Sabbin sharuɗan da Iran ta gindaya kafin buɗe mashigar Hormuz

    • Marubuci, Jack Burgess
    • Marubuci, Bernd Debusmann Jr
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, White House reporter
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Oman ta ce tattaunawa na gudana tsakanin ta da Iran a kan ƙulla yarjejeniyar tabbatar da tsaro ga jiragen ruwa masu wucewa ta mashigar Hormux, yayin da Tehran ta yi gargaɗin cewa ba za ta gaggauta buɗe hanyar tekun mai matuƙar muhimmanci ba.

A ranar Asabar dukkan ɓangarorin suka bayyana cewa tattaunawar tasu na samun armashi, amma babu wani tabbaci kan lokacin da za a ƙulla yarejejeniya. Ma'aikatar harkokin wajen Oman ta yi gargaɗin cewa duk wani hari a kan jiragen ruwan zai iya kawo cikas ga tattaunawar da ke gudana.

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce tattaunawar ta shiga zango na ƙarshe amma har yanzu ''ba a cimma matsaya kan buɗe mashigar Hormuz'' ba.

Tun bayan harin da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar kan Iran a watan Faburairu, Tehran ta rufe mashigar wadda ta kanta ake jigilar aƙalla kashi biyar cikin ɗari na mai da iskar gas da ake amfani da su a sassan duniya'

Tattaunawar baya-bayan nan ta mayar da hankali ne kan fatan ƙulla yarjejeniya tsakanin Iran da Oman a game da ƙulla wata haɗakar kula da mashigar Hormuz, wadda ake fatan za ta kai ga daidaita jigila ta mashigar.

Amma Araghchi ya ce buɗe mashigar ta danganta ne ga cika sauran sharuɗɗan da suka gindaya.

Ya ce sharudɗan sun haɗa da tilastawa Amurka biyan Iran diyyar ɓarnar da ta yi, musamman bayan yarjejeniyar zaman lafiya da suka ƙulla a watan nYuni.

Yarjejeniyar ta wargaje ƴan kwanaki bayan sanya hannu a kai, lamarin da ya kai ga hare-haren ramuwa a tsakani.

A wata sanarwa ta daban, babban jami'in tsaron Iran, Mohammad Baqer Zolqadr, ya shaidawa manema labarai cewa ba za su buɗe mashigar Hormuz ba har sai ''Amurka ta gyara kura-kuran da ta ke tafkawa ba''.

Ya ce suna buƙatar Amurka ta cika sharuɗɗa shida da suka haɗa da dakatar da sabuwar barazana ga Iran da janye dakarunta daga tekun Iran da kuma sakin ƙaddarorin Tehran da ta riƙe.

Mayaƙan Houthi masu samun goyon bayan Iran kuma sun toshe wata mashigar da ke kan tekun maliya na Saudiyya tun daga ranar 20 ga watan Yuli.

A farkon makon nan shugaban Amurka Donald Trump ya ce ''nan ba da jimawa ba'' za a ƙulla yarjejeniya da Iran. Amma mataimakin shi JD Vance ya bayyana shakku kan hakan, inda ya shaidawa Fox News cewa akwai sauran aiki idan har ana fatan cimma yarjejeniyar.

Ya ce "Muna a tsakiyar batun ne yanxu, wannan dambarwa ba ta ƙarewa ba tukun.''

Vance ya ƙara da cewa "Muna fuskantar batutuwa da dama ne, daga diflomasiyya zuwa tattalin arziki da ayyukan soji da kuma ƙoƙarin aiwatar da abin da Amurkawa ke so''.

Ya kuma yi iƙirarin cewa yankin Gulf zai samar da yawan man da ya saba samarwa duniya kafin harin ranar 28 ga watan Faburairu da Amurka ta ƙaddamar kan Iran.

Wani abu da ake jayayya kanshi tsakanin Tehran da Washington dai shi ne barazanar da Iran ke ci gaba da yi cewa za ta ƙaƙaba haraji kan duk kayan da ake wucewa da su ta mashigar Hormuz.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito jami'an gwamnatin Iran na cewa suna buatar a riƙa biyan su harajin kashi biyar zuwa bakwai na duk kayan da aka wuce da su ta mashigar Hormuz.

Mr Vance ya yi watsi da batun yana mai cewa "Iraniyawa sun shaida mana suna da shirin sayar da mashigar Hormuz."

Gargadin da Oman ta yi game da kai hari kan jiragen ruwa a mashigar na zuwa ne bayan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta sanar a ranar Asabar cewa Iran ta kai hari kan wani jirgin dakon mai mallakin kamfanin Adnoc na ƙasarta.

A ranar Asabar hukumar kula da sufurin jiragen sama na Birtaniya ya ce an kai hari kan wani jirgin shi a kan tekun Oman, amma ya ce ba a san wanda ya kai harin ba.