Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bangarori 10 na rayuwa da za su fi samar da ayyukanyi a 2030
- Marubuci, Mamadou Faye
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Afrique
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
A cewar rahoton Zauren Babban Taron Tattalin Arziki na Duniya na 2025, da aka wallafa a Janairun 2025, bangaren tattalin arziki da dama da na fasaha ne ake sa ran za su samar da sabbin ayyukan yi miliyan 170 a fadin duniya nan da 2030, yayin da kuma ake samun ɓacewar wasu ayyuka da aka saba da su na yau da kullum.
Yayin da muke tunkarar 2030, Zauren Babban Taron ya ayyana wasu bangarorin tattalin arziki da za su zama sune kan gaba wajen samar da ayyukan yi a nan gaba.
Ga wasu wurare 10 da ake tsammanin za su taka rawa wajen samar da ayyukan yi da habbaka tattalin arziki a shekaru masu zuwa.
Rahoton bai gabatar da wani jerin jadawali ba na cewa wuri kaza ne a gaba sannan wani wurin, kawai dai ya fitar da bayanai ne na habbakar ayyukan yi da kuma bayanai kan hasashen na wurare 22 da za su taimaka, tare da nuna manyan wuraren da za su samar da sauyi a bangaren aiki.
A cewar rahoton, tsakanin 2025 zuwa 2030, ana tsammanin za a samu karin sabbin ayyukan yi miliyan 170, karin kashi 14 kan ayyukan da ake da su a yanzu, ana kuma tsammanin za a shafe ayyuka miliyan 92 da ake da su a yanzu, raguwar kashi takwas kenan kan ayyukan da ake da su a yanzu, zai samar da karuwar albashi ga miliyan 78 karin kashi bakwai kan wanda ake da su a yanzu kamar yadda alkaluman ayyuka biliyan 1.2 suka bayyana.
1. Aikin noma da ma'adanan kasa
Yayin da ake tsammanin za a samu karin sama da ayyuka miliyan 35 nan da 2030, bangaren ayyukan noma ake tsammanin zai fi kowanne samar da ayyuka, kama daga ma'aikatan noma da masu barema na kullum, da sauran ma'aikata za su karu. Binciken ya ce za a samu karin yawan albashi ga mutanen da suke wannan bangaren.
Wannan bangaren na da ma'aikata sama da miliyan 200 a fadin duniya. A na sa ran wasu bangarorin rayuwa ne za su taimaka wajen habbakar wurin, ciki har da tsarin kula da muhalli, kokarin samar kawo sauyi ga matsalar sauyin yanayi, aiki da tsarin na'urorin zamani a fannin noma da kuma karuwar tsadar rayuwa.
2. Samar da abubuwan rayuwa da sufurinsu
Ayyuka biyu a wannan fanni za su taimaka wajen habbakar albashin da yawa, masu kai sako, da kuma direbobi.
Fannin ya samar da sabbin tsarin ayyukan yi da suka kai kashi 35 idan aka kwatanta da 22 da ake da su a baya a fadin duniya, wanda kai kaya ta hanyar dirobobi da kuma ta abubuwan sufuri masu tuka kansu.
3. Fasahar bunkasa bayanai da yada labarai
Masu samar da software da mahnajoji nada cikin kwararrun da tattalin arzikinsu ke habbaka kuma zai taimaka wajen samar da yawan albashi ga al'umar duniya.
Fannin zai samar da karin kashi 34 sabo da bayanai da za ta rika alkintawa da kuma zamar da su abubuwan dogaro wajen samar da abubuwan yi.
4. Aikin lafiya da na samar da magani
Bangaren malaman jinya na cikin ayyuka 15 da za su samar da karuwar albashin ma'aikata a duniya.
Yawan al'umma da ake samu a fannoni da yawa ana daukar shi a matsayin abin da zai rika taimakawa wajen habbakar tattalin arziki.
Adadin da fannin zai samar ya kai kashi 19 cikin 100.
