Ko Najeriya na da damar zuwa Gasar Kofin Duniya ta mata bayan shan kashi?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Ƴan Najeriya na ci gaba da muhawara kan fitar da tawagar matan ƙasar daga gasar cin Kofin Afirka ta Mata, (WAFCON) da ake yi a ƙasar Moroko.

A ranar Lahadi ne Kamaru ta yi waje da tawagar ta Super Falcons bayan doke ta da ci 1-0.

Sakamakon wasan ya ɗasa shakku kan samun damar zuwan zakarun na Afirka Gasar Kofin Duniya ta Mata da za a yi a 2027 a ƙasar Brazil.

Najeriya, wadda ta lashe kofin Afirka na mata har sau 10 - an yi hasahen za ta taka muhimmiyar rawa a gasar ta bana, bayan lashe kofin a bara.

Tuni dai kocin tawagar Justin Madugu ya ɗauki alhakin rashin nasarar tare da bai wa ƴan ƙasar haƙurin baƙin cikin da suka ji kan rashin nasarar.

Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, jim kaɗan bayan tashi daga wasan, Madugu ya ce ƴanmatan sun yi iyakar bakin ƙoƙarinsu, amma "haka Allah ya ƙaddara".

''Don haka muna bayar da haƙurin abin da ya faru, kuma na ɗauki alhakin duk abin da ya auku a wasan'', in ji shi.

Me ya janyo rashin nasarar?

Sakamakon wasan ya bai wa masu bibiyar harkokin ƙwallon ƙafa da dama mamaki kasancewar wannan ne karon farko da aka fitar da Najeriyar a matakin kwata-fainal a tsawon gasar.

To sai dai Shehu Abdullahi shugaban ƙungiyar marubuta labaran wasanni na jihar Kaduna ya ce dalilai biyu ne suka janyo wa Super Falcons rashin nasarar.

Ya ce na farko shi ne rashin shiri.

''Ƴanwasan da ma kocin kowa ya sakankance cewa za su yi nasara a wasan'', in ji shi.

Masanin harkokin wasannin ya ce Najeriya ta riƙa takama da cewa ita ce zakarar gasar don haka ne suka kasa wani shirin kirki domin tunkarar gasar ta bana.

''Ai ma idan ka duba duka wasanninta na wannan gasar, za ka fahimci ba su shirya ba, ya kamata a ce su ne suka ja ragamar rukuninsu, amma ka ga sai Malawi wadda wannan ne karonta na farko a gasar, ta ba su mamaki'', in shi ji.

Abu na biyu da Shehu Abdullahi ya bayyana a matsayin dalili shi ne tsufan wasu daga cikin ƴanwasan tawagar.

''Idan ka duba a cikin tawagar akwai ƴanwasan da sun fi shekara 10 suna bugawa Super Falcons, kuma yanzu yadda duniyar ƙwallon ƙafa take shi ne matasan ƴanwasan ne ke tashe'', in ji marubucin labarin wasannin.

Ya ƙara da cewa yana da kyau wasu tsoffin ƴanwasan tawagar su haƙura a ɗauki sabbin jini a gwama da sauran ƴantawagar a ba su horo tare.

Ko Najeriya za ta samu gurbin Kofin Duniya?

Samun nasara a wasan na ranar Lahadi ya bai wa Kamaru gurbin zuwa Gasar Kofin Duniya ta Mata da za a yi a shekarar 2027 a ƙasar Brazil, damar da Najeriya ta ɓarar a wasan.

To sai dai Shehu Abdullahi ya ce har yanzu ƙasar na da damar zuwa Gasar ta Brazil, amma kuma damar ba ta da yawa.

''Yanzu za su buga wasan neman gurbi ne da Afirka ta Kudu, idan sun yi nasara, za kuma su buga wasan neman gurbi na nahiyoyi da Koriya ta Kudu, idan ta yi nasara ne za ta samu gurbi'', in ji shi.

Sai dai masanin wasannin ya ce idan har Najeriya na son samun nasara a wannan buri nata, to dole ne ta sake shiri.

''Yanzu haɗuwar su a Afirka ta Kudu na buƙatar gagarumin shiri, tun da su ma Afirka ta Kudu ba kwanciya suka yi ba, suna nan suna ta shiri'', in ji shi.