Ƴanƙwallon Turai da suka samu rauni a wasannin ƙasashensu

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Bruno Fernandesda Cody Gakpo da Patrick Dorgu suna cikin jerin fitattun ƴan wasan da suka samu rauni a lokacin wasannin ƙasashe, bayan raunin da suka ji da ya takaita musu buga wasannin Nations League.

Bayan da ya buga wa Portugal wasa a nasarar da ta doke Wales ranar Alhamis, kyaftin ɗin Manchester United, Fernandes, bai yi wa tawagar karawar Norway ba ranar Lahadi.

Kafin wasan, kocin Portugal, Jorge Jesus ya bayyana cewa Fernandes ya "buga wasan farko da muka yi nasara a kan Wales ɗauke da rauni''

"Ya buga karawar yana jin raɗaɗi daga raunin da ya zo da shi daga Manchester United," in ji kociyan. "Kawai yana son buga wasan Wales ne."

A halin da ake ciki abokin wasansa a United, Dorgu da ɗan wasan Liverpool, Gakpo duk sun samu raunuka a lokacin da suka buga wa ƙasashensu tamaula ranar Lahadi.

An cire Gakpo daga wasan bayan mintuna 17 a fafatawa da Netherlands ta samu nasara a kan Serbia da ci 2-1, inda ya nuna alamun ciwo tare da riƙe ƙasan ƙafarsa ta dama.

A ranar Alhamis Liverpool ta tabbatar da cewa ɗan wasan na Netherlands ya koma ƙungiyar. domim yin jinya, kenan ba zai buga wa Netherlands wasannin gaba ba.

"Ya ji rauni a kafa, wannan shi ne abin da na sani," in ji kocin Netherlands, Xavi kamar yadda ya sanar ranar Lahadi. "Muna fatan raunin ba wani mai tsanani ba ne."

Shi kuwa Dorgu, ya shafe mintuna 30 a fili kafin nasarar da Denmark ta samu a kan Wales da ci 2-0, kuma ana sa ran zai koma Manchester domin ƙarin tantance girman raunin da ɗan ya ji.

Wasannin kasa da kasa a 2026-27 an tsawaita kwanakin fiye da yadda aka saba, bayan da aka aka hade shi da wanda ake yi a cikin watan Oktoba.

Kenan mako uku aka gindaya daga karshen watan Satumba zuwa farkon makon Oktoba da kasashe za su buga Nations League ko wasannin neman shiga gasar kofin Afirka ko kuma na sada zumunta da sauransu.

Kuma ƴanwasa za su buga wa kasashensu karawa hudu, fiye da biyun da aka saba na al'ada.

Su wane ne suka ji rauni a wannan lokacin?

Raunin da Gakpo ya ji ya zama na biyu da zai yi jinya a Liverpool, bayan da Alexander Isak ya janye daga tawagar Sweden, sakamakon raunin da ya ji.

Tsohon ɗan wasan Newcastle United ya buga dukkan minti 90 a karawar da Sweden ta yi nasara 2-1 a kan Romania ranar Juma'a a gasar Nations League.

Saboda haka ba zai yi wa Sweden sauran wasa uku ba a wannan lokacin na karawa tsakanin kasa da kasa, kuma likitocin Liverpool suna auna koshin lafiyarsa.

A ranar Alhamis ɗan wasan Arsenal Kai Havert da mai taka leda a Sunderland, Brien Brobbey sun yi rauni a fafatawar da aka yi tsakanin Netherlands da Jamus.

Ɗan wasan Jamus, Havert ya ji rauni ne, bayan da Quinten Timber ya doki gwiwarsa a wasan da suka yi a Amsterdam da taka kai an canja shi.

Shi kuwa ɗan wasan Netherlands, Brobbey - wanda ya ci ƙwallo uku rigis a Sunderland a gasar Premier League da Manchester City ta yi nasara 5-3, shima ya ji rauni a karawar ta Nations League.

Haka kuma Sunderland ta kara cin karo da koma baya, sakamakon da Dan Ballard shima ya ji rauni a karawar da Ireland ta Arewa ta ci Georgia 1-0 ranar Juma'a.

Tuni kociya, Boss Michael O'Neill ya tabbatar da cewa Ballard ba zai buga wa kasar sauran wasannin Nations League ba.

Ba wai kawai ƴanwasan Premier League kadai ne suka rauni ba a lokacin da suke buga wa kasashensu wasa ba a wannan lokacin.

An sanar da cewar Kylian Mbappe zai yi jinyar mako biyu, bayan rauni da ya ji a gwiwarsa a lokacin da ya ci ƙwallo a wasan farko da Zinedine Zidane ya yi nasara a matakin kociyan Faransa.

Ƙwallon da Mbappe ya ci ita ce ta 67 a Faransa, bayan da Michael Olise ya bashi ƙwallon a karawar da suka ci Turkiya 1-0 daga nan aka sauya shi minti biyar tsakani.

Haka kuma ɗan wasan Jamus, Jamal Musiala ya ji rauni a lokacin atisayen tunkarar Jamus, daga nan ya hakura daga buga wa kasarsa wasan na Nations League.