirar takardun sakamakon zaɓe na bogi, kwaikwayon muryoyin jami'an zaɓe ko ƙirƙirar bidiyoyin bogi na ma'aikatan hukumar.

Ya kuma ce za a iya amfani da AI wajen ƙirƙirar takardun hukumar INEC na bogi, don haka hukumar na ɗaukar matakan kariya daga irin waɗannan barazanar.

Sai dai Amupitan ya bayyana cewa fasahar da hukumar ke amfani da ita ba za ta maye gurbin tsare-tsaren da kundin tsarin mulki ya tanada ba, illa dai za ta taimaka wajen ƙarfafa aikinsu ne.

"Dole ne AI ya ƙarfafa sahihancin zaɓe, ya inganta ayyukan gwamnati, kuma a koyaushe ya kasance ƙarƙashin ikon ɗan Adam. Duk wani binciken sakamako da aka yi ta na'ura zai kasance ƙarƙashin binciken ɗan Adam da kuma tantancewa bisa doka," in ji shi.

Amupitan ya ce INEC ta fara amfani da wasu fasahohin AI kai tsaye wajen sarrafa sakamakon zaɓe, inda fasahar za ta taimaka wajen gano bambance-bambance ko kura-kura yayin gudanar da aiki a bayanan sakamako kafin a amince da su.

Ya ce hukumar ta kuma kafa wani ƙaramin sashe na AI a sashen ICT ɗinta, tare da samar da taswirar yadda za ta yi amfani da AI da kuma tsarin kula da fasahar.

Bugu da ƙari, shugaban INEC ya ce hukumar na aiki da manyan kamfanonin fasaha irin su Microsoft da Google kan tsaron intanet da kuma kare tsarin adana bayananta a kan cloud daga yiwuwar kutse.

Hukumar ta kuma haɗa gwiwa da wata cibiyar ƙasa da ƙasa da cke kula da fasahohin tsarin zaɓe ta IFES, domin horas da ma'aikatanta kan yadda za su tafiyar da AI da kaucewa haɗurran ke tattare da shi da kuma yadda za a yi amfani da fasahar cikin tsari gabanin zaɓen 2027.

A farkon watan Satumba, shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya halarci wani taron na duniya kan amfani da AI a lokacin zaɓe a Ottawa, da ke ƙasar Kanada, inda ya yi magana kan shirin ƙara amfani da fasahar AI wajen inganta sahihanci da ingancin zaɓe a Najeriya.

A wajen taron, Amupitan ya ce yawan masu rajistar zaɓe a Najeriya, wanda ya kai miliyan 93, tare da kusan rumfunan zaɓe 180,000, ya sa amfani da fasaha ya zama wajibi kuma wani muhimmin ɓangare a tsarin zaɓen ƙasar.

A shekarun baya-bayan nan, Najeriya ta fara amfani da fasahohi daban-daban wajen gudanar da zaɓe, ciki har da na'urar BVAS da IReV, kuma hukumar na ƙara duba yadda za ta yi amfani da AI.

Shugaban INEC ya kuma ce hukumar ta fara horas da ma'aikatanta kan ilimin AI, kuma ba iya waɗanda ke sashen ICT ba, har da ma'aikatan sassan shari'a, wayar da kan masu zaɓe da kuma kula da haɗurran da ka iya tasowa.

A cewarsa, hakan zai tabbatar da cewa ma'aikatan hukumar a sassa daban-daban sun fahimci sabuwar fasahar da yadda za su yi amfani da ita.

A cewar Amupitan, akwai muhimman ƙa'idoji guda biyar da za su jagoranci shirin INEC na amfani da fasahar AI.

Waɗannan sun haɗa da:

  • Tabbatar da cewa ɗan Adam ne ke sa ido kan amfani da fasahar
  • Tabbatar da gaskiya da adalci
  • Kare bayanan jama'a da sirrinsu
  • Tsaron intanet da kula da haɗurran da ka iya tasowa
  • Tabbatar da fasahar na amfani ga ayyukan hukumar da amicewar jama'a

Ya ce tsarin gudanar da zaɓen 2027 kuma zai kasance ƙarƙashin dokoki da tanade-tanaden Najeriya guda biyar:

  • Kundin Tsarin Mulkin Najeriya
  • Sabbin dokokin zaɓe na 2026 da aka yi wa kwaskwarima
  • Dokoki da ƙa'idojin INEC na babban zaɓen 2027
  • Dokar kiyaye bayanai ta 2023
  • Dokar laifukan intanet ta 2024

Shugaban INEC ya jaddada cewa sanya AI cikin tsarin zaɓe ba yana nufin fasahar za ta riƙa yanke shawara da kanta ba ne.

Ya ce AI zai kasance wani ƙarin mataki da zai taimaka wa ma'aikatan hukumar wajen gano yiwuwar kura-kurai da bambance-bambance, domin ƙara sahihanci da inganta tsarin gudanar da zaɓe.

'INEC na son al'umma su sake yarda da ita'

INEC na ƙoƙarin ganin ta sake tabbatar da amincewar jama'a da hukumar bayan matsalolin da suka faru a babban zaɓen 2023, musamman gazawar shafin INEC na IReV wajen nuna sakamakon zaɓen shugaban ƙasa yadda ya kamata.

IReV wani shafi ne da aka ƙirƙira domin jama'a su riƙa bibiyar sakamakon zaɓe daga rumfunan zaɓe daban-daban a duk faɗin ƙasar a yayin da ake shigar da su ta intanet.

Bayan an kammala ƙidayar ƙuri'u a rumfar zaɓe, jami'in INEC da ke kula da rumfar ya kamata ya yi amfani da na'urar BVAS wajen ɗaukar hoton fom ɗin EC8A, wanda ke ɗauke da sakamakon zaɓen, sannan ya wallafa hoton a shafin IReV.

Sai dai a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na 2023, wannan tsarin bai yi aiki yadda aka tsara ba. Ƙoƙarin tura sakamakon zuwa IReV ya samu cikas, duk da cewa an yi nasarar wallafa sakamakon zaɓen Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai waɗanda aka gudanar a rana guda.

Daga baya INEC ta bayyana cewa matsalar na'ura ce ta hana wallafa sakamakon zaɓen shugaban ƙasar. Daga baya an wallafa sakamakon, amma hakan ya faru ne bayan hukumar ta tattara sakamakon da hannu.

Wani binciken BBC daga baya ya nuna cewa sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da INEC ta sanar a Jihar Rivers bai yi daidai da jimillar sakamakon da aka wallafa a IReV ba.