5. Ilimi da ba da horo
Bangarori biyu a wannan fanni suna cikin 15 da za su iya taimakawa; bangaren malaman manyan makarantu da na malaman sakandire.
Babban abin da zai ba da wannan dama shi ne fadada ilimi ya koma ta intanet da kuma yadda aka kara samun fadadar shekarun a yankuna da dama.
Zai taimaka da kashi 22 shi ma.
6. Diloli da masu sayar da daidai
Aiki a shagunan sayar da kaya na cikin wuraren da suka da samar habbakar albashin ma'aikata.
Fannin zai samar da karin kashi 28 a matsagaicin hasashe, yayin da ake kara samun kwarewa a fannin fasahar AI kamar yadda alkaluma suka bayyana a fanni.
7. Ma'aikatun samar da abubuwan amfani
Masu samar da abincin gwangwani da kuma ma'aikatan da suke aiki a fannin cinikayya su ma za su samu kari mai gwabi.
Amma idan aka fadada hannu kan ma'aikatun, za a sa bangaren samar da lantarki da masu sayan kayayyaki, shi ma ya nuna za a samu karuwar da kashi 50 amma idan aka kalli ma'aikatun da babban masaki, wannan ne kuma fanni da za a samu kashi mafi yawa a duka rahoton wannan.
Wannan ya nuna irin habbakar da ake samu a bangaren fasahar zamani, (butun-butumi da masu sarrafa kansu)
8. Abubuwan more rayuwa da gine-gine da Injiniya
Masu tsara gine-gine da masu kammala su da kuma masu sayar da kayayyakin ginin duka na cikin wadanda za su taimaka wajen habbaka tattalin arziki.
Fannin an ce zai samu ci gaba ne saboda abubuwan da ake yayi, don haka ba a ayyana abu guda ba da zai zama shi zai babbaka fanni, yawan al'umma da habbakar birane da kuma amfani da makama shi wajen gine-gine da dai sauransu.
9. Ayyukan taimakon al'umma da tattalin arzikin ba da kulawa
Ayyukan taimakon al'umma da kwararrun da suke bayar da shawarwari, da masu taimako wajen ba da kulawa, dukansu suna cikin wadanda za su habbaka bangaren.
Yawan al'umma da karuwar mayar da hankali kan jin dadin al'umma suna cikin abubuwan da za su taimaka.
10. Makamashi da Fasaha mara gurbata muhalli
Duk da cewa ba a ta cikin ainihin jerin farko, wannan fannoni za su taimaka wajen habbakar tattalin arziki cikin gaggawa; makamashi mara gurbata muhalli ta fannin injiniya, akwai kuma wanda yake ta fannin fasahar zamani, kwararru wajen harkokin abubuwan hawa masu sarrafa kansu, injiniyoyin muhalli da masu sa makamashi irin na sola.
A bangaren makamashi da biyan kudaden ruwa da wuta, injiniyoyin bangaren makamashi mara gurbata muhalli shi ne na biyu a irin wannan rawa ta habbaka tattalin arziki, inda kudaden albashin fannin zai karu da kashi 46.
Shirin matasa na mamaye komai
Duk da haka, rahoton bai fitar da bayanan sabbin ayyukan da za a samu a kowanne fanni ba - ko kuma yawansu - kamar a ce ayyukan miliyan 35 a fannin aikin noma, sai dai kawai a ce aikin kaza ne za a rasa ko za a samu.
Abu na karshe, mafi muhimmancin abun da za a tuna shi ne aiki zai kasance na daban ne a gobe, amma kuma bukatar kwarewa za ta karu da narkewa a fanni cikin gaggawa da kuma ci gaba da koyo ko da yaushe.
Fannonin da za su samar da ayyuka masu yawa nan da 2030 za su magance matsaloli na kasa da kuma jurewa bukatu da ta yadda za su iya ciyar da bukatun mutanen duniya, su habbaka bangaren makamashi cikin da kuma komawa amfani da shi cikin sauri, karfafa tsarin lafiya, da kuma taimakawa wajen komawa kan harkokin intanet